'Dan Takarar Shugaban Kasa a SDP Ya Fadi Yadda Aka Jawo El Rufai daga APC
- Tsohon dan takarar shugaban kasa a SDP, Adewole Adebayo ya bayyana jin dadin yadda su ka yi nasarar farauto Nasir El-Rufa'i zuwa jam'iyyarsu
- Ya bayyana cewa sai da aka sha tattauna wa kafin a yi nasarar shawo kan tsohon gwamna, amma ya na ganin akwai ra'ayoyin da ba za su dauka ba
- Kalamansa na zuwa ne a lokacin da fadar shugaban kasa ke ganin Nasir El-Rufa'i ba shi da wani tasiri a siyasa da zai sa ta yi dar don ya fice daga cikinta
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
FCT Abuja - Tsohon dan takarar shugaban kasa na SDP, Adewole Adebayo, ya bayyana Nasir El-Rufa'i a matsayin babban kadara ga jam’iyyar.
Ya kuma yaba da tsohon gwamnan, wanda ya bayyana a matsayin shugaba mai kyakkyawan tarihin shugabanci.

Asali: Twitter
A wata hira da ya yi da Channels TV, Adebayo ya jinjinawa basirar tsohon gwamnan, wanda ya mulki Kaduna har sau biyu.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
"Nasir El-Rufa'i na da rauni" – Jigon SDP
Amma a zantawar da aka yi da shi, ya ce akwai wasu abubuwa da ya dace El-Rufa'i ya gyara.
'Dan takarar shugaban kasa a inuwar SDP a zaben 2023, Adewole Adebayo, ya bayyana cewa Nasir El-Rufa'i na da raunin da ya kamata ya gyara sannu a hankali.
Ya ce:
“Matsalar ita ce, ina ganin shi a matsayin kadara—mutum mai kwazo wanda ke da tarihin aikin gwamnati da za a iya kwatanta da shi."
"Ina ganin yana da rauni da ya kamata ya gyara, amma ba ni ne mai ba shi shawara ko malamin gyaran hali ba.”
Jam'iyyar SDP ta yi maraba da El-Rufa'i
A ranar Litinin, 10 ga Maris, 2025, El-Rufa'i ya sanar da ficewarsa daga APC mai mulki zuwa jam’iyyar adawa ta SDP domin a hada karfi gabanin zabe mai zuwa.
A jawabinsa na lale, Adebayo ya bayyana cewa SDP ta karbi El-Rufai hannu bibbiyu kuma tana murna da karin da ta samu.

Asali: Facebook
Ya ce:
“Najeriya kasa ce mai bambance-bambance, kuma za ka samu masu kishinta a kowane bangare."
Sai dai ya jaddada cewa mutane kada su yi mamaki idan nan da wasu 'yan kwanaki shi da tsohon gwamnan suka samu sabani a kan wasu batutuwa.
'El-Rufa'i ya koyi darasi' – Jigon SDP
Tsohon dan takarar shugaban kasa ya ce El-Rufai ya koyi darasi a jam’iyyar APC, domin sun nuna masa abubuwa da dama da ya dace ya hankalta da su.
Jagoran ya ce:
“Za ka iya zargin El-Rufai da komai, amma ba za ka iya zarginsa da rashin tunani ba.
Abin da kawai zan ce shi ne ya shiga wata jam'iyya maras kima, amma yanzu ya koyi darasi. Amma hakan ba yana nufin cewa babu kwararru a APC ba—akwai su, sai dai ban yarda da manufofinsu ba.”
Yadda jam'iyyar SDP ta jajibo El-Rufai
Adebayo ya ce an dauki lokaci ana tattaunawa kafin El-Rufai ya yanke shawarar barin APC zuwa SDP, amma hakan ba ya nufin cewa za su yarda da duk ra’ayoyinsa.
Ya ce:
“Har yanzu akwai abubuwan da ake aiki akansu – wasu daga cikin ra’ayoyinsa da ya saba da su shekaru da suka gabata, SDP ba za ta yarda da su ba, kuma muna aiki a kan hakan.”
Babban abin da ya fi daukar hankali a yanzu shi ne irin tasirin da El-Rufai zai yi wajen kawo karshen mulkin APC a matakin kasa da jihar Kaduna.
SDP: Fadar shugaban kasa ta soki El-Rufa'i
A baya, kun ji cewa mai ba shugaban ƙasa shawara kan harkokin sadarwa da tsare-tsare, Daniel Bwala, ya ce Nasir El-Rufa'i ba shi da wani tasirin a zo a gani a siyasar Najeriya.
Ya jaddada cewa ba sabon abu ba ne a tarihin siyasar ƙasar cewa manyan 'yan siyasa na canza jam'iyya lokacin da abubuwa suka ƙi tafiya yadda suke so, domin 'yancinsu ne na 'yan kasa.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Salisu Ibrahim ya fadada labarin ta hanyar tsokaci kan makomar siyasar APC a Kaduna.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng