Rikicin Manoma da Makiyaya Ya Barke a Taraba, an Samu Asarar Rayuka

Rikicin Manoma da Makiyaya Ya Barke a Taraba, an Samu Asarar Rayuka

  • Rayukan mutane sun salwanta sakamakon ɓarkewar rikicin manoma da makiyaya a jihar Taraba da ke yankin Arewa maso Gabas
  • Rikicin wanda ya fara bayan wasu makiyaya sun kai hare-hare, suka hallaka mutane 10 da ba su san hawa ba kuma ba su san sauka ba
  • Bayan kai wannan farmakin, wasu matasa sun kutsa zuwa cikin daji inda suka buɗewa wasu makiyaya da ke kula da dabbobinsu wuta

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Taraba - An tabbatar da cewa aƙalla mutane 16 sun mutu sakamakon rikice-rikicen da suka ɓarke tsakanin manoma da makiyaya a jihar Taraba.

Rikicin manoman da makiyayan ya ɓarke ne a ƙaramar hukumar Karim Lamido ta jihar Taraba.

Rikicin manoma da makiyaya ya barke a Taraba
Rikicin manoma da makiyaya ya jawo asarar rayuka a Taraba Hoto: @AgbuKefas
Asali: Twitter

Masani kan harkokin tsaro a yankin Tafkin Chadi da Arewacin Najeriya, Zagazola Makama, ya bayyana hakan a shafinsa na X.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yadda rikicin manoma da makiyaya ya auku

Majiyoyi sun bayyana cewa rikicin ya faru ne tsakanin ranakun 12 zuwa 14 ga Mayun 2025, inda ya shafi ƙauyuka kamar Mungadosso, Bandawa, Wuro Guga da dajin Fitowa.

Shaidun gani da ido sun bayyana cewa an kai hare-hare na ramuwar gayya daga ɓangarorin biyu.

Harin farko ya faru ne a ƙauyukan Mungadosso da Bandawa, inda ake zargin wasu makiyaya sun kai hare-hare guda uku a jere, suka kashe mutane 10, tare da ƙona gidaje da dama.

Al’ummar yankin na zargin cewa maharan sun yi amfani da wani sansani da ke Wuro Guga ta hanyar Jen a matsayin mafakar su.

A wani hari na ramuwar gayya, wasu matasa ɗauke da makamai daga Mungadosso sun hau babura zuwa dajin Fitowa da ke da nisan kilomita 20, suka buɗe wuta kan makiyaya da ke kiwon dabbobinsu.

Aƙalla makiyaya shida ne aka tabbatar da mutuwarsu a wannan harin na ramuwar gayya.

Mutane sun shiga halin fargaba

Wasu mazauna yankin sun bayyana cewa halin rashin tabbas da fargaba ya dabaibaye yankunan, inda iyalai da dama ke ƙaura daga gidajensu saboda tsoron ƙarin rikici.

Rikicin makiyaya da manoma ya barke a Taraba
Rayuka sun salwanta sakamakon rikicin makiyaya da manoma a Taraba Hoto: Legit.ng
Asali: Original

Wannan sabon rikici ya samo asali ne daga daɗaɗɗen rikici tsakanin manoma da makiyaya kan filin noma da ruwa, wanda ya jima yana haddasa zaman ɗar-ɗar a tsakanin al’umma.

Hukumomi da masu ruwa da tsaki sun buƙaci a kwantar da tarzoma nan da nan tare da shirya tattaunawa tsakanin ɓangarorin da abin ya shafa domin gujewa ƙarin asarar rayuka.

A halin yanzu, ƴan sandan yankin da sauran jami’an tsaro na ci gaba da sintiri a wuraren da ake ganin rikici na iya sake ɓarkewa.

Rikicin ƙabilanci ya ɓarke a Taraba

A wani labarin kuma, kun ji cewa an samu ɓarkewar wani rikicin ƙabilanci tsakanin Jukunawa da Tiv a jihar Taraba.

Maharan waɗanda suka kai hari a ƙauyen Denkeh da ke kan hanyar Wukari zuwa Taraba sun hallaka mutum ɗaya tare da barin wani da raunin harbin bindiga.

Miyagun waɗanda suke ɗauke da bindigogi sun buɗe wuta kan mai uwa da wabi kafin su cinnawa gidaje da rumbunan abinci wuta.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng