Italiya Ta Datse Yarjejeniyar Sayar wa Isra'ila Makamai kan Yakin Lebanon

Italiya Ta Datse Yarjejeniyar Sayar wa Isra'ila Makamai kan Yakin Lebanon

  • Kasar Italiya ta dakatar da sabunta yarjejeniyar tsaro da Isra’ila kai tsaye yayin da Benjamin Netanyahu ke ci gaba da kai hare-hare Gabas ta Tsakiya
  • Matakin ya zo a gabar da ake samun tashin hankali da sabani kan hare-haren Lebanon da aka nemi Isra'ila ta dakata da kashe jama'a da rusau
  • Dakarun IDP suna ci gaba da kai munanan hare-hare da ke rusa yankunan Lebanon musamannan ta Kudancin kasar ana cikin yaki da Iran

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Italy – Italiya ta dakatar da sabunta yarjejeniyar haɗin gwiwar tsaro da Isra’ila kai tsaye, wani mataki da ke nuna sauyi mai girma a manufofinta bayan shekaru ana cinikayya babu tangarda.

Rahotanni sun ce Firaministar ƙasar, Giorgia Meloni, ta bayyana cewa, duba da halin da ake ciki a yanzu, gwamnati ta yanke shawarar dakatar da sabunta yarjejeniyar tsaro da Isra’ila kai tsaye.

Kara karanta wannan

Yadda ake shirin hana Trump sayarwa Isra'ila makamai a majalisar Amurka

Italiya ta datse alakar soja da Isra'ila
Giorgia Meloni, Firaministar Italiya da takwaranta na Isra'ila, Benjamin Netanyahu a gefe Hoto: Giorgia Meloni/Prime Minister of Israel
Source: Facebook

Aljazeera ta wallafa cewa rahotanni sun nuna cewa Ministan tsaron Italiya, Guido Crosetto, ce ya tabbatar da matakin ta hanyar wasiƙa da ya aika wa takwaransa na Isra’ila, Israel Katz.

Italiya ta yanke alakar tsaro da Isra'ila

Palestine Chronicle ta wallafa cewa an yanke wannan shawara biyo bayan tattaunawa da hadin gwiwa tsakanin Ministan harkokin wajen ƙasar Antonio Tajani, da Mataimakin Firaminista Matteo Salvini.

An rattaba hannu kan yarjejeniyar tun a shekarar 2006, kuma ana sabunta ta duk bayan shekara biyar. Yarjejeniyar na bai wa kasashen biyu damar haɗin gwiwa a fannin soja, ciki har da musayar kayan aiki, horo, da binciken fasaha.

Italiya ta samu matsala da Isra'ila
Benjamin Netanyahu, Firaministan Isra'ila yana bayani Hoto: Benjamin Netanyahu
Source: Getty Images

Farfesa Triestino Mariniello, malamin shari’a a jami’ar Liverpool John Moores, wanda kuma yana cikin tawagar lauyoyin da ke wakiltar waɗanda rikicin Gaza ya shafa a Kotun Hukunta Manyan Laifuka ta Duniya ya magantu kan batun.

Mariniello ya jaddada muhimmancin tantance lokacin da aka aika wasiƙar Crosetto zuwa Katz. A cewarsa, yana da matuƙar muhimmanci a san ko an aika wasiƙar ne kafin ko bayan sabunta yarjejeniyar ta 2026.

Kara karanta wannan

Tsaro ya damalmale, Amnesty ta fadi yawan mutanen da aka sace a watanni 3

An magantu kan alakar Isra'ila da Italiya

Ya ce idan aka aika wasiƙar bayan sabunta yarjejeniyar, to za ta ci gaba da aiki har zuwa shekarar 2031, wanda hakan ke sa batun ya zama mai matuƙar muhimmanci a bangaren doka.

Matakin na Italiya ya zo ne a daidai lokacin da dangantaka tsakanin ƙasar da Isra’ila ta kara tsami, musamman bayan abubuwan da suka faru a Lebanon.

Mahukuntan Italiya sun zargi sojojin Isra’ila da harba gargadi kan ayarin jami’an wanzar da zaman lafiya na na majalisar dinkin duniya na Italiya (UNIFIL) a kudancin Lebanon, inda aka ce akalla mota guda ta lalace.

A matsayin martani, Italiya ta gayyaci jakadan Isra’ila domin nuna rashin amincewa, yayin da Isra’ila ma ta kira jakadan Italiya bayan Antonio Tajani ya yi Allah-wadai da ayyukan sojin Isra’ila.

Ana son hana sayar wa Isra'ila makamai

A baya, mun wallafa cewa ana cigaba da samun masu fada a ji a Amurka suna nuna adawa game da alakar kasar da Isra'ila kan sayar wa Tel Avi makamai da sauransu yayin da ta ke yakar kasashe.

Kara karanta wannan

Wata sabuwa: Firaministan Isra'ila ya sake dauko rigima bayan dakatar da yakin Iran

Rahotanni sun nuna cewa Sanata Bernie Sanders ya yi alƙawarin tilasta dakatar da sayar da makaman Amurka ga Isra’ila a majalsar kasar, a lokacin da ake yaki da Iran, Lebanon da Falasdinu.

Bernie Sanders ya kasance na gaba-gaba wajen caccakar yake-yake da Donald Trump ke yi da kuma hare-haren Isra'ila a Gaza da Lebanon, da kuma na Iran da aka fara a karshen watan Fabrairu.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng