Latest
Malaman makaranta da ma'aikatan lafiya sun yi zanga zanga a Abuja suna bukatar a kara masu albashin N70,000. Masu zanga zangar sun kewaye ofishin Nyesom Wike.
Bayan gwamnan Delta ya shiga APC, shugaban jam'iyyar na ƙasa, Abdullahi Ganduje, ya ce wasu gwamnoni daga PDP za su sauya sheƙa zuwa cikinta kafin zaɓen 2027.
Hukumar FGSHLB ta fara tattara jerin sunayen ma'aikatan da suka yi ritaya da suka kasa biyan cikakken lamunin gidajen da suka samu daga gwamnatin tarayya.
Jam'iyyar NNPP reshen jihar Kano, ta nuna rashin damuwarta kan sauya shekar da Sanata Abdulrahman Kawu Sumaila, ya yi zuwa APC mai adawa a jihar.
Hukumar tattara kudin shiga da raba su, RMAFC, ta yi karin haske kan albashin shugabanni inda ta ce bai da yawa kamar yadda ake tunani kuma bai karu tun 2007 ba.
Tsohon kakakin majalisar Kano, Kabiru Alhassan Rurum, wanda yanzu ke wakiltar Rano, Kibiya da Bunkure a majalisar wakilai, ya sanar da ficewarsa daga NNPP zuwa APC.
‘Yan bindiga da ake zargin makiyaya ne sun kashe sabon ango a Nasarawa, tare da sace amaryarsa. A Edo kuma, 'sun kashe magidanci tare da sace matarsa da ‘yar uwarta.
Sheikh Habeebullah Adam El-Ilory ya ce ya kamata a sake duba wasu koyarwar addini da suka sabawa ci gaban al’umma na yau duba fahimtar wasu malamai.
Gwamnan jihar Delta, Sheriff Obovrevwori, ya sauya sheƙa daga PDP zuwa APC a ranar Laraba, sakamakon rikici da ya mamaye PDP da wasu matsalolin siyasa a jihar.
Masu zafi
Samu kari