Tsaro: Ƴan Najeriya Sun Taso Tinubu a Gaba, Suna So a Kori Ɗan Arewa daga Minista

Tsaro: Ƴan Najeriya Sun Taso Tinubu a Gaba, Suna So a Kori Ɗan Arewa daga Minista

  • Ana nemi Shugaba Bola Tinubu da ya sallami ministan tsaro, Mohammed Badaru Abubakar, saboda tabarbarewar tsaro a sassan Najeriya
  • Wata ƙungiyar Yarabawa, AYPN, ta goyi bayan sukar da ɗan majalisar tarayya, Yusuf Gagdi, ya yi wa Badaru kan rashin ƙwarewa
  • Ƙungiyar AYPN ta zargi Badaru da fifitabuƙatun kansa fiye da tsaron ƙasa tare da kuma zargin aikata ba dai dai ba a ma'aikatar tsaro

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Abuja - Ana ƙara ci gaba da yin kira ga Shugaba Bola Tinubu da ya sallami ministan tsaro, Mohammed Badaru Abubakar daga muƙaminsa.

Wannan ya biyo bayan sukar da wani ɗan majalisar tarayya da wata ƙungiyar matasa suka yi masa a bainar jama'a kan yadda yake tafiyar da lamuran tsaro da ke ƙara ta'azzara a Najeriya.

An nemi Shugaba Bola Tinubu da ya sallami ministan tsaro, Muhammed Badaru
Shugaba Bola Tinubu | Ministan tsaro, Mohammed Badaru, Hoto: Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, Mohammad Badaru Abubakar
Asali: Facebook

Kungiyar Yarbawa ta zargi ministan tsaro

Ƙungiyar matasan Afenifere (AYPN), ta Yarabawa, ta goyi bayan kalaman Hon. Yusuf Gagdi, tana mai kira da a tsige Muhammadu Badaru daga minista, inji rahoton The Nation.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Hon. Yusuf Gagdi, ɗan majalisar wakilai daga Jihar Plateau, ya nuna shakku kan ƙwarewar ministan a wani zaman majalisa da aka yi kwanan nan.

A zaman majalisar da ta gabata, Gagdi ya nuna damuwarsa game da yawaitar hare-haren 'yan ta'adda, musamman a jihar Borno, inda aka ce 'yan bindigar da suka kai hari kan sansanonin sojoji sun ƙwace tankunan yaki da makamai masu yawa.

Ƙungiyar AYPN ta bayyana kalaman Gagdi a matsayin "gaskiyar da babu surki a cikinta," tana mai cewa halin da ake ciki a kasar ya fara fusata jama'a.

'Ma'aikatar tsaro ta ruguje' - AYPN

Shugaban matasan Afenifere, Olatunji Fadare, a wata sanarwa da ya fitar ranar Lahadi, 11 ga Mayu, ya ce "babu wani uzuri ga abin da ke faruwa a ƙarƙashin kulawar Badaru".

Ya ƙara da cewa:

"Ma'aikatar tsaro ba ma'aikata ce da za a rika mika ta a hannun wadanda siyasa za ta yi wa rana ba ce. Ita ma'aikata ce da ta zamo ginshiƙin tsaron Najeriya, yanzu kuma ta rushe."

Ƙungiyar ta zargi Badaru da fifita bukatun kansa da na 'kasuwancinsa' fiye da tsaron ƙasa tun lokacin da ya hau mulki, tana mai zarginsa da rashin gogewar da ake buƙata don magance ƙalubalen tsaro masu sarkakiya na Najeriya.

Zargin aikata ba daidai ba a ma'aikatar tsaro

AYPN ta kuma yi ikirarin cewa ana ba da kwangilolin tsaro bisa ga alaƙar siyasa ba bisa cancanta ba, wanda ke haifar da rashin isassun kayan aiki da bayanan sirri ga sojoji.

Jaridar Independent ta rahoto Olatunji Fadare ya ce:

"Muna da sahihan bayanai da ke nuna cewa ana ba wata ƙabila da ƙungiyar siyasa ta musamman fifiko a dukkanin shawarwarin tsaro da ake yanke wa.

"Wannan yana barazana ga haɗin kan ƙasa kuma yana lalata amincewar al'umma ga hukumomin tsaro."

Ƙungiyar ta zargi Badaru da mayar da ma'aikatar tsaro zuwa "ma'aikatar Hausa-Fulani," inda ta ce ana nuna bambanci na ƙabila da siyasa a cikin ɗaukar ma'aikata da ba da kwangila.

An nemi shugaban kasa Tinubu ya sallami ministan tsaro, Mohammed Badaru.
Ministan tsaron Najeriya, Mohammed Badaru. Hoto: @Mohammed_Badaru
Asali: Facebook

An bukaci Tinubu ya gaggauta tsige Badaru

Ƙungiyar matasan ta yi kira ga Shugaba Tinubu da ya gaggauta yin garanbawul a fannin ta hanyar farawa da tsige Badaru daga mukamin minista.

Sanarwar kungiyar ta ce:

"Wannan ba siyasa ba ce; batun rayuwa ne. Dole ne Tinubu ya tabbatar da cewa biyayya ga Najeriya ta fi biyayya ga abokai. Dole ne Badaru ya tafi."

Kungiyar ta yi ikirarin cewa rashin tsaro na ci gaba da ƙaruwa a yankin Arewa maso Gabas, Arewa maso Yamma, da sassan Tsakiyar Najeriya.

AYPN ta yi gargadin cewa gwamnati za ta iya kara rasa yardar jama'a idan har ta gaza ɗaukar mataki kan shugabannin da ba su yi aiki yadda ya kamata ba.

"Muna so a yi adalci ga sojojinmu da 'yan ƙasarmu da aka zubar da jinunsu, kuma wannan adalcin zai fara ne daga lokacin da aka cire waɗanda suka gaza kare mu."

- Olatunji Fadare.

Gwamnati ta karyata korar ministoci 3

A wani labarin, mun ruwaito cewa, fadar shugaban ƙasa ta ce labaran da ke yawo game da korar ministan tsaro, karamin ministan tsaro, da Ministan Makamashi ba su da tushe.

Mai ba wa shugaban ƙasa shawara kan harkokin yaɗa labarai, Bayo Onanuga, ya bayyana cewa wadannan labarai da ake yaɗawa a kafafen sada zumunta ba gaskiya ba ne sam-sam.

Onanuga ya yi kira ga hukumomin tsaro da su ɗauki matakan gaggawa kan kafafen yaɗa labarai da ke yaɗa labaran ƙarya ba tare da wani tabbaci ko bincike ba.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.