Wata Sabuwa: Bankin CBN Ya Kara Kudin Mallakar Katin ATM a Najeriya

Wata Sabuwa: Bankin CBN Ya Kara Kudin Mallakar Katin ATM a Najeriya

  • Rahotanni sun nuna cewa babban bankin Najeriya na CBN ya kara kudin mallakar da katin ATM da kashi 50 cikin 100, inda ya dawo N1,500
  • Bayan haka, an ruwaito cewa bankin ya sanar da soke kudin kula da katin ATM da 'yan Najeriya ke biya a kowane wata a fadin kasar nan
  • Biyo bayan lamarin, Legit Hausa ta tattaro karin bayani game da sauye-sauyen da aka yi da yadda sababbin dokokin za su shafi al'ummar Najeriya

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja - Babban Bankin Najeriya (CBN) ya kawo sauye-sauye, inda ya kara kudin mallakar katin ATM daga N1,000 zuwa N1,500.

Bugu da kari, bankin ya bayyana cewa ya soke tsarin karbar kudin kula da katin ATM na wata-wata da ake cire N50 daga asusun abokan hulda.

Kara karanta wannan

An cafke sojan Amurka da ya je kama shugaban kasar Venezuela

Mutane na cire kudi a ATM
Yadda wasu 'yan Najeriya ke cire kudi a ATM. Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Vanguard ta wallafa cewa CBN ya jaddada cewa sabon tsarin zai sauya yadda ake cire kudin mu’amala da POS, inda aka daura nauyin kudin kan ‘yan kasuwa.

Bankin CBN ya kara kudin katin ATM

A karkashin sabon tsarin, duk wanda zai mallaki sabon katin ATM ko maye gurbin tsoho zai biya N1,500 maimakon N1,000 da ake biya a baya.

Hakan ya nuna cewa CBN ya kara kudin da kashi 50 cikin 100 duk da yadda 'yan Najeriya ke kuka kan tsadar rayuwa da wahalar tattalin arziki.

Sai dai bankin ya ce akwai tsarin da za a bar abokin mu'amala da yarjejeniya da ya yi tsakanisa da bankinsa. Haka kuma, katunan da ake amfani da su ta yanar gizo za su kasance kyauta.

Kudi na fita a ATM
Yadda wani ke cire kudi a katin ATM. Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Game da katunan ATM na kudin waje kuwa, CBN ya bayyana cewa za a ci gaba da karbar $10 a shekara a matsayin kudin kula da su.

Kara karanta wannan

Atiku ya tono 'babbar matsala' kan kada kuri'a a 2027, ya ce za a yi magudi

Sauyin zai shafi masu POS

Sabon tsarin ya tanadi cewa ba za a cire ko sisi a asusun kwastoma ba a duk wata mu’amala da aka yi da katin ATM a wajen yan kasuwa

Maimakon haka, bankin ya ce 'yan kasuwa ne za su rika biyan kudin hidimar da aka yi da ake kira MSC a tsarin bankuna a Najeriya.

An kayyade kudin da za a rika cirewa da kaso 0.5 cikin 100 na kowace mu’amala kuma zai kasance na bai daya ba tare da la’akari da irin hanyar biyan kudin da aka yi amfani da ita ba.

CBN ya ce matakin na nufin rage wa abokan mu'amala wahalar biyan karin kudi yayin mu’amala, tare da karfafa amfani da hanyoyin biyan kudi na zamani.

CBN ya kawo sababbin dokokin BVN

A wani labarin, kun ji cewa Babban bankin Najeriya (CBN) ya kawo wasu sababbin dokokin da suka shafi lambar banki ta BVN.

Kara karanta wannan

Alhakin Falasdinawa: Za a cafke Benjamin Netanyahu a kasar Hungary

A karkashin dokokin da aka kawo, masu mu'amala da banki za su iya sauya lambar wayar da suka hada da BVN sau daya ne kacal.

CBN ya sanar da cewa ya kawo dokokin ne domin kara tsaro a asusun bankuna kuma za su fara aiki daga ranar 1 ga watan Mayu, 2026.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng