Kano: Fashewar Tukunyar Gas Ta Jawo Asarar Rai, Ƴan Sanda Sun Ɗauki Matakin Gaggawa
- Mazauna wani yanki na jihar Kano sun shiga fargaba bayan tukunyar gas ta fashe daga dakin girkin wani bawan Allah mai suna Isyaka Rabi'u
- Wani yaro mai shekara 14 ya koma ga Mahaliccinsa a sakamakon fashewar tukunyar gas ɗin, yayin da mutum sama da 20 su ka samu raunuka
- Rahotanni sun bayyana cewa jami'an ƴan sandan jihar da na kwana-kwana ne su ka wurin a tare, kuma sun bayar da gagarumar gudummawa
- Zuwa yanzu, mutanen da su ka ji raunuka sun rarrabu a asibitoci daban-daban na jihar, yayin da ƴan sanda su ka yi ta'aziyyar wanda ya rasu
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Kano - Wani yaro mai shekara 14 ya rasa ransa, yayin da wasu mutum 21 suka jikkata sakamakon fashewar tukunyar gas da ta auku a unguwar Goron Dutse da ke Kano. Lamarin ya faru ne da 2:30 na ranar Litinin, a gidan wani mutum mai suna Malam Isiyaka Rabiu, inda wata tukunyar gas da ke cikin dakin girkin gidansa ta tarwatse.

Asali: Twitter
Jaridar Leadership ta wallafa cewa bayan fashewar gas ɗin, gobara ta tashi a wasu sassan gidan kafin jami’an agaji su kawo ɗauki don rage asarar da za a samu.
Gobara a Kano: Ƴan sanda sun ɗauki mataki
Jaridar The Sun ta wallafa cewa wata sanarwa daga rundunar ‘yan sandan Jihar Kano, ta ce jami’an tsaro sun hanzarta zuwa wurin domin bayar da gudunmawa wajen shawo kan gobarar.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Asali: Facebook
Tawagar ‘yan sanda ƙarƙashin jagorancin ACP Nuhu Mohammed Digi na rundunar da ke yankin Dala sun isa wurin tare da jami’an kashe gobara domin dakile wutar da ta kama.
Kano: Wadanda gobara ta illata na asibiti
Rahotanni sun tabbatar da cewa an gaggauta kai waɗanda suka jikkata zuwa asibitoci daban-daban don samun kulawar gaggawa daga ƙwararru.
Daga cikin asibitocin da aka kai su akwai asibitin Gamji, asibitin ƙashi na Dala da kuma asibitin ƙwararru na Murtala Mohammed da ke cikin birni.
An yi nasarar shawo kan gobarar Kano
Bayanai sun nuna cewa an shawo kan gobarar kafin ɓarnar da ta yi ya faɗaɗa zuwa wasu wuraren da ke kusa da yankin, yayin da hankalin jama'a ya dawo jikin su.
Rundunar ‘yan sandan Kano ta mika ta’aziyyarta ga iyalan wanda ya rasu, tare da yabawa gaggawar da jami’an agaji suka yi wajen dakile barnar fashewar gas ɗin tare da ceton rayuka.
Mummunar gobara ta tashi a Kano
A baya, kun samu labarin cewa wata gobara da ta tashi a kauyen Danzago, karamar hukumar Dambatta a jihar Kano, ta hallaka dabbobi 78 ciki har da shanu, tumaki, awaki da kaji.
Kakakin hukumar kashe gobara ta Kano, Saminu Yusif Abdullahi, ya bayyana cewa ofishinsu da ke Dambatta ya samu kiran gaggawa daga wani Abdurashid Sha’aibu kan gobarar.
Da isar jami’an kashe gobara, sun tarar da wuta tana cin gidan Ado Yubai, wanda ke da girman ƙafa 200 x 200, tare da sassa tara da ɗakuna 17, kuma ta kashe dabbobi da dama.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng