Hakeem Baba Ahmed: Tsohon Hadimin Kashim Ya Fadi Dalilin Ajiye Aiki a Aso Rock
- Dr. Hakeem Baba-Ahmed ya bayyana dalilin ajiye mukaminsa na Mashawarcin mataimakin shugaban ƙasa a kan harkokin siyasa
- Ya ce bai ga alamar cewa gwamnati na kan hanyar magance matsalolin da suka mamaye kasar nan ba, musamman wadanda ta gada
- Dr. Hakeem ya shawarci Shugaba Bola Ahmed Tinubu da sauran tsofaffin yan siyasa da su hakura da sake neman takara a zaben 2027
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
FCT Abuja – Tsohon mai ba wa mataimakin shugaban kasa shawara kan harkokin siyasa, Dr. Hakeem Baba-Ahmed, ya bayyana dalilin da ya sa ya ajiye mukaminsa.
Ya ce ya gano kurakurai da dama da suka bayyana a fili dangane da yadda ake tafiyar da matsalolin da aka gada daga gwamnatin baya da na yanzu

Asali: Twitter
BBC Hausa ta ruwaito cewa Dr. Hakeem Baba-Ahmed ya kara da cewa bai ga wata alama da ke nuna cewa gwamnati na kan hanyar magance matsalolin ba.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
'Na ajiye aiki saboda jama'a,' Hakeem Baba Ahmed
Daily Trust ta ruwaito Hakeem Baba Ahmed ya ce wasu daga cikin jama'a za su rika kallon ya na tare da gwamnati, saboda haka ya na ba da shawarwarin da suka dace.
Ya ce:
''Na tafi ne saboda yadda nake ganin alƙiblar gwamnatin, da kuma yadda aka ajiye ni, ni ban ce ba a yi daidai ba, ko na gaya maku ba ji zaku yi ba, ƙasa kuma na ƙara taɓarɓarewa."
"A waje kuma ana gani na ana cewa ohh, su Dr Hakeem da suna nan da yanzu sun ce kaza."
Tsohon hadimin Kashim ya shawarci Tinubu
Tsohon hadimin Kashim Shettima ya shawarci Shugaba Bola Ahmed Tinubu da ya hakura da batun neman takarar shugaban kasa bayan wa'adi na farko.

Asali: Facebook
Dr. Hakeem Baba Ahmed ya ce:
''Sannan na ce da mun zauna da kai (shugaba Tinubu) da zan ba ka shawara guda ɗaya… idan ka gama wannan shekara huɗu da ƴan Najeriya suka baka, kada ka sake neman shugaban ƙasa."
"Ka ɗauki wasu matakai na gyara Najeriya ba wai bayan ka ba. Kun ci jiya, kun ci shekaran jiya kuma kuna cin yau.''
Ya kara da cewa ba Tinubu kadai ne ya kamata ya hakura da batun takara ba, dukkanin tsofaffin 'yan siyasa ne ya kamata su bar masu tasowa su nemi mukamai.
Hadimin Kashim Shettima ya yi murabus
A baya, mun wallafa cewa Dr. Hakeem Baba-Ahmed, mai ba wa shugaban kasa shawara kan harkokin siyasa, ya yi murabus daga mukaminsa da ke fadar shugaban kasa.
An gano Baba-Ahmed, wanda kuma shi ne tsohon mai magana da yawun kungiyar dattawan Arewa (NEF), ya mika takardar murabus dinsa saboda dalilan kashin kai.
A wani jawabi da ya yi a baya, Baba-Ahmed ya bayyana damuwa kan yadda ake tafiyar da gwamnati, lamarin da bai yi masa dadi ba, yana kuma gudun yadda ake kallon mukaminsa.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng