Rahoton Bankin Duniya Ya Nuna yadda 'Yan Najeriya za Su Kara Talaucewa a 2027
- Bankin Duniya ya bayyana cewa yawan talauci a Najeriya zai karu da 3.6% kafin shekarar 2027 da ake sa ran za a yi zabe
- Rahoton ya danganta hakan da dogaro da danyen mai, raunin tattalin arziki da kuma kalubalen shugabanci a ƙasar
- Bankin duniya ya ce Najeriya na daga cikin ƙasashe huɗu da ke dauke da mafi yawan matsanancin talakawa a Afirka
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja - Bankin Duniya ya fitar da wani rahoto a taron bazara da ya gudanar tare da IMF a birnin Washington DC, wanda ke nuna yadda matsanancin talauci ke ƙara yawa a Najeriya.
Rahoton mai suna Africa’s Pulse ya nuna cewa yawan talakawan Najeriya zai karu da 3.6% daga shekar ta 2022 zuwa 2027 saboda matsalolin tattalin arziki da tsarin mulki.

Asali: Twitter
A cewar Bankin, dogaron da Najeriya ke yi ga arzikin mai da raunin bangaren kudi da shugabanci na cikin dalilan da ke hana raguwar talauci a kasar.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Bankin duniya: 'Ana fama da talauci a Najeriya'
Punch ta wallafa cewa rahoton ya ce Najeriya da Jamhuriyar Dimokuraɗiyyar Kongo (DRC) na daga cikin ƙasashen da talauci zai fi karuwa a cikinsu.
A cewar rahoton:
“Najeriya da wasu ƙasashe na da arzikin ma’adinai amma saboda raunin tsarin shugabanci za su fuskanci karuwar talauci daga 2022 zuwa 2027,”
Duk da haka, bangaren tattalin arzikin da ba na man fetur ba ya nuna an samu ci gaba a karshen shekarar 2024.
Bankin Duniya ya yi gargadin cewa hakan ba zai rage yawan talauci ba saboda manyan kalubale na tsare tsare da kudi.
Afirka na da mafi yawan talakawa a duniya
Bankin Duniya ya bayyana cewa nahiyar Afirka na dauke da 80% na wadanda talauci ya yi wa katutu.
A cikin 80% na talakawan, kusan rabinsu (Kimanin mutane miliyan 280) na zaune ne a ƙasashe huɗu, ciki har da Najeriya.
A gefe guda, yankin Asiya ta Kudu na da 8%, Gabashin Asiya da Tekun Pasifik na da 2%, Gabas ta Tsakiya da Afirka ta Arewa na da 5%, yayin da Latin Amurka da Caribbean ke da 3%.
Bankin duniya ya ba da shawari
Rahoton ya nuna cewa ƙasashen da ba su dogara da ma’adinai ba suna samun ci gaba a tattalin arziki saboda kyakkyawan tsari.
Don haka, Bankin Duniya ya shawarci Najeriya da ta mayar da hankali wajen gyara tsarin kudi da inganta shugabanci domin rage talauci a gaba.
Ta kuma bukaci gwamnatoci su gyara alakarsu da 'yan kasa musamman a kan harkokin tsare tsaren kudi domin samun goyon baya wajen yaki da talauci.

Asali: Facebook
Dr Hakeem ya caccaki tsare tsaren Tinubu
A wani rahoton, kun ji cewa tsohon mashawarci a fadar shugaban kasa, Hakeem Baba Ahmed ya bukaci Bola Tinubu ya hakura da takara a 2027.
Dr. Hakeem Baba Ahmed ya ce tsare tsaren Tinubu sun jefa al'umma cikin talauci kuma gwamnatin shi na nuna wariya.
Baya ga haka, ya ce idan Bola Tinubu ya hakura da takara zai kafa tarihi mai kyau da za a tuna da shi a Najeriya a shekaru masu zuwa.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng