'Yan Arewa Sun Taso Ministan Buhari a gaba Ya Tsaya Takarar Shugaban Kasa a 2027
- Wata ƙungiya mai suna 'Young Nigerian Voices' ta bukaci tsohon minista, Emeka Nwajiuba ya tsaya takarar shugaban ƙasa a zaɓen shekarar 2027
- Shugaban ƙungiyar daga Arewa ta Tsakiya, Alhaji Aawul Mohammed Giri, ya ce Hon. Nwajiuba na da ƙwarewa da hangen nesa da zai mulki Najeriya
- Ƙungiyar ta ya ba da misalin rawar da Nwajiuba ya taka lokacin da ya kasance Ministan Ilimi, musamman wajen cigaban matasa da bangaren ilimi
- Wannan kira da aka sake yi masa a game da takarar shekarar 2027 na nuni da cewa ƙungiyar na son shugabancin kasa daga Kudu Maso Gabas
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
FCT, Abuja - Wata ƙungiyar siyasa mai suna 'Young Nigerian Voices' ta bukaci tsohon minista a gwamnatin Muhammadu Buhari ya fito takarar shugaban kasa.

Kara karanta wannan
Sarki Sanusi II ya karbi bakuncin kungiyar 'Obedient' a Kano, ya ba su shawarwari
Kungiyar ta roki Hon. Emeka Nwajiuba da ya tsaya takarar a zaɓen shekarar 2027 saboda kwarewarsa da hangen nesa.

Asali: Facebook
An roki ministan Buhari ya fito takara
An bayyana wannan kira ne a cikin wata sanarwa da mataimakin shugaban kungiyar ta ƙasa daga Arewa ta Tsakiya, Alhaji Aawul Mohammed Giri, ya fitar, cewar Tribune.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A cewar Giri, wannan kira ya biyo bayan bajintar Emeka Nwajiuba wajen hidimar jama’a da kuma ƙwarewarsa wajen gyara kura-kuran gwamnati mai ci.
Sanarwar ta ce:
"Yayin da yake matsayin Ministan Ilimi, Hon. Nwajiuba ya nuna ƙwazo wajen cigaban matasa da fannin ilimi a Najeriya.
“Gwanintarsa da gogewarsa sun sa ya cancanci fuskantar ƙalubale da dama da ƙasar ke fuskanta, ciki har da matsalolin tattalin arziki, lafiya da ababen more rayuwa.”
“Kiranmu ba kawai mun yanke shawararmu ba ne, mun yi nazari sosai kafin yanke hukuncin goyon bayansa.
“Muna da yakinin cewa Hon. Nwajiuba na da jajircewa, gaskiya da hangen nesa da za su amfani Najeriya da al’umma."

Kara karanta wannan
Zargin Shugaban Majalisa da neman lalata da matar aure ya riƙide, an samu wasiƙa daga Kogi

Asali: Facebook
Musabbabin kiran Nwajiuba tsayawa takara
Kungiyar ta ce wannan ba shi ne karon farko ba ta ke neman tsohon ministan ya tsaya takarar shugaban kasa ba saboda irin kwazo da yake da shi.
Ta ce har a zaben 2023 ma sai da ta yi wannan kira domin kwarewarsa a fannoni da dama musamman bangaren tattalin arziki.
“Ba wannan ne karon farko da muke nuna goyon baya ga Nwajiuba ba, a 2023 ma, mun bukaci a zabi shugaban ƙasa daga Kudu Maso Gabas.”
“Yayin da zaɓen shugaban ƙasa na 2027 ke karatowa, wannan goyon bayan da 'Young Nigerian Voices' ke bayarwa, na da muhimmanci matuƙa.”
“Yana nuna fatan samun shugaba mai haɗa kan al’umma, haɓaka tattalin arziki da samar da rayuwa mai kyau ga kowa, shin Nwajiuba zai karɓi wannan kira? Lokaci ne kawai zai bayyana hakan.
2027: Sanata Ningi zai nemi takarar gwamna
Kun ji cewa Sanata Ahmed Abdul Ningi ya bayyana niyyarsa ta tsayawa takarar gwamnan Bauchi a 2027 karkashin jam'iyyar PDP mai adawa a Najeriya.
Sanata Abdul Ningi ya fadi haka ne bayan ganawa da shugabannin jam’iyya a karamar hukumar Ganjuwa wacce ta ke karkashin mazabarsa a jihar.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng