Gwamna Ya Zubar da Hawaye a cikin Taro, Ya Bayyana Abin da Ya Sosa Masa Zuciya

Gwamna Ya Zubar da Hawaye a cikin Taro, Ya Bayyana Abin da Ya Sosa Masa Zuciya

  • Gwamna Siminalayi Fubara na jihar Ribas ya bayyana yadda abu ya taɓa zuciyarsa har ya zubar da hawayen tausayi a kwanakin baya
  • Fubara, wanda ke fama da rikicin siyasa ya ce ya ji matuƙar tausayi a lokacin da sarkin Akprlor ya ba shi labarin ba su da fada a masarautarsa
  • Gwamnan na jihar Ribas ya buƙaci magoya bayansa su ci gaba da haƙuri kuma su bi tafarkin zaman lafiya domin za su ci ribar hakan a ƙarshe

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Rivers - Gwamnan jihar Ribas, Siminalayi Fubara, ya bayyana yadda wani abu ya taba zuciyarsa har ya zubar da hawaye.

Gwamna Simi Fubara ya ba da labarin ne a wurin kaddamar da fadar Nyeweali ta masarautar Akpor da kuma gidan zaman sarki, Mai kartaba Eze Levi Amor Oriebe.

Kara karanta wannan

'Dan takarar shugaban kasa a SDP ya fadi yadda aka jawo El Rufai daga APC

Gwamna Fubara
Gwamna Fubara ya zubar da hawaye lokacin da y asaurari sarkin Akpor a jihar Ribas Hoto: Sir Siminalayi Fubara
Asali: Facebook

Jaridar Daily Trust ta tattaro cewa Gwamna Simi Fubara ne ya fara aikin gina fada da gidan sarkin kuma ya kammala aikin a halin yanzu.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Da yake magana a wajen kaddamar da fadar Nyeweali, Fubara ya ce yana farin ciki cewa gwamnatinsa na yin ayyukan da ke shafar rayuwar jama’a kai tsaye.

Duk da rikicin siyasar da ake fama da shi a jihar, gwamnan ya bukaci al’ummar Ribas da su kasance masu bin doka da oda da zaman lafiya, yana mai cewa za su ci ribar hakan a ƙarshe.

Dalilin da ya sa gwamna ya zubar da hawaye

Fubara ya ce kimanin watanni 10 da suka gabata, da yake kaddamar da aikin gyaran titin Okania-Ogbogoro a karamar hukumar Obi Akpor, mutanen yankin sun roƙe shi da ya gina fadar masarautar Akpor.

Gwamnan ya ce:

"Na ji matukar tausayi da har hawaye ya zubo mani a lokacin da Mai Martaba Sarki ke magana, ya ce, ‘Tun bayan kafuwar masarautar Akpor fiye da shekaru 200 da suka gabata, ba ta taɓa samun fada ba har yau.’

Kara karanta wannan

Abubuwan da suka jawo El Rufai ya yi sallama da APC, ya burma jam'iyyar SDP

"Amma Allah ba ya yin kuskure. Watakila, ya bar shi ne don gwamnatina ta cika wannan tarihi, domin mu zama wani bangare na tarihinsu har abada."

Gwamna Fubara ya gina wa Sarki sabon gida

Gwamnan ya kara da cewa gwamnatinsa ba fada kaɗai ta gina ba, har ma da wani gida da za ta mallaka wa sarki, don tabbatar da cewa bayan karewar wa’adinsa ko wani abu ya faru, iyalansa za su samu wurin zama mai kyau.

"Mun fahimci cewa fada mallakin kowa ne, amma bayan wa’adin sarki ko kuma idan kaddara ta yi halinta, iyalansa ba za su zauna a fadar ba.
"Saboda haka, mun gina masa gida domin ya ci gaba da jin dadin rayuwa ko bayan barinsa fada," in ji shi.
Gwamna Fubara.
Gwamnan jihar Ribas ya kaddamar da sabuwar fadar Akpor, ta farko cikin shekaru 200 Hoto: Sir Siminalayi Fubara
Asali: Facebook

Gwamna ya bukaci jama’a su ƙara hakuri

A cikin jawabinsa, Fubara ya bukaci magoya bayansa da su danne zuciyoyinsu su ci gaba da bin tafarkin na zaman lafiya, yana mai cewa Allah ba ya fara abu, ya bar shi a rabi.

Kara karanta wannan

Rikici ya ƙara Kamari, jam'iyyar APC ta buƙaci gwamna ya yi murabus cikin sa'o'i 48

Gwamna Fubara ya yi kira ga al’ummar jiharsa da su ci gaba da zama cikin kwanciyar hankali, yana mai tabbatar musu da cewa za su fita da karfi daga kalubalen da ake fuskanta.

Ya bukaci jama’a da su guji tashin hankali, yana mai gargadi cewa idan wata fitina ta tashi, su ne za su fi shan wahala. "Ku ci gaba da bin tafarkin zaman lafiya," ya kara da nanatawa.

Fubara ya ce:

"Na san wasu daga cikin ku sun cika da kwarin gwiwa, wasu kuma suna jin cewa ba a kan turbar nasara muke ba. Amma ina tabbatar muku da abu guda: Allah ba ya fara abu ya bari a rabi.
"Duk abin da ke faruwa a yau, zan tabbatar muku da cewa za mu fito da karfi fiye da da. Ku ci gaba da bin tafarkin zaman lafiya, domin idan wani abu ya faru, mu ne za mu fi shan wahala."

Kara karanta wannan

'Shiga fim ne ya hana ni zama malamin Musulunci': Jarumin Kannywood ya fadi gaskiya

APC ta ba Fubara wa'adi ya yi murabus

A wani labarin, kum ji cewa APC mai adawa a jihar Ribas ta bukaci Gwamna Simi Fubara ya yi murabus daga muƙaminsa cikin sa’o’i 48.

APC ta zargi gwamnan da karya dokokin kundin tsarin mulki, kuma ta yi barazanar cewa Majalisa za ta tsige shi idan bai sauka ta lalama ba.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262