Sabon Ministan Tinubu Ya Shiga Ofis, Ya Jero Manufofi 5 na Gyara Tattalin Arziki
- Taiwo Oyedele ya kama aiki a hukumance a matsayin Ministan Kuɗi da Tattalin Arziƙi bayan karɓar ragama daga hannun tsohon minista Wale Edun
- Ministan ya bayyana cewa babban burinsa shi ne ganin sauye-sauyen da ake yi sun taba rayuwar talakawa kai tsaye ta hanyar gyara tsarin haraji
- Oyedele ya jaddada cewa ba zai tsaya ga kyawawan manufofi a takarda ba, sai dai zai mayar da hankali ne wajen samar da sakamako na gani da ido
CHECK OUT: How to Start Earning with Copywriting in Just 7 Days – Even if You’re a Complete Beginner
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.
Abuja – Sabon Ministan Kuɗi da Tattalin Arziƙi, Taiwo Oyedele, ya fara aiki gadan-gadan a yau Juma’a, 24 ga watan Afrilu, 2026.
Mista Oyedele ya karɓi ragamar ma'aikatar ne daga hannun Mista Wale Edun, inda ya yaba masa bisa ginshiƙan da ya aza wa tattalin arziƙin ƙasar.

Source: Twitter
Sabon ministar kudi ya kama aiki
Labarin kama aikin Oyedele na kunshe ne a cikin sanarwar da ya wallafa a shafinsa na X, dauke da wani hoto da ke nuna lokacin da shi da Edun suka kammala tsarin mika aiki.
A cikin jawabin da ya yi jim kaɗan bayan kama aiki, Oyedele ya bayyana cewa Najeriya na mataki mai muhimmanci, don haka akwai babban aiki a gabansa.
A cewar sabon ministan, babban aikin da ke gabansa shi ne tabbatar da cewa gyare-gyaren da ake yi kan tattalin arziki sun samar da fa'ida ta zahiri ga ƴan Najeriya.
Manyan manufofin Taiwo Oyedele
Ministan ya bayyana wasu fannoni guda biyar da zai ba su muhimmanci:
- Inganta kasuwanci: Samar da yanayi mai sauƙi ga masu zuba jari ta hanyar tabbatar da cewa dokoki da manufofin gwamnati ba su saba wa juna ba.
- Gyaran tsarin haraji: Sauƙaƙa harkar haraji domin rage wa talakawa da marasa ƙarfi nauyi, tare da faɗaɗa hanyoyin samun kuɗin shiga cikin adalci.
- Adalci wajen kashe kuɗi: Tabbatar da gaskiya da riƙon amana wajen amfani da dukkanin kuɗaɗen shiga na gwamnati.
- Haɗin gwiwar masu zaman kansu (PPPP): Yin aiki tare da kamfanoni da ɓangarorin kasuwanci domin tsara dokoki masu amfani ga tattalin arziƙi.
- Daidaita aikin gwamnati: Tabbatar da cewa dukkan matakan gwamnati suna tafiya akan manufa guda domin samun sakamako mai sauri.

Kara karanta wannan
Gwamna zulum ya fadi manyan dabaru 2 da ke ba ƴan ta'adda damar kai wa sojoji hari

Source: Twitter
Aiki ba surutu ba
Ministan, wanda kwararre ne a fannin haraji da tattalin arziƙi, ya bayyana cewa nasarar ma'aikatar tasa za ta ta'allaka ne akan aiwatar da ayyuka cikin natsuwa.
Ya bayyana cewa ba zai yarda da tsara kyawawan manufofi akan takarda ba tare da an aiwatar da su yadda ya kamata ba.
"Tsara kyakkyawar manufa kaɗai ba za ta isa ba, nasara za ta tabbata ne ta hanyar aiwatarwa. Mun himmatu wajen gudanar da aiki da zai nuna sakamako a zahiri kuma a bayyane." — Taiwo Oyedele
Oyedele ya kammala da cewa yana sa ran yin aiki tare da dukkan ƴan Najeriya da ɓangaren masu zaman kansu domin gina tattalin arziƙi mai ƙarfi da zai samar da wadata ga kowa.
Karanta sanarwar a nan kasa:
An karkatar da kudin FAAC?
A wani labari, mun ruwaito cewa, ma'aikatar kuɗi ta karyata rahotannin da ke cewa ana karkatar da kuɗaɗen shigar gwamnati ko ana kashe kudin a ɓoye.
Cire kuɗaɗe daga asusun FAAC ba ɓata kuɗi ba ne, face biyan buƙatun doka kamar tsaro, da kuma maido wa jihohi haƙƙoƙinsu, cewar Taiwo Oyedele.
Ministan kudin, ya kuma soki yadda wasu ke amfani da tsofaffin bayanai da watsi da sauye-sauyen da aka samu a farkon 2026 don sukar gwamnati.
Asali: Legit.ng

