Yaki da Zaman Banza: Tinubu na Shirin Samar da Ayyuka ga Matasa Miliyan 10
- Kungiyar Bishop-Bishop na Katolika (CBCN) ta bukaci a dauki matakan gaggawa kan matsalolin tattalin arziki da siyasa a Najeriya
- Fadar Shugaban Kasa ta yi martani da cewa Najeriya ta samu gagarumin ci gaba tun bayan hawar Bola Tinubu kan mulki a 2023
- Gwamnatin Tinubu ta ce tana aiwatar da shirye-shiryen inganta tsaro, bunkasa tattalin arziki da samar da ayyukan yi ga matasa
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja - Kungiyar Bishop-Bishop na Katolika (CBCN) ta bukaci shugabannin Najeriya da su dauki matakan gaggawa don hana kasar kara fuskantar tabarbarewa.
Shugaban kungiyar, Lucius Iwejuru, ya bayyana matsalolin da ke damun kasar, kamar rashin aikin yi ga matasa, rashin tsaro, talauci, cin hanci da magudin zabe.

Kara karanta wannan
El Rufa'i na shirin jan 'yan APC zuwa SDP, Tinubu ya yi magana kan tallafin fetur

Asali: Facebook
Mai magana da yawun shugaban kasa, Bayo Onanuga ya ce kungiyar ba ta fahimci inda aka dosa ba ne a cikin wani sako da ya wallafa a X.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Fadar Shugaban Kasa ta ce Najeriya ta samu ci gaba sosai tun bayan hawan Bola Ahmed Tinubu kan mulki.
Martanin Tinubu ga kungiyar Katolika
Gwamnatin tarayya ta ce gwamnatin Tinubu na tafiya a hanya madaidaiciya sabanin abubuwan da kungiyar ta fada
Fadar shugaban kasa ta ce:
“Duk da cewa akwai matsaloli a wasu bangarori, Najeriya ta samu gagarumar ci gaba tun bayan hawar Tinubu.”
A cewar sanarwar fadar shugaban kasa, matsalar tsaro ta ragu matuka, inda a cikin shekaru biyu da suka gabata, an kashe ‘yan ta’adda sama da 8,000, an kuma kubutar da mutum 10,000.
Gwamnatin Bola Tinubu ta kara da cewa hakan ya bai wa manoma damar komawa gonaki, musamman a yankunan Arewa maso Yamma da Arewa maso Gabas.
Samar da aiki ga matasa miliyyan 10
Dangane da tattalin arziki, gwamnatin Tinubu ta ce ta tsaftace tattalin arzikin kasa daga mawuyacin halin da ta gada.
A cewar Bayo Onanuga, an samu ci gaba a fannin hada-hadar kudi, darajar Naira na kara dagawa, kuma masana’antu kamar matatar Dangote sun fara samar da mai a cikin gida.
Onanuga ya ce:
“Gwamnati na bunkasa matasa ta hanyar shirye-shirye irin su 3MTT, NATEP, LEEP da NiYA, wadanda za su samar da ayyukan yi sama da miliyan 10.”
An yabawa Tinubu a duniya - Onanuga
Fadar Shugaban Kasa ta ce gwamnatoci da kungiyoyin duniya na yabawa da salon shugabancin Tinubu.
A cewar Onanuga, cibiyar nazari ta Chatham House ta bayyana cewa Najeriya ta samu bunkasa a fannin tattalin arziki a karkashin mulkin Tinubu.

Asali: UGC
Mai magana da yawun shugaban kasar ya ce Chatham House ya wallafa cewa:
“Kasar na kara samun kudin shiga, ana kuma aiwatar da kasafin kudi mafi girma a tarihi – N54.9tn domin habaka tattalin arziki.”
Fadar Shugaban Kasa ta ce tana fahimtar cewa har yanzu ‘yan Najeriya na fama da kalubale, amma tana da yakinin cewa matakan da ake dauka za su haifar da kyakkyawan sakamako.
An yi hasashen faduwar APC a 2027
A wani rahoton, kun ji cewa wani jigo a jam'iyyar PDP ya ce akwai alamu da suka nuna cewa jam'iyyar APC za ta fadi warwas a 2027.
'Dan siyasar ya bayyana cewa 'yan Najeriya za su juya wa APC baya saboda sun gaji da salon mulkin da jam'iyyar ke yi a kasar nan.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng