'Jam'iyyar APC za Ta Fadi Warwas a Babban Zaben Shekarar 2027'

'Jam'iyyar APC za Ta Fadi Warwas a Babban Zaben Shekarar 2027'

  • Wani jigo a PDP, Kelvin Ogboru ya ce jam’iyyar APC ba za ta yi nasara ba a 2027, ya kwatanta ta da gini mai rauni da zai rushe
  • Ya jaddada cewa babu madadin Gwamna Sheriff Oborevwori a Delta, yana mai yabawa da kokarinsa wajen ci gaban al'umma
  • Ogboru ya bukaci masu rike da mukamai a gwamnati su kara kokari wajen wayar da kan al'umma da goyon bayan PDP a zaben 2027

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Delta - Mataimaki na musamman ga Gwamna Sheriff Oborevwori, Kelvin Ogboru, ya bayyana cewa jam’iyyar APC za ta sha kaye a zaben 2027.

A wata tattaunawa da manema labarai a taron matasa da aka gudanar a Delta ta Tsakiya, Ogboru ya ce babu mai iya karawa da Gwamna Oborevwori a jihar Delta.

Kara karanta wannan

An fara: Tsohon ministan Buhari ya goyi bayan tafiyar El Rufa'i a jam'iyyar SDP

Ganduje
Jigon PDP ya fadi yadda APC za ta sha kaye a 2027. Hoto: Salihu Tanko Yakasai
Asali: Twitter

Jaridar Vanguard ta rahoto cewa Ogboru ya kwatanta jam’iyyar APC da kungiya maras alkibla da ke fatan samun nasara wajen amfani da gwamnati.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

PDP za ta yi nasara a Delta inji Ogboru

Kelvin Ogboru ya bayyana cewa PDP za ta yi nasara sosai a jihar Delta, domin Gwamna Oborevwori yana aiwatar da manyan ayyukan raya kasa.

A cewarsa, tsarin MORE Agenda na gwamnan ya kawo ci gaba da dama ga al’ummar Delta, kuma hakan zai tabbatar da zarcewarsa a 2027.

Ogboru ya kara da cewa:

"Gwamna Oborevwori ba dan kansa yake ba, jama’a ne ke gabansa.
"Yana aiki kamar yadda manyan shugabanni na duniya irin su Lee Kuan Yew suka mayar da hankali wajen inganta rayuwar jama’a."

Ogboru ya ce APC ba ta da alkibla

Da yake magana kan jam’iyyar APC, Ogboru ya bayyana cewa ba ta da shugabanci mai karfi kuma ba ta da hadin kai a jihar Delta.

Kara karanta wannan

Gwamna ya zubar da hawaye a cikin taro, ya bayyana abin da ya sosa masa zuciya

A cewarsa:

"APC jam’iyya ce da ba ta da tsari. Har yanzu suna neman wanda za su tsayar a 2027, yayin da PDP ta riga ta kafu da shugaba mai hangen nesa."

Ogboru ya zargi APC da dogaro da gwamnatin tarayya wajen ganin ta yi nasara a zabe, maimakon ta fito da manufofi na gaskiya da za su amfanar da jama’a.

Kiraye-kirayen goyon bayan Oborevwori

Ogboru ya bukaci dukkan masu rike da mukamai a gwamnatin Oborevwori da su kara azama wajen fadakar da jama’a kan nasarorin PDP a jihar.

A cewarsa:

"Nasarar zaben 2027 za ta kasance ga PDP, domin mutane za su zabi ci gaba a kan rudani, kuma za su zabi shugabanci nagari a kan siyasar son zuciya."

Ya ce PDP za ta ci gaba da jan ragamar jihar Delta, domin ta riga ta kafa tubalin ci gaba mai dorewa.

Kara karanta wannan

"PDP ta mutu murus," Minista ya fadi yadda Tinubu zai yi nasara a zaben 2027

Gwamnan Delta
Gwamnan jihar Delta. Sheriff Oborevwori. Hoto: Delta State Government
Asali: Facebook

APC ta fara yi wa Tinubu kamfen a 2027

A wani rahoton, kun ji cewa jam'iyyar APC ta fara neman goyon baya ga shugaba Bola Tinubu a jihohin Arewa shekaru biyu kafin zabe.

An gudanar da taron siyasa a jihohi kamar Kaduna, Kebbi, Kwara da Abuja inda aka bukaci a ba Bola Tinubu damar yin tazarce a 2027.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng