An ba Gwamna Lambar Yabon 'Khadimul Qur'an' saboda Hidimtawa Littafin Allah

An ba Gwamna Lambar Yabon 'Khadimul Qur'an' saboda Hidimtawa Littafin Allah

  • Malaman Tsangaya na jihar Gombe sun ba Gwamna Inuwa Yahaya lambar yabon Khadimul Qur'an bisa gudummuwar da yake bayarwa
  • Sun karrama gwamnan ne a wurin taron buɗa bakin azumi da ya shirya kuma ya gayyace su a fadar gwamnati da ke cikin birnin Gombe
  • Gwamna Inuwa Yahaya ya jaddada kudirin gwamnatinsa na zamanatar da makarantun Tsangaya domin bunkasa ilimin Alƙur'ani

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Gombe - Ƙungiyar Malaman Tsangaya a jihar Gombe ta karrama Gwamna Inuwa Yahaya da lambar yabo ta ‘Khadimul Qur’an’ bisa gudunmuwarsa ga ilimin Alƙur’ani da kyautata tsarin almajiranci.

An gabatar da wannan girmamawa ne a wani taron buɗa-baki na musamman da mai girma gwamna ya shirya a fadar gwamnati da ke Gombe.

Gwamna Inuwa Yahaya
Malaman Tsangaya sun ba Gwamna Inuwa Yahaya lambar yabon Khadimul Qur'an Hoto: @GovernorYahaya
Asali: Twitter

Aminiya ta tattaro cewa malaman Tsangaya daga sassa daban-daban na jihar Gombe da ke Arewa maso Gabashin Najeriya sun halarci buɗa bakin.

Kara karanta wannan

Shugaba Tinubu ya halarci wurin tafsir, ya roƙi musulmi alfarma a Ramadan

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Gwamna Inuwa ya shirya buɗa baki

Taron na ɗaya daga cikin tarurrukan da Gwamna Inuwa Yahaya ya saba shirya wa duk shekara domun shan ruwa tare da jama’a, wanda ke ƙarfafa haɗin kai da zaman lafiya a tsakanin al’ummar Musulmi.

A bayaninsa bayan buɗa-bakin, Gwamnan Inuwa ya jaddada aniyarsa na inganta rayuwar malaman Tsangaya da Almajirai, tare da samar da yanayi mai dacewa don koyarwa da koyo.

Hidimar da gwamnan ya yi wa Al-Kur'ani

Ya bayyana cewa gwamnatinsa ta gina manyan makarantun Tsangaya da na almajirai tare da haɗa ilimin Alƙur’ani da na zamani a cikin tsarin karatu.

Haka kuma, ya tabbatar da cewa an sanya yara almajirai cikin shirin lafiya na Go-Health domin samun ingantaccen kiwon lafiya.

“Mun fahimci rawar da makarantun Tsangaya ke takawa wajen tarbiyya da ilimi, shi ya sa muka ɗauki matakai daban-daban don kyautata jin daɗinsu, ciki har da gina sabbin makarantu da kuma bai wa Almajirai damar samun kiwon lafiya kyauta,” in ji Gwamnan.

Kara karanta wannan

Tallafin Ramadan ya haɗa rigima, gwamna da jam'iyya sun fara nuna wa juna yatsa

An naɗa Gwamna Inuwa Khadimul Qur'an

A nasa jawabin, jagoran malaman Tsangaya, Goni Mai Babban Allo, ya yaba wa Gwamna Inuwa Yahaya bisa ƙoƙarin da yake yi wajen tallafa wa tsarin Tsangaya.

Ya jaddada cewa wannan gwamnati ta fi kowacce nuna kulawa ga malamai da ɗalibai, ta hanyar samar da fitilu masu aiki da hasken rana a makarantun Tsangaya da kuma shigar da almajirai cikin shirin kula da lafiya.

Gwamna Inuwa Yahaya.
Gwamma Inuwa Yahaya ya jaddada kudirinsa na inganta makarantun tsangaya a Gombe Hoto: Muhammed Inuwa Yahaya
Asali: Facebook

Domin girmamawa ga irin wannan namijin ƙoƙari, ƙungiyar Alarammomi ta naɗa Gwamnan a sarautar ‘Khadimul Qur’an’, wanda ke nuna kasancewarsa bawan Alƙur’ani mai sadaukarwa.

Sayyada Amina Sheikh Dahiru Bauchi, mai bai wa gwamna shawara kan harkokin Tsangaya da Ilimin Almajiranci, ta yi kira ga Alarammomi da su ci gaba da yin addu’a domin zaman lafiya da ci gaban jihar Gombe.

An fara musayar yawu kan tallafin azumin Gombe

A wani labarin, kun ji cewa jam'iyyar PDP ta caccaki Gwamna Inuwa Yahaya kan kayan tallafin Ramadan da aka fara rabawa a jihar Gombe.

Kara karanta wannan

Rikicin sarauta ya ƙara tsanani, Sarki ya yi sabon naɗin da zai iya tayar da ƙura

PDP ta yi ikirarin cewa tallafin daga gwamnatin tarayya ya fito amma hadimin Gwamna Inuwa ya ce zargin ba gaskiya ba ne.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262

Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng