An Fara: Tsohon Ministan Buhari Ya Goyi Bayan Tafiyar El Rufa'i a Jam'iyya SDP

An Fara: Tsohon Ministan Buhari Ya Goyi Bayan Tafiyar El Rufa'i a Jam'iyya SDP

  • Tsohon Ministan Wasanni, Solomon Dalung, ya ce jam’iyyun APC da PDP sun gaza ceto Najeriya daga matsalolin da take ciki
  • Barista Solomon Dalung ya bayyana cewa jam’iyyar SDP ita ce makomar siyasar Najeriya kuma za ta dawo da martabar kasa
  • Wasu 'yan Najeriya sun bayyana ra’ayoyinsu kan sauya shekar El-Rufai zuwa SDP da maganar da Dalung ya yi kan jam'iyyar

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja - Tsohon Ministan Wasanni, Solomon Dalung, ya bayyana cewa Najeriya ta bata hanya tun bayan shekarar 1993.

A karkashin haka Solomon Dalung ya bayyana cewa lokaci ya yi da za a koma inda aka bata domin dawo da martabar kasar nan.

Dalung
Dalung ya bukaci a shiga SDP. Hoto: Barrister Solomon Dalung
Asali: Facebook

Tsohon Minista ya jima a jam'iyyar SDP

Tsohon ministan ya bayyana haka ne a cikin wani sako da ya wallafa a shafinsa na Facebook a ranar Talata.

Kara karanta wannan

'Jam'iyyar APC za ta fadi warwas a babban zaben shekarar 2027'

Dalung, wanda ya yi jawabin jim kadan bayan sauya shekar tsohon gwamnan Kaduna, Nasir El-Rufai, zuwa SDP, ya caccaki APC da PDP, yana mai cewa ba su cika alkawarin da suka dauka ba.

A cewarsa, PDP ta kasa ba wa al’umma kariya, yayin da APC ke kara jefa jama’a cikin talauci da yunwa.

Solomon Dalung ya soki PDP da APC

Solomon Dalung ya bayyana cewa Najeriya na bukatar sabon shugabanci da zai gyara kura-kuran da aka tafka tun 1993.

Tsohon ministan ya ce:

“Lema (PDP) ba ta kare jama’a ba, tsintsiya (APC) maimakon ta share cin hanci, sai ta jawo talauci, yunwa, rashin adalci da danniya.”

Dalung ya ce jam’iyyar SDP ita ce makomar siyasar Najeriya, yana mai cewa:

“Farin doki (SDP) shi ya kamata a fuskanta, Najeriya za ta fita daga wannan yanayi da take ciki.”

Kara karanta wannan

Tsohon gwamna ya fice daga jam'iyyar APC mai mulki? An samu gaskiyar bayani

Kaduna
El-Rufa'i bayan komawa SDP. Hoto: Nasir El-Rufa'i
Asali: Twitter

Jama’a sun tofa albarkacin bakinsu

Bayan wannan jawabin Solomon Dalung, jama’a da dama sun tofa albarkacin bakinsu a shafukan sada zumunta, musamman Facebook.

Wani mai suna Francis Kargwak Zitta ya ce:

“Mutanen da suka fito daga lema sun koma tsintsiya, yanzu kuma sun koma doki! Ba tambarin jam’iyya ba ne matsala, matsalar ita ce shugabanni.”

Shi kuwa Baban Nana ya ce:

“Tabbas, miliyoyin ‘yan Najeriya masu tunani mai kyau za su rungumi wannan ra’ayi ba tare da shakka ba.”

Wasu sun goyi baya, wasu sun tambayi Dalung

Wasu sun goyi bayan Dalung, yayin da wasu suka bukaci karin bayani kan dalilan da suka sa suke ganin SDP ita ce mafita.

Ahmed Danladi ya yi tambaya da cewa:

“Ka na nufin SDP ita ce mafita?”

Shi kuwa Muhammad S Abubakar ya ce:

“Mun samu karuwa, barka da shigowa, ranka ya dade.”

Kara karanta wannan

Fadar shugaban ƙasa ta yi magana kan sauya sheƙar El Rufai daga APC zuwa SDP

Abdulraheem Adamu Bappa ya yi kashedi, yana mai cewa:

“Ba da wuri ba ake yanke hukunci ba. Ina ganin mu jira mu ga yadda wasan siyasar zai kaya.”

Hussaini Samaila Mani ya ce:

“Za mu hade domin gina Najeriya tare.”

El-Rufa'i zai hada kan 'yan adawa a SDP

A wani rahoton, kun ji cewa tsohon gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufa'i ya ce zai hada kan 'yan adawa domin tunkarar APC a zabuka.

Nasir El-Rufa'i ya bayyana haka ne a cikin wani bayani da ya yi na nuna fitar sa daga jam'iyyar APC zuwa jam'iyyar adawa ta SDP a makon nan.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng