Abubuwa 4 da Suka Ja Hankali kan Kashim Shettima a Kwanan nan

Abubuwa 4 da Suka Ja Hankali kan Kashim Shettima a Kwanan nan

A ‘yan makonnin da suka gabata, an samu abubuwa da suka kara mayar da hankalin jama'a ga Mataimakin Shugaban ƙasa, Kashim Shettima.

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

FCT Abuja – Mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima na daga cikin shugabannin Najeriya da aka samu karancin cece-kuce a kansu.

Kashim
Abubuwa da dama sun afku, wanda aka dangana da mataimakin shugaban ƙasa a watan Afrilu Hoto: Kashim Shettima
Asali: Facebook

Amma daga farkon watan Afrilu zuwa yanzu, an samu wasu manyan abubuwa da suka shafi Kashim Shettima, wanda suka haɗa da:

1. Yunkurin kutse gidan Kashim Shettima

A safiyar ranar 9 ga Afrilu, 2025, jami’an tsaro a Maiduguri sun dakile yunƙurin wani mutum mai shekaru 35, Musa Ibrahim, na kutse gidan mataimakin shugaban ƙasa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Zagazola Makama ya wallafa a shafinsa na X cewa matashin ya yi kokarin tsallaka wa zuwa gidan Kashim Shettima ta bakin kogin Gadabul.

Sai dai ya gamu da jami'an tsaron da ke kula da gidan, wadanda suka harbe shi a ƙafarsa yayin da yake ƙoƙarin tserewa.

An garzaya da shi asibitin koyarwa na Jami’ar Maiduguri, daga baya kuma aka mika shi ga Sashen binciken manyan laifuffuka domin zurfafa bincike.

2. Abin da Kashim ya fada wa yan siyasar Kano

Voice of Nigeria ta ruwaito cewa a ranar 20 ga Afrilu, 2025, Mataimakin Shugaban ƙasa Kashim Shettima ya ziyarci Kano domin miƙa ta’aziyya ga iyalan marigayi Galadiman Kano, Alhaji Abbas Sanusi.

A zaman karbar gaisuwar tare da Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf da jiga-jigan APC, Kashim ya yi amfani da damar wajen kiran a zauna lafiya.

Kashim
Kashim Shettima yayin ziyarar ta'aziyya a Kano Hoto: Abdullahi Jamilu Sarigirin
Asali: Facebook

Ya ce:

“Don Allah, ina roƙonku da sunan Allah, kada mu bari siyasa ta raba mu. Mu yafewa juna kuma mu duba babbar manufa—Kano tana da matuƙar muhimmanci."

Kashim Shettima ya kara tuna wa masu ruwa da tsakin cewa Kano, “zuciyar Arewa" ce, kuma rigingimu ba za su haifar da 'da mai ido ba.

3. An yi zargin hana Kashim shiga Aso Rock

An samu wasu rahotanni da ke cewa sojoji a fadar shugaban ƙasa da ke Abuja sun hana Mataimakin Shugaban ƙasa shiga fadar.

Tuni dai fadar Shugaban ƙasa ta yi watsi da waɗannan rahotanni da ta bayyana a matsayin kokarin hada rikici da rabuwar kai.

Stanley Nkwocha, Babban mataimaki kan hulda da jama’a ga mataimakin shugaban ƙasa ya ce:

“Wadannan rahotanni na nufin jawo rikici, kuma gaba ɗaya ƙarya ne da ake yada wa don jawo rudani."

4. An mari Tuggar a gaban Kashim Shettima?

Rahotanni a kafafen sada zumunta sun nuna cewa Mataimakin Gwamnan Bauchi, Auwal Jatau, ya mari Ministan harkokin waje, Yusuf Maitama Tuggar.

Sahara reporters ta ruwaito cewa an yi marin ne a gaban Mataimakin shugaban ƙasa, Kashim Shettima yayin da tawagarsu ke hanyar zuwa nadin sarauta.

Rahoton ya ce:

“Lokacin da Tuggar ya mayar da martani cewa ‘jiha ba mallakar mutum ba ce,’ mataimakin gwamnan ya taho daga bayan motar yana barazanar dukan Tuggar, amma tsaron da ke kewaye da Mataimakin Shugaban ƙasa ya hana shi.

Gwamnatin jihar Bauchi dai ta ƙaryata labarin, ta ce ba shi da tushe ko makama, kuma babu hotuna ko bidiyo da suka fito don goyan bayan wannan zargi.

Abin da Kashim ke bukata daga Arewa

A baya, mun wallafa cewa tsohon Sanatan Kaduna ta Tsakiya, Shehu Sani, ya yi kira ga al’ummar Arewa da su ba Mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima, goyon baya.

Ya ce Shettima ne wakilin Arewa lamba ɗaya a matakin tarayya kuma mutum ne jajirtacce, mai kamun kai da ƙaunar yankinsa saboda haka yana bukatar hadin kai.

Tsohon Sanata ya bukaci shugabannin Arewa da daukacin al’umma su mutunta Shettima tare da ba shi goyon bayan da ya dace, saboda muhimmancinsa ga ci gaban yankin.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.