Gwamna Ya Tara Malamai 800, za Su Dukufa wajen Yi wa Tinubu Addu'a

Gwamna Ya Tara Malamai 800, za Su Dukufa wajen Yi wa Tinubu Addu'a

  • Gwamna Mai Mala Buni na Yobe ya gana da manyan malamai da suka fito daga sassa daban-daban na jihar a wani taro da suka yi
  • Ya bukaci malaman su rika gudanar da addu'a ga shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu da sauran shugabanni domin kawo cigaba a kasa
  • Mai Mala Buni ya sanar da cewa Najeriya ce kasar da kowa zai yi alfahari da ita, saboda haka dole kowa ya tashi tsaye wajen yi mata addu'a

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Yobe - Gwamnan jihar Yobe, Mai Mala Buni ya bukaci jama'a da su yi addu’a ga Najeriya, Shugaba Bola Ahmed Tinubu da sauran shugabannin kasar nan..

Mai Mala Buni ya bayyana haka ne yayin wata ganawa da manyan limaman masallatan Juma’a daga sassa daban-daban na jihar Yobe.

Kara karanta wannan

Abin da zai hana El Rufa'i shaƙar iskar ƴanci duk da kotu ta bayar da belinsa

Gwamna Mai Mala Buni na yi wa malamai jawabi
Mai Mala Buni na yi wa malaman Yobe bayani a gidan gwamnati. Hoto: Mamman Mohammed
Source: Facebook

Legit ta tattaro bayanan da gwamna Buni ya yi wa malaman ne a wani sako da mai magana da yawunsa, Mamman Mohammed ya wallafa a Facebook.

An tara malamai a jihar Yobe

Kashi na farko na taron da aka shirya domin malaman Musulmi da Kirista a jihar, ya samu halartar sama da manyan limamai 800 daga masallatan Juma’a.

Buni ya bayyana cewa Najeriya na bukatar addu’o’i domin magance makircin cikin gida da na waje da kuma tabbatar da zaman lafiya da ci gaban kasa.

Ya kara da cewa babu wani ci gaba mai ma’ana da zai samu ba tare da zaman lafiya ba:

“Shi ya sa yake da muhimmanci mu hada kai mu tallafa wa shugabanninmu domin ceton kasarmu.”

Bukatar yi wa Tinubu addu'a

Ya tunatar da jama’a cewa ba su da wata kasa face Najeriya, don haka alhaki ne a kansu su yi addu’a domin dorewar zaman lafiya da ci gaba, da kuma neman Allah Ya datar da shugaba Tinubu da sauran shugabanni.

Kara karanta wannan

Tinubu bai ji dadin abin da sojoji suka yi ba, ya tara manyan hafsoshin tsaro a Aso Rock

Mai bai wa gwamnan shawara kan harkokin addini, Ustaz Babagana Malam Kyari, ya ce an shirya taron ne domin tunatar da limamai muhimmancin yin addu’a ga Najeriya da shugabanninta.

Sama da limaman masallatan Juma’a 800 ne suka halarci taron, inda suka yi alkawarin isar da sakon zaman lafiya da zaman tare cikin lumana ga mabiyansu.

Wasu daga cikin malaman da suka halarci taro da gwamna Buni
Malaman da suka yi taro da gwamna Mai Mala Buni a Yobe. Hoto: Mamman Mohammed
Source: Facebook

Limaman sun kuma yi alkawarin kara kaimi wajen yin addu’a ga kasa, Shugaba Tinubu, Gwamna Buni da sauran shugabanni domin samun zaman lafiya da ci gaban Najeriya.

Ya kara da cewa kashi na biyu na taron zai hada fastoci da shugabannin majami’u daga fadin jihar domin suma su bayar da gudunmuwa wajen addu'a.

An yi wa Tinubu saukar Kur'ani

A wani labarin, kun ji cewa malaman Musulunci sun yi taro a Abuja domin taya shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu murnar cika shekara 74.

Fadar shugaban kasa ta sanar da cewa malaman sun yi saukar Al-Kur'ani sau 100 ga Bola Tinubu tare da rokon Allah ya kare shi, ya ba shi nasara.

Limamin masallacin kasa da ke birnin tarayya Abuja, Farfesa Ibrahim Makari na cikin malaman da aka hango wajen gudanar da addu'o'in.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng