Bayan El Rufai Ya Koma SDP, Babbar Jigon Matan Arewa Ta Fice daga Jam'iyyar APC
- Tsohuwar kwamishina a Kaduna, Hajiya Hafsat Baba ta sanar da murabus dinta daga APC, tana mai cewa jam’iyyar ta rasa alkiblarta
- Bayan ficewar Malam Nasir El-Rufai daga APC zuwa SDP, Hajiya Hafsat ta bi sahunsa, tana nuna aminci da biyayya ga tsohon ubangidanta
- Ana ganin cewa ficewar Hajiya Hafsat na iya kara rikita APC a Kaduna, musamman idan wasu manyan ‘yan siyasa suka bi bayanta
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Kaduna – Siyasar APC a Kaduna na ci gaba da fuskantar kalubale yayin da daya daga cikin jiga-jiganta, Hajiya Hafsat Mohammed Baba, ta sanar da ficewarta daga jam’iyyar.
Hajiya Hafsat, tsohuwar kwamishinar walwala da jin ƙan al’umma ta jihar Kaduna, ta aika takardar murabus dinta ga shugaban APC na Unguwar Sarki, Kaduna ta Arewa.

Asali: Twitter
Tsohuwar kwamishinar Kaduna ta fice daga APC
Takardar ficewarta daga APC, wadda ta dora a shafinta na X a ranar Litinin, na dauke da kwanan wata 10 ga Maris, 2025.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Hajiya Hafsat, wadda tsohuwar shugabar mata ta jam’iyyar ACN (da aka rusa) ce, ta ce APC ta rasa alkiblarta kuma ba za ta iya ci gaba da kasancewa a cikinta ba.
An rahoto cewa Hajiya Hafsat ta yi aiki a matsayin kwamishinar walwala da jin kai a gwamnatin Malam Nasir El-Rufai daga 2017 zuwa 2023.
Rahotanni na nuna cewa ficewarta daga APC tana da alaka da barin jam’iyyar da Malam El-Rufai ya yi a ranar Litinin domin komawa SDP.
Kwamishinar ta fadi dalilin barin jam'iyyar APC
A cikin wasikar murabus dinta, ta bayyana cewa burinsu lokacin da suka kafa APC shine inganta adalci da kyakkyawan tsarin shugabanci a Najeriya, amma a cewarta, jam’iyyar ta kauce daga wannan hanya.
"Jam’iyyar ta rasa tsarinta da manufarta, ta kauce daga tafarkin adalci, zaman lafiya da hadin kai da muka kafa ta a kai.
"Ni mai tsayawa kan waɗannan ka’idoji ne, don haka ba zan iya ci gaba da kasancewa cikin jam’iyyar APC a halin da take ciki ba."
- Hajiya Hafsat.
Kalubalan da APC ka iya fuskanta a Kaduna

Asali: Twitter
El-Rufai zai iya janye 'yan APC a Kaduna
Wannan mataki nata ya zo ne 'yan awanni bayan da ubangidanta, Malam Nasir El-Rufai ya bayyana ficewarsa daga APC zuwa SDP.
Legit Hausa ta ruwaito cewa tsohon gwamnan na Kaduna ya zargi jam’iyyar da saba wa manufofin da suka jawo kafa ta a shekarar 2013.
Masana siyasa na ganin cewa ficewar Hajiya Hafsat wani bangare ne na biyayya da aminci ga El-Rufai, kuma hakan na iya nuni da yiwuwar shigarta SDP tare da sauran magoyanta.
A halin yanzu dai, ana sa ran karin wasu mukarraban El-Rufai za su bi sahunta, lamarin da ake ganin zai kara jawo ficewar jiga-jigan APC a Kaduna.
Karanta takardar murabus din a nan kasa:
"Ficewar El-Rufai, ko a jikinmu" - APC
A wani labarin, mun ruwaito cewa, jam’iyyar APC reshen Kaduna ta yi martani kan sauya sheƙar Mallam Nasir Ahmad El-Rufai zuwa SDP.
Sakataren jam’iyyar a jihar, Yahaya Baba-Pate, ya bayyana cewa ficewar tsohon gwamnan ba ta zama abin damuwa ko kadan ga APC ba.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng