"Bai Mutu ba," Gwamnatin Taraba Ta Fadi Halin da Mataimakin Gwamna ke ciki
- Gwamnatin Taraba ta bayyana dalilin da ya sa aka daina ganin mataimakin gwamnan jihar, Aminu Abduallahi Alkali
- Tun a watan Nuwamba na shekarar 2024 rabon da a ga mataimakin gwamnan a cikin jama'a ko al'amuran gwamnatin Taraba
- Lamarin ya jefa masu ruwa da tsaki a Taraba a cikin damuwa, har ta kai ana tambayar halin da Aminu Alkali ya ke ciki
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Taraba – Bayan watanni ana ta hasashe kan inda mataimakin gwamnan Taraba ya shiga, gwamnatin jihar ta bayyana cewa Aminu Alkali ba shi da lafiya.
Kwamishinar yaɗa labarai da wayar da kai a jihar Taraba, Zainab Usman da ta bayyana haka, ta ce mataimakin gwamnan na fama da cutar shanyewar ɓarin jiki.

Asali: Facebook
Jaridar Leadership ta wallafa cewa tun daga watan Nuwamba na 2024, aka daina ganin Alkali a bainar jama’a, labarin da ya haifar da damuwa a tsakanin al’ummar ciki wajen jihar.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Halin da mataimakin gwamnan Taraba ke ciki
Kwamishinar yaɗa a labarai da wayar da kai ta Taraba, Zainab Usman, ta tabbatar da cewa mataimakin gwamnan ya fara karbar magani a Abuja
Amma ta ce daga baya, an ɗauke shi daga Abuja, an mayar da shi birnin Alkahira a kasar Masar domin ci gaba da jinya da kuma samun kulawar kwararru.
Ta bayyana haka ne a yayin da take bayani kan rashin ganin Aminu Alkalai bayan taron Majalisar zartarwar jihar da aka gudanar a ranar Litinin.
Mataimakin gwamnan jihar Taraba zai koma aiki
Gwamnatin Taraba ta bukaci al’ummar jihar da su taya mataimakin gwamna, Aminu Alkali addu'ar samun lafiya bayan tsintar kansa a cikin tsananin rashin lafiya.

Asali: Facebook
Kwamishinar yaɗa labarai ta jihar, Zainab Usman ta ce:
"Rashin lafiya abu ne da ke shafan kowa."
Ta yi watsi da batun cewa Alkali ba shi da ikon ci gaba da rike mukaminsa, tana mai cewa ci gaba da zama a ofis ya dogara ne kacokan ga gwamna Agbu Kefas.
Kwamishinar ta ce:
“Bari in yi magana a matsayin lauya yanzu. A bisa ilimina, wannan ka’ida ta kwanaki 90 tana aiki ne kawai ga gwamnan jiha mai ci, ba mataimakin gwamna ba.
Wanda zai tantance ko yana da cancantar ci gaba da zama a ofis shi ne gwamna."
"Mataimakin gwamnan Taraba na samun lafiya"
Kwamishinan lafiya na Taraba, Bordiya Buma, wanda kwanan nan ya kai ziyara ga mataimakin gwamna a Masar, ya bada karin bayani kan halin da yake ciki
Ya ce:
"Ya kamu da shanyewar barin jiki, wadda ta shafi wani ɓangaren jikinsa, ta haddasa masa rauni a gefen jiki guda, kuma ta hana shi iya magana yadda ya kamata."

Kara karanta wannan
Ana batun cin zarafin Sanata, Remi Tinubu ta bukaci karin wakilcin mata a majalisa
Amma godiya ta tabbata ga Allah, kuma muna farin ciki da yadda yake samun sauki. Muna fatan nan ba da dadewa ba, zai dawo jihar domin ci gaba da aikinsa."
Taraba: Jama'a na neman mataimakin gwamna
A wani labarin, kun ji cewa bayan kusan watanni uku na rashin ganin mataimakin gwamna, al’ummar Jihar Taraba sun shiga ruɗani tare da neman bayani .
Tun daga ranar 11 ga Nuwamba 2024, babu wanda ya sake jin duriyar Alhaji Aminu Alkali, lamarin da ya jefa jama’a cikin damuwa da hasashe kan halin da yake ciki.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng