'Yan Bindiga Sun Farmaki Wani Ɗan Takarar Jam'iyyar APC, Sun Aika Shi Lahira
Wasu ‘yan bindiga sun kashe ɗan siyasa, Oluwatosin Onamade, a kofar gidansa da ke Ijede, Ikorodu, jihar Legas, bayan sun sare shi da adda
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
- Ɗan uwansa, Oluwafemi Onamade, ya danganta kisan ga siyasa, yana mai cewa marigayin ya fito takarar ciyaman kuma yana da tarin mabiya
- Rundunar 'yan sandan Legas ta tabbatar da faruwar lamarin yayin da kakakinta, Benjamin Hundeyin ya bayyana matakin da suka dauka
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Legas - Wasu 'yan bindiga sun yiwa wani ɗan siyasa, Oluwatosin Onamade, kisan gilla a yankin Ijede da ke Ikorodu, jhar Legas.
Rahotanni sun nuna cewa marigayin yana neman kujerar shugabancin ƙaramar hukumar Ijede a ƙarƙashin jam'iyyar APC kafin rasuwarsa.

Asali: Twitter
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
'Yan bindiga sun kashe dan takarar APC
Ɗan uwansa, Oluwafemi Onamade, ya bayyanawa jaridar Punch cewa maharan sun dade suna bibiyar yayan nasa kafin su kashe shi a ranar Asabar da dare.

Kara karanta wannan
Kano: Fashewar tukunyar gas ta jawo asarar rai, ƴan sanda sun ɗauki matakin gaggawa
A wata hira da jaridar, Oluwafemi Onamade ya ce maharan sun sa baƙaƙen kaya, ta yadda babu wanda zai iya gane su a lokacin da suka kai harin.
Ya ƙara da cewa yana tare da yayan nasa lokacin da aka kai musu wani hari makamancin haka a shekarun baya, amma suka tsallake rijiya da baya.
A cewarsa, 'yan bindigar sun harbi Onamade, amma harsasan ba su ji masa ciwo ba, sai suka sassare shi da adduna a kai da fuska har ya mutu, inji Sahara Reporters.
Legas: Yadda aka kashe dan siyasa a kofar gidansa
Oluwafemi Onamade ya shaida cewa:
"Abin ya faru ne da misalin ƙarfe 9:00 na daren ranar Asabar. ‘Yan bindigar su biyu ne, sun saka baƙaƙen kaya, kuma ba wanda ya iya gane su.
"Hadiminsa ya ce ya gaza ci gaba da tsayawa a wajen a lokacin da ya ji karar harbe-harben bindiga, sai ya tsere.
"Sun harbe shi (Oluwatosin) tare da sassara shi da adda a kofar gidansa. Lamarin ya faru ne a gidansa da ke Ijede, a layin Oluwatosin Onamade, wanda aka sanya wa sunansa.
"Da farko sun harbe shi, amma da harsasan ba su shige shi ba, sai suka yi amfani da adduna, suka sassare shi a kai da fuska."
Oluwafemi ya danganta kisan dan takarar ga harkokin siyasa, yana mai cewa, "Onamade yana da rinjaye da mabiya da dama, shi ya sa suka kashe shi."
Rundunar 'yan sanda ta tabbatar da lamrin

Asali: Facebook
Ya bayyana cewa a shekarar 2021 an kai wa Oluwafemi makamancin wannan harin, inda har yanzu wasu daga cikin maharan ke tsare a gidan yari, amma ba a yanke musu hukunci ba.
Wannan lamari ya janyo cece-kuce a tsakanin al’umma, musamman dangane da jinkirin shari’a da rashin gurfanar da maharan a gaban kuliya cikin gaggawa.
Har yanzu jam’iyyar a matakin ƙasa da jiha ba ta fitar da wata sanarwa kan abin da ya faru da dan takarar ta ba, lamarin da ya haifar da shakku da tambayoyi daga magoya bayan jam’iyyar da masu bibiyar harkokin siyasa.
Wasu na ganin shiru da jam’iyyar ke yi na iya kasancewa wata dabara ta kauce wa yin gaggawar yanke hukunci kan lamarin, yayin da wasu ke ganin hakan wata alama ce ta rashin tsari ko rarrabuwar kawuna a cikin jam’iyyar.
Bayanin 'yan sanda
Amma, kakakin rundunar ‘yan sandan Legas, CSP Benjamin Hundeyin, ya tabbatar da faruwar lamarin, yana mai cewa tuni aka fara gudanar da bincike.
Ya bayyana hakan ne a cikin wata saƙon kar-ta-kwana da ya aike wa manema labarai a ranar Litinin, 10 ga watan Maris, 2025.
A cewar sa, hukumomi na aiki tukuru don gano hakikanin musabbabin harin tare da gano wadanda ke da hannu a ciki.
Sai dai har yanzu ba a bayyana ko an kama wani mutum dangane da wannan harin ba, lamarin da ke kara tayar da hankali a tsakanin jama’a.
'Yan bindiga sun kashe dan takarar APC a Ogun
A wani labarin makamancin wannan, mun ruwaito cewa, ‘yan bindiga sun kashe ɗan takarar kansila na jam’iyyar APC a jihar Ogun.
Maharan sun harbe Adeyinka Adeleke har lahira a unguwar Jide Jones, cikin ƙaramar hukumar Abeokuta ta Kudu, lamarin da ya jefa mutane a firgici.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Salisu Ibrahim ya fadada labarin ta hanyar zakulo tarihin shari'ar da kuma bayanan 'yan sanda.
Asali: Legit.ng