Kamfani Ya Fara Tura 'Kudi' ga Masu Amfani da Layukan MTN a Najeriya, An Ji Dalili
- Kamfanin MTN ya fara rabawa mutane katin waya a layukansu domin biyan diyyar matsalar sabis da aka samu a watan Janairu, 2026
- Hakan ya biyo bayan umarnin da hukumar kula da harkokin sadarwa ta Najeriya (NCC) ta ba kamfanonin saboda rashin karfin sabis
- Wani matashi, Zaharaddeen Hamisu ya nuna damuwarsa kan matsalar sabis, yana mai cewa tana hana matasa samun wata damar
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Abuja, Nigeria - Kamfanin sadarwa na MTN Nigeria ya fara biyan yan Najeriya diyyar matsalar karancin sabis da aka fuskanta a watan Janairun 2026.
Masu amfani da layukan MTN da dama sun tabbatar da cewa sun samu sakon katin waya a wayoyinsu, lamarin da ke nuna kamfanin ya raba wa mutane kudin kira don biyansu diyya.

Source: Facebook
MTN ya fara biyan mutane diyya

Kara karanta wannan
Rashin imani: Bam ya tashi da mutane da yawa, yan ta'adda sun bi su da harbi a Borno
Jaridar Punch ta ruwaito cewa a sakonnin tes da kamfanin ya rika turawa abokan ciniki ta wayoyinsu na hannu, MTN ya ce:
“Ya abokin ciniki, an saka maka N341 a layinka a matsayin diyya kan matsalar sabis da aka samu a watan Janairu 2026. Mun gode da haƙurinka."
Masu amfani da layukan MTN sun tabbatar da cewa kudin da aka tura ya bambanta, ba adadi daya aka tura wa kowa ba.
Wasu mutanen sun ce kamfanin MTN ya tura masu katin N20, wasu N91, yayin da wasu kuma suka samu har N341.
Har yanzu kamfanin bai fito ya tabbatar ba ko an tura wa dukkan abokan ciniki da matsalar ta shafa wannan diyya ba.
Dalilin fara biyan yan Najeriya diyya
Wannan mataki na zuwa ne bayan hukumar sadarwa ta kasa (NCC) ta umarci kamfanonin su magance koke-koken rashin ingancin sadarwa tare da bin ƙa’idojin sabis.
Hakanan an bukaci su rika bai wa abokan cinikinsu diyya idan an samu matsaloli irin haka, kamar yadda The Cable ta ruwaito.

Kara karanta wannan
Sanusi II ya magantu kan yawan cin bashin Gwamnatin Tinubu duk da cire tallafin fetur
Tun da farko MTN ya bayyana cewa za ta bi umarnin hukumomi, tare da ci gaba da zuba jari wajen inganta sadarwa a yankunan kasar nan.
Duk da kokarin MTN, wasu da suka sha fama da matsalar sabis sun ce har yanzu ba a turo masu ko kwandala ba a layukansu.

Source: Getty Images
Matsalar sabis na jawo wa matasa cikas
Zaharadeen Hamisu, wani matashi a Katsina ya shaidawa Legit Hausa cewa har damar raiki ya rasa saboda rashin karfin sabis na MTN.
Ya ce an kira shi daga hukumar kula da kiwon lafiya a matakin farko ta jihar Katsina kan wani aiki da ya cike, amma saboda matsalar sabis bai jin abik da ake fada.
Matashin ya ce:
"Ba su turo mana komai ba, kuma ire-ire na suna da yawa, ni har damar aiki ina tunanin na rasa, an kira ni daga hukumar kula da lafiya amma bana ji saboda rashin sabis.
"Tun lokacin har yanzu ba a kara kira na ba, a yanzu na la dauka na rasa wannan damar, mun rokon mahukunta su gyara mana matsalar sabis don mu samu sadarwa yadda ya kamata.

Kara karanta wannan
Ningi: Babban kuskuren da zai hana wasu sanatoci da 'yan majalisu koma wa kujerunsu a 2027
An rufe shafukan yan Najeriya miliyan 13
A wani labarin, kun ji cewa gwamnatin tarayya ta rufe shafukan 'yan Najeriya miliyan 13,597,057 a dandalin TikTok, Facebook, Instagram da kuma X.
Wannan mataki na gwamnati ya fito ne daga rahoton bin Dokar CoP ta 2024 da masu gudanar da dandalan sadarwa irin su Google, Microsoft, da TikTok suka miƙa wa gwamnati.
Hukumar NITDA ta ce goge shafukan zai ƙara tsaron yanar gizo, kuma za ta ci gaba da wayar da kan masu amfani da soshiyal midiya.
Asali: Legit.ng