NNPP Ta Yi Martani kan Ficewar Sanata Kawu Sumaila zuwa Jam'iyyar APC
- Shugaban jam'iyyar NNPP a jihar Kano, Hashim Dungurawa ya taɓo batun sauya sheƙar Sanata Abdulrahman Kawu Sumaila zuwa APC
- Hashim Dungurawa ya bayyana cewa ba su damu ba ko kaɗan da ficewar da sanatan mai wakiltar Kano ta Kudu a majalisar dattawa ya yi
- Ya bayyana cewa dama tuni sanatan ya zame musu ƙarfen ƙafa kuma sun yi murna da sauya sheƙar da ya yi zuwa jam'iyyar APC
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Kano - Jam'iyyar NNPP reshen jihar Kano ta yi magana kan ficewar Sanata Abdulrahman Kawu Sumaila zuwa APC.
Jam'iyyar NNPP mai alamar littafi ta bayyana sauya sheƙar Kawu Sumaila a matsayin hanya ta samun sauƙi a gare ta.

Asali: Facebook
Shugaban NNPP na jihar Kano, Hashim Sulaiman Dungurawa, ya bayyana hakan yayin da yake magana da manema labarai a Kano, cewar rahoton jaridar Daily Trust.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Martanin na NNPP na zuwa ne ƙasa da sa’o’i 24 bayan Sanata Sumaila ya sanar da sauya shekarsa daga jam'iyyar zuwa APC.
Me NNPP ta ce kan ficewar Kawu Sumaila?
Hashim Dungurawa ya yi watsi da muhimmancin ficewar Kawu Sumaila daga jam’iyyar, yana bayyana shi a matsayin “yaro mai taurin kai” wanda kasancewarsa a NNPP bai kawo wani alheri ba sai rikici da ruɗani.
Hashim Dungurawa ya ƙara da cewa ficewar Kawu Sumaila ba asara ba ce ga NNPP, illa kuwa wata hanya ce da za ta dawo da zaman lafiya da daidaito a cikin jam’iyyar.
“Ba mu yi mamaki ba domin tuni mun daɗe da sa ran hakan zai faru. A matsayinsa na mamba a jam’iyyar, tuni mun dakatar da shi domin ba shi da wani abin kirki da zai kawo. Shi yasa ba shi da wani muhimmanci a wajenmu."
"Jam’iyya za ta samu zaman lafiya yanzu. Ya zama yaro mai taurin kai cikin ƴaƴan jam’iyyar."
"Saboda haka ficewarsa na nufin jam’iyyar za ta iya mayar da hankali kan abin da ya kamata ta yi, saɓanin lokacin da yake addabar ta."
- Hashim Dungurawa

Asali: Facebook
NNPP ba ta tsammanin ficewar wasu daga jam'iyyar
Da aka tambaye shi ko ficewar Kawu Sumaila na iya janyowa sauran fitattun ƴan jam’iyyar su bi sahunsa, kamar tsohon kakakin majalisar dokokin jihar Kano, Kabiru Alhassan Rurum, sai ya kada baki yace:
“A’a, ka da a haɗa wasu da batun nan. Kawu Sumaila kaɗai nake magana a kai. Babu wani da ya ce zai bar jam’iyyar. Haƙiƙa mun dakatar da wasu irinsu Rurum, amma ba su sauya sheƙa ba. Har yanzu suna cikin jam’iyyar."
Dalilin Kawu Sumaila na komawa APC
A wani labarin kuma, kun ji cewa Sanata Abdulrahman Kawu Sumaila ya bayyana dalilinsa na sauya sheƙa daga NNPP zuwa jam'iyyar APC.
Kawu Sumaila ya bayyana cewa ya yi ƙaura daga jam'iyyar NNPP saboda neman mafita ga mutanen da yake wakilta.
Sanatan mai wakiltar Kano ta Kudu ya nuna cewa barinsa NNPP na da nasaba da damar da ya samu ta kawowa al'ummarsa ci gaba.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng