El Rufa'i na Shirin Jan 'Yan APC zuwa SDP, Tinubu Ya Yi Magana kan Tallafin Fetur

El Rufa'i na Shirin Jan 'Yan APC zuwa SDP, Tinubu Ya Yi Magana kan Tallafin Fetur

  • Shugaban kasa Bola Tinubu ya ce an cire tallafin man fetur ne domin kare makomar 'yan kasa da za su rayu nan gaba
  • Tinubu ya bayyana hakan ne yayin kaddamar da kwamitin shirya taron matasa a fadar shugaban kasa da ke garin Abuja
  • Shugaban kasar ya bukaci matasa su rungumi damarmaki, yana cewa gwamnati za ta yi iya bakin kokari wajen inganta rayuwarsu

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja - Shugaban kasa Bola Tinubu ya ce cire tallafin man fetur daya ne daga cikin matakan da ya dauka domin kare makomar matasa da kuma tabbatar da ingantaccen ci gaban kasar nan.

Shugaban kasar ya bayyana haka ne yayin kaddamar da kwamitin shirya taron matasa na kasa a fadar gwamnati da ke Abuja.

Kara karanta wannan

Yaki da zaman banza: Tinubu na shirin samar da ayyuka ga matasa miliyan 10

Bola Tinubu
Bola Tinubu ya kaddanar da kwamitin taron matasa a Najeriya. Hoto: Bayo Onanuga
Asali: Facebook

Mai magana da yawun shugaban kasa, Bayo Onanuga ne ya wallafa jawabin Bola Tinubu a shafinsa na X.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A yayin jawabin, Tinubu ya tabbatar da cewa gwamnatinsa ta kuduri aniyar aiwatar da manufofin da za su samar da ingantacciyar makoma ga matasa.

Tinubu: Dalilin cire tallafin man fetur

Shugaban kasa ya bayyana cewa dukkan matakan da gwamnatinsa ke dauka, ciki har da cire tallafin man fetur, na nufin samar da kyakkyawar makoma ga matasan kasar.

Ya kara da cewa matasan Najeriya na da rawar da za su taka wajen gina kasa, don haka ya bukace su da su hada kai da gwamnati domin cimma burinsu da kawo ci gaba.

Shugaban ya bayyana cewa yana da yakinin cewa matasa na da basira da dabarun da za su taimaka wajen inganta rayuwa da samar da ci gaba mai dorewa.

Ya bukace su da su ci gaba da ba da shawarwari kan yadda kuke son abubuwa su kasance, yana mai jaddada cewa gwamnatin za ta yi kokarin aiwatar da duk abin da zai amfani kasa.

Kara karanta wannan

Bayan sauya shekar El Rufa'i, Tinubu ya ba gwamnoni da ministoci umarni

Bola Tinubu ya ce:

“An cire tallafin man fetur ne domin kare makomar ‘ya’yanmu da ke tafe. Idan aka samar da wadatar arziki a gida, mutane ba za su sha wahala suna ficewa zuwa ketare ba.”

Tinubu ya kuma bukaci matasa su dauki damarmaki da muhimmanci, yana mai cewa gwamnati a shirye take don tallafa musu domin su gina makomarsu.

Tattalin arziki na farfadowa – Tinubu

Shugaba Tinubu ya kuma bayyana cewa tattalin arzikin Najeriya na samun ci gaba a hankali, kuma hakan zai ci gaba da inganta.

Bola Tinubu ya ce:

“A farkon tafiyar mu, abubuwa sun kasance masu wahala, mun yi kokari sosai kamar masu kokarin debo ruwa daga rijiya busasshiya.
"Amma a yau, tattalin arziki na farfadowa, farashin kayayyaki na raguwa, kuma ‘yan kasuwa da masu zuba jari suna kara zuwa Najeriya.”

Tinubu ya bude kofar sauraron matasa

Ya kara da cewa matasan Najeriya suna da dama mai girma wajen gina kasa, inda ya bukace su da su hada kai da gwamnati domin cimma burinsu.

Kara karanta wannan

Saukaka sufuri: Za a samar da motoci masu aiki da lantarki 10,000 a Arewa

“Ina sauraren ku sosai, ku gaya mini duk abin da ba daidai ba, ku ba ni shawarwari kan yadda kuke son abubuwa su kasance.
"Za mu yi kokarin aiwatar da su matukar suna da alfanu ga kasa.”
Ministan matasa
Ministan matasan Najeriya. Hoto: Ayodele Olawande
Asali: Facebook

Gwamnati za ta tallafa wa matasa inji Tinubu

Tinubu ya jaddada cewa matasa su ne jigon cigaban Najeriya, kuma gwamnatin tarayya za ta yi iya kokarinta don tallafa musu.

Hakazalika, shugaban kasa ya ce matakan za su taimakawa wajen tabbatar da rayuwar matasa a Najeriya ta yi kyau.

Shugaban kasar ya ce:

“Zan tabbatar da cewa gwamnati ta yi duk mai yiwuwa domin tabbatar da Najeriya ta zama wuri mai kyau ga matasa.
"Amma ba za mu iya yin hakan mu kadai ba, domin ku ne fiye da kashi 60% na al’ummar kasar nan.”

Bola Tinubu ya ba gwamnoni umarni

A wani rahoton, kun ji cewa shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya bukaci gwamnoni da ministoci da su tausayawa talaka.

Kara karanta wannan

Tinubu ya fadi abin da ba a yi zato ba kan Osinbajo bayan zaben fitar da gwani a 2023

Bola Tinubu ta bukaci a yi tsare tsaren da za su taimaki talaka ne yayin wata liyafar buda baki da ya shirya a fadar shugaban kasa.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Salisu Ibrahim ya fadada labarin nan ta hanyar kara bayani kan matakan da gwamnati ta za ta dauka kan matasan kasa.

Wanda ya tantance Ibrahim Yusuf, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng

Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng