'Tinubu Ya Gama Na Shi': An Taso Ministan Tsaro a Gaba Ya Ajiye Muƙaminsa Nan Take
- Masanin tsaro, Opialu Fabian ya yabawa Bola Tinubu bisa yawan kasafin kudin tsaro, amma ya ce ministocin da aka nada ba sa aiki yadda ya kamata
- Ya soki Ministan Tsaro, Mohammed Badaru Abubakar yana cewa kiran TY Danjuma na daukar mataki a kare kai tamkar rashin yarda ne da aikin Ministan
- Fabian ya bukaci Ministan da ya yi murabus saboda rashin iya aiki, ya ce matsalar tsaro tana bukatar sabbin shugabanni da tsari na musamman
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
FCT, Abuja - Masanin harkokin tsaro kuma mai sharhi kan al’amuran yau da kullum, Opialu Fabian, ya yabawa kokarin Bola Tinubu wajen yaki da rashin tsaro a Najeriya.
Fabian ya bayyana cewa kasafin kudin da aka ware wa fannin tsaro a wannan gwamnati shi ne mafi girma a tarihi, yana nuna an shirya yakar matsalar sosai.

Asali: Twitter
An yabawa Bola Tinubu a batun matsalar tsaro
Sai dai ya soki wasu daga cikin mukarraban Tinubu, yana cewa ba su tabuka komai ba wajen shawo kan matsalar tsaro da ke kara kamari, cewar Leadership.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ya ce Tinubu ya cancanci yabo duba da makudan kudi da ya ware a bangaren tsaro ya rage masu alaka da hakan su yi abin da ya dace.
Sanarwar ta ce:
“Shugaban kasa ya yi kokari, kasafin kudin ya fi kowanne yawa, yana nuna cewa yana da niyyar yaki da rashin tsaro.
“Amma wadannan mukarraban ba su yin abin kirki. Shugaban kasa ya ba jami’an tsaro umarni su kawo karshen matsalar, amma hakan ba zai yi aiki haka kawai ba.”

Asali: Facebook
An bukaci Badaru ya yi murabus daga Minista
Fabian ya kira Ministan Tsaro, Mohammed Badaru kai tsaye yana cewa kiran da TY Danjuma ya yi na daukar matakin kare kai na nuna rashin amincewa da Ministan.
Ya kara da cewa:
“Wannan na nuni da cewa Ministan bai yin abin da ya kamata wajen tinkarar matsalolin tsaron da ke addabar kasar.”
“Tattara bayanan sirri muhimmin bangare ne a harkar tsaro, Ministan kuma bai kware wajen yin hakan ba."
Saboda haka, Fabian ya bukaci Badaru Abubakar da ya ajiye aikinsa, ya gode wa Tinubu da ‘yan Najeriya bisa damar da suka ba shi, Tribune ta ruwaito.
Ya ce:
“Ministan ya gode wa ‘yan kasa da Shugaban kasa bisa damar da aka bashi sannan ya ajiye aikinsa.
"Bai dace da wannan aiki ba, ci gaba da kasancewarsa a kujerar zai kara ta’azzarar matsalolin tsaro."
Ya danganta matsalolin tsaron Najeriya da gazawar shugabanni, yana mai cewa dole a sake fasalin tsarin tsaro don ya dace da halin yanzu.
Badaru ya shirya kawo karshen rashin tsaro
Kun ji cewa ministan tsaron, Badaru Abubakar ya jagoranci kaddamar da sababbin jiragen yaƙi samfurin ATAK-129 a jihar Katsina.
Badaru ya ce jiragen za su taimaka wajen kawo karshen ƴan bindiga da dukkan nau'in miyagun da ke kawo cikas a zaman lafiya.
Ya kuma jinjinawa dakarun sojoji bisa sadaukarwar da suke yi domin tabbatar zaman lafiya da kwanciyar hankali a Najeriya.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng