Babban Malamin Addini Ya Ayyana Tsayawa Takarar Shugaban Ƙasa, Zai Kara da Tinubu
- Wani bidiyo ya nuna malamin coci, Odumeje ‘Indaboski’ yana bayyana kudurinsa na tsayawa takarar shugabancin Najeriya a 2027
- A yayin wata huduba mai zafi da ya gabatar ga mabiyansa, Fasto Odumeje ya bayyana cewa Najeriya na bukatar shugaba mai jini a jika
- Bidiyon da ke nuna lokacin da Fasto Odumeje ya nuna sha'awar tsayawa takara ya yadu sosai, ya haifar da cece-kuce a tsakanin jama’a
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Malamin addinin Kirista a Najeriya, Chukwuemeka Cyril Ohanaemere da aka fi sani da Odumeje ko Indasbosky ya nuna sha'awar tsayawa takarar shugaban kasa a 2027.
Odumeje, wanda ya assasa Cocin Mountain of Holy Ghost Intervention da Deliverance Ministry ya bayyana aniyarsa a fili ne a yayin da yake wa'azi ga mabiyansa.

Asali: Instagram
Fasto Odumeje zai fito takarar shugaban kasa

Kara karanta wannan
Sarki Sanusi II ya karbi bakuncin kungiyar 'Obedient' a Kano, ya ba su shawarwari
Legit Hausa, ta ci karo da bidiyon babban malamin a shafin The Nation na X, inda malamin ke nuna shirinsa na jagorantar Najeriya a 2027.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Malamin addinin Kiristan wanda ya saba fadin maganganun da ke jawo ce-ce-ku-ce, ya bayyana cewa Najeriya na bukatar matashi mai jini a jika.
Baya ga matashi mai jini a jika, Chukwuemeka Cyril Ohanaemere ya kuma ce kasar tana bukatar matashin da ya san kan fasahohin zamani.
"Najeriya na bukatar matashi" - Fasto Odumeje
Da yake jawabi ga mabiyansa a cikin bidiyon, an ji Fasto Odumeje ya na cewa:
"Muna bukatar matashi a shugabancin kasar nan, kuma ina tunanin zan fito takarar shugaban kasar.
"Muna bukatar matashi mai jini a jika a matsayin shugaban kasar nan. Shugaban da ya san kan fasahohin zamani, ba wai irin tsofaffin nan ba."
A yayin da yake bayyana wannan kuduri nasa, an ji mabiyan nasa suna shewa, alamar karfafa masa gwiwa kan shirin da ya sanya a gabansa.
Malamin ya karfafi mabiyansa kan shirin takararsa

Asali: Instagram
Fasto Odumeje wanda ya shahara saboda salon wa'azinsa da ya sha bamban da na sauran fastoci, ya tambayi mabiyansa ko sun shirya ganinsa a matsayin shugaban kasa na gaba.
"Kun shirya na fito? Kun shirya na zama shugaban kasa,"
- Odumeje ya tambayi mabiyan nasa.
Ya kara da cewa,
"Saboda ni na san abin da kuke da bukata. Don haka kowa ya ce Amin."
Sai dai kuma, babban malamin addinin Kiristan bai wani yi bayani game da shirinsa na shiga wata jam'iyyar siyasa ko kuma tsarin yakin neman zabensa ba.
Kalli bidiyo da ra'ayoyin mutane game da ra'ayin malamin addinin na zaman shugaban kasar Najeriya na gaba, a nan kasa:
Minista ya nuna sha'awar tsayawa takarar gwamna
A wani labarin, mun ruwaito cewa, ministan lafiya a gwamnatin shugaba Bola Tinubu, Farfesa Ali Pate ya nuna sha'awar tsayawa takarar gwamnan jihar Bauchi a 2027.
Pate, ya bayyana cewa yana da duk wata cancanta da ake bukata ta shugabanci don haka zai jaraba sa'arsa idan har wakilan jam'iyyar APC sun ba shi goyon baya.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng