Latest
‘Yan bindiga sun kashe ɗan takarar APC, Oluwatosin Onamade, a Legas. Bayan harsashi ya gagara shigarsa, sun sassare shi da adda a kai da fuska har ya mutu.
Sarki Muhammadu Sanusi II ya karbi bakuncin kungiyar 'Obidient' a jihar Kano. Sanusi ya zauna da mutanen Peter Obi ranar da Malam Nasir El-Rufai ya bar APC.
Tsohon ministan wasanni, Barista Solomon Dalung ya yi barka da shigar EL-Rufa'i zuwa SDP. Dalung ya ce SDP ce za ta gina kasa mai kyau a fadin Najeriya.
Gwamna jihar Ribas, Sir Siminalayi Fubara ya bayyana yadda labarin masarautar Akpor ya sosa masa zuciya har ya zibar da hawaye a cikin taro, ya gina ma sarki gida.
Wani yaro mai shekaru 14 ya koma ga Mahaliccinsa sanadiyyar fashewar tukunyar Gas a Goron Dutse da ke Kano, lamarin ya jawo hankalin jami'an yan sandan jihar.
Mai taimakawa gwamnan jihar Delta, Kelvin Ogboru ya ce APC za ta sha kaye a zaben shekarar 2027 mai zuwa. Ya ce APC kamar katanga ce da za ta rushe.
Hajiya Hafsat Mohammed Baba ta sanar da ficewarta daga APC, tana mai cewa jam’iyyar ta rasa alkiblarta, lamarin da ake ganin yana da alaka da ficewar El-Rufai.
Daya daga cikin jagororin PDP, Kola Ologhondinyan ya bayyana cewa APC ta kwana da sanin cewa akwai gagarumin shirin da zai kawo karshen mulkinta a 2027.
Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya ce an cire tallafin man fetur ne domin kare goben Najeriya. Ya fadi haka ne yayin kaddamar da taron matasan Najeriya a Abuja.
Masu zafi
Samu kari