Sarki Sanusi II Ya Karbi Bakuncin Kungiyar 'Obedient' a Kano, Ya ba Su Shawarwari
- Matashin dan siyasa, Morris Monye ya jagoranci tawagar 'Obidient Movement' wajen ziyarar Sarkin Kano don karfafa hadin kai
- Tawagar ta tattauna da Muhammadu Sanusi II kan ci gaban kasa, karfafa matasa da bukatar shigar kowa a harkokin dimokuradiyya
- Monye ya yi buda baki tare da mabiyan Peter Obi a Kano, suka tattauna kan samar da Najeriya sabuwa mai gaskiya da shugabanci nagari
- Ziyarar ta nuna yunƙurin fadada tasirin kungiyar a Arewa don hada kai da gina Najeriya bisa gaskiya, adalci da shugabancin jama’a
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Kano - Daraktan 'Obidient Movement', Morris Monye ya jagoranci tawaga zuwa fadar Sarkin Kano don jaddada kishin kasa da hadin kai.
A yayin ziyarar, Monye da tawagarsa sun tattauna da Sarki Muhammadu Sanusi II kan batun ci gaban kasa, karfafa matasa da shiga siyasa cikin gaskiya da zaman lafiya.

Asali: Facebook
Kano: Sarki Sanusi II ya shawarci ƴan 'Obidient'
Monye ya bayyana haka ne a cikin wata sanarwa da ya wallafa a shafin Facebook a jiya Litinin 10 ga watan Maris, 2025.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ƴan kungiyar 'Obidient' dai sun samo asali ne daga tafiyar akida da Peter Obi yayin neman takarar shugaban kasa a zaben 2023 da ta gabata wanda ya shanye a hannun Bola Tinubu.
Yayin ziyarar, Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II ya tarbe su hannu bibbiyu, ya jaddada muhimmancin zaman lafiya, hadin kai da shiga siyasa don ci gaban Najeriya gaba daya.
Yayin da yake ci gaba da ziyarar, Morris Monye ya halarci buda baki tare da mabiya kungiyar 'Obidient' a Kano domin sada zumunta.
Taron buda bakin ya kara hada kai da fahimtar juna, inda mabiya kungiyar suka bayyana burin ganin Najeriya ta samu shugabanci nagari.
Monye ya bukaci mabiya kungiyar a Kano da su dage wajen ganin an samu shugabanci mai gaskiya da kuma rikon amana.
Ya ce:
“Wannan tafiya da muke yi ta wuce maganar siyasa, tafiya ce da aka gina ta domin inganta rayuwar al'umma da ci gaban kasa saboda samun ingantacciyar rayuwa."

Asali: Twitter
Tafiyar Peter Obi na kara karfi a Arewa
Ziyarar na nuni da yunƙurin 'Obidient Movement' wajen karfafa gindinta a Arewa, domin ganin an hada kowa da kowa cikin harkar siyasa.
Monye ya jaddada muhimmancin hadin kai tsakanin kabilu da addinai, yana mai cewa ci gaban Najeriya yana bukatar hadin gwiwa.
An rufe taron da addu’o’i don samun zaman lafiya da cigaba, yayin da magoya bayan kungiyar suka kara jaddada goyon bayansu ga muradun kungiyar.
Rigimar sarauta: Gwamnatin Kano ta roki Tinubu
Mun ba ku labarin cewa Gwamnatin jihar Kano ta bukaci shugaba Bola Tinubu ya cire Sarki na 15, Aminu Ado Bayero daga Fadar Nasarawa.
Gwamnatin ta ce daukar wannan mataki ne kawai zai kawo zaman lafiya da kwanciyar hankali a jihar da kowa ke bukata tun bayan rigimar sarauta.
Hakan na cikin wani sako da mataimakin gwamnan, Aminu Abdussalam Gwarzo ya fitar, ya ce matasan Kano sun gaji da halin da ake ciki.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng