2027: Yan Adawa na Shirin Firgita Tinubu, Ƙusa a PDP Ya Ce Guguwar Canji za Ta Tafi da APC
- Tsohon sakataren yaɗa labaran jam'iyyar hamayya ta PDP ya bayyana cewa ƴan adawa suna shirin kawar da APC daga mulki
- Kola Ologbondiyan ya faɗi haka ne a lokacin da tsohon gwamnan Kaduna, Nasir El-Rufa'i ya fice daga APC zuwa jam'iyyar SDP
- Ya ce jiga-jigan ƴan adawa a Najeriya suna ƙulla shirin da zai wargaza aniyar APC na ci gaba mulkin Najeriya bayan zaɓen 2027
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
FCT Abuja – Tsohon sakataren yaɗa labaran PDP na ƙasa, Kola Ologbondiyan, ya bayyana cewa ana shirin kafa haɗin gwiwa tsakanin jam’iyyun adawa kafin zaɓen shugaban ƙasa na 2027.
Ologbondiyan ya yi gargaɗi ga jam’iyya mai mulki, yana mai cewa abin da ke tafe ba ƙaramin abu ba ne, domin ana haɗa shirin da zai girgiza APC a zaben 2027

Asali: Facebook
Da yake magana a tashar AIT, jigon na PDP ya bayyana cewa an tsara matakin da zai ƙalubalanci APC a babban zaɓen 2027 mai zuwa.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Jam'iyyar PDP ta shirya tunkarar APC
Kola Ologbondiyan ya ce ‘yan Najeriya su kwantar da hankalinsu, domin ana shirin kwato musu ‘yanci a kakar zaɓen 2027 mai zuwa.
Ya bayyana hakan ne bayan da tsohon gwamnan Kaduna, Nasir El-Rufa’i, ya fice daga jam’iyyar APC zuwa SDP, awanni kaɗan bayan ganawa da Atiku Abubakar a gidansa da ke Abuja.
Jagora a PDP ya ce manyan ‘yan adawa sun shirya tsaf don fuskantar APC a zaɓe mai zuwa tare da kyakkyawan shirin da zai ba ta mamaki.
PDP na ƙoƙarin haɗa kan ‘yan adawa
Kola Ologbondiyan ya bayyana cewa ana shirin haɗa manyan ‘yan adawa don yin aiki tare kafin 2027.
Ya ce:
“Abin da ke tafe ba ƙaramin abu ba ne. Abu mafi muhimmanci shi ne sha’awa da shirin ‘yan adawa na haɗa kai.”
"Zan cewa ‘yan Najeriya su kwantar da hankalinsu, domin akwai kyakkyawar makoma a gaba. A Ghana, ‘yan adawa sun ci zaɓe.”
"Akwai shirin haɗaka," Tsohon ɗan takarar PDP
Kalaman Ologbondiyan na zuwa ne a daidai lokacin da tsohon dan takarar shugaban ƙasa a jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar, ya tabbatar da yunƙurin kafa ƙawancen ‘yan adawa.

Asali: Facebook
Atiku ya tabbatar da cewa ana tattaunawa tsakanin jam’iyyun adawa don kafa kawance, sai dai ya musanta ikirarin cewa yana shirin komawa jam’iyyar SDP, kamar yadda ake faɗi.
Jama'a na ganin PDP za ta dawo mulki
A wani labarin, mun wallafa cewa ziyarar da tsohon gwamnan Kaduna, Nasir El-Rufa'i ya kai wa tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ja hankalin ƴan Najeriya.
Wasu sun fara hasashen cewa wannan wata alama ce ta haɗaka mai ƙarfi da za ta kawo cikas ga burin APC na mayar da Bola Ahmed Tinubu kan kujerar shugabancin ƙasa a 2027.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng