Tsofaffin Ma'aikata Sun Shiga Uku, Gwamnatin Tarayya Za Ta Karbe Masu Gidaje
- Hukumar FGSHLB ta fara tattara jerin sunayen ma'aikatan da suka karbi lamunin gidaje, suka yi ritaya ba su gama biya ba
- Hukumar ta ce za ta dauki matakan shari'a da doka don dawo da kadarorin da aka ba ma'aikatan da basu biya bashin nasu ba
- FGSHLB ta ce tun da farko, an bukaci ma'aikatan da abin ya shafa su gyara matsayin lamunin su kafin su yi ritaya
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
FCT Abuja – Hukumar lamunin gidajen ma'aikatan gwamnati ta tarayya ta fara tattara jerin sunayen ma'aikatan da suka yi ritaya da suka kasa biya cikakken lamunin gidajen da suka samu.
Shugabar sashen sadarwa da hulda da jama'a ta hukumar, Ngozi Obiechina, ta bayyana wannan a wata sanarwa da ta fitar a ranar Alhamis a Abuja.

Asali: Facebook
A cikin sanarwar da aka wallafa a shafin yanar gizon Ma'aikatar Sadarwa, Obiechina ta ce sakatariyar zartarwa hukumar, Hajiya Salamatu Ahmed, ce ta ba da umarnin .
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Za a kwace gidaje daga hannun wasu ma'aikata
Punch News ta wallafa cewa za a kwace kadarorin daga hannun ma'aikatan da suka yi ritaya da suka kasa cika biyan lamunin gidajen da suka karba. Hajiya Salamatu Ahmed ta nuna cewa hakan ya biyo bayan umarnin da sanarwa da aka samu daga Ofishin Shugaban ma'aikatan gwamnatin tarayya.
A cewarta, umarnin ya tunatar da ma'aikatan gwamnati cewa wajibi ne su samu takardar shaida daga FGSHLB da kuma MDA Staff Multipurpose Cooperative Society kafin ritaya.

Asali: Facebook
Hajiya Salamatu ta tabbatar da cewa:
“Hukumar na tattara jerin sunayen irin wadannan ma'aikatan da za a tura su zuwa hukumomi masu alhakin karbar bashi don ci gaba da dawo da kudaden.”
“FGSHLB na ci gaba da tabbatar da bin doka da kuma tabbatar da an bi tsarin dawo da lamuni yadda ya kamata."
Gwamnati za ta buga da tsofaffin ma'aikata
Hajiya Salamatu Ahmed ta ce hukumar za ta dauki matakan shari'a don dawo da kadarorin inda ya dace, bisa ga ka'idojin yarjejeniyar lamuni. Ta ce wannan yana cikin tanade-tanaden Dokar Ayyukan Jama'a ta 021002 (p), wadda Ofishin shugaban ma'aikatan gwamnatin tarayya ya fitar.
Ta ce:
“An umurce ni in sanar da ku game da tanadin Dokar Ayyukan Jama'a (PSR) 021002 (p), wanda ke umartar dukkan ma'aikatan gwamnati su samu Takardar Shaidar Rashin Bashi kafin su yi ritaya."
“Gwamnatin Tarayya za ta fara kwace kadarorin da aka ba ma'aikatan gwamnatin tarayya da suka yi ritaya kuma basu biya lamunin gidajen da suka samu daga hukumar ba."
Gwamnan Kano ya gwangwaje tsofaffin ma'aikata
A baya, mun wallafa cewa hukumar kula da kudin fansho ta Kano ta bayyana cewa ta biya sama da N21bn daga cikin bashin da tsofaffin ma'aikata ke bin gwamnatin jihar.
Shugaban hukumar kula da fansho na jihar, Habu Fagge, ne ya fadi wannan lokacin da yake zantawa da manema labarai a Kano, tare da bayyana yadda ya samu hukumar.
Alhaji Fagge ya bayyana cewa bashin gado ne daga gwamnatocin baya da suka yi mulki a jihar.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng