Za a Daura Auren Rarara da Aisha Humaira bayan Sun Dade Suna Aiki Tare
- Shahararren mawakin siyasa, Dauda Kahutu Rarara, na shirin ɗaura aure da fitacciyar jaruma kuma 'yar amshi, Aisha Humaira
- Wani aminin Rarara ya bayyana cewa za a ɗaura auren ranar Juma’a 25 ga watan Afrilu 2025, a Maiduguri, jihar Borno, bayan sallah
- Dangantakar shi da Aisha ta samo asali ne tun shekaru da dama da suka yi tare a harkar waka, a yanzu dangantakar za ta kai ga aure
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
JIhar Borno - Daga cikin labarai da ke tashe a fagen nishadi da siyasa, akwai batun shirin ɗaura auren Dauda Kahutu Rarara da Aisha Humaira, wadda ta shahara a Kannywood.
Rarara wanda ya shahara wajen rera wa shugabannin siyasa wakokin yabo, musamman a lokacin zaɓe, ya shafe shekaru yana aiki kafada da kafada da Aisha Humaira.

Asali: Facebook
Jaridar Leadership ta wallafa cewa za a daura auren ne a Maiduguri, babban birnin jihar Borno a yau Juma'a.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Wani makusancin Rarara da ya nemi a ɓoye sunansa ya tabbatar wa Kano Times cewa an kammala shiri tsaf domin ɗaura auren a Maiduguri bayan sallar Juma’a.
Yadda za a yi bikin Rarara da Humaira
Majiyar ta ce ba za a yi shagulgula ba a lokacin bikin saboda wasu dalilai, amma bikin yana da matuƙar muhimmanci ga ɓangarorin biyu da kuma masoyansu.
Majiyar ta ce:
“Komai ya kammala. Za a ɗaura auren ne a Maiduguri bayan sallar Juma’a. Ba za a yi wani biki mai girma ba, amma za a yi shi cikin natsuwa da kulawa,”
Aisha Humaira dai ta yi fice a fina-finan Hausa da kuma wakokin siyasa, inda ta kasance muryar amshi a yawancin wakokin Rarara na baya-bayan nan.
Alakar Rarara da Humaira tsawon shekaru
Bincike daga wakilan Legit.ng Hausa ya nuna cewa dangantakar Rarara da Aisha ba sabuwa ba ce, domin sun dade suna aiki tare tun kafin lamarin ya juya zuwa soyayya.
Wani aboki na kusa da su ya ce:
“Duk wanda ya san su, ba zai yi mamakin wannan aure ba. Tun da dadewa akwai alaka ta musamman tsakanin su fiye da aiki kawai.”
Ya kara da cewa, tun lokacin da suka fara haɗin gwiwa a fagen waka, akwai girmamawa da fahimta tsakanin su wanda ya ƙara ƙarfafa dangantakarsu.
Masu fashin bakin masana nishadi sun bayyana wannan auren a matsayin wata gagarumar alama ta haɗin kai tsakanin mawaka da 'yan fim a Arewacin Najeriya.

Asali: Instagram
A kwanakin baya ma an fara rade radin daura auren amma Aisha Humaira ta karyata zancen a wani sako da ta fitar.
Da wakalin; goro a miya
Dangantakar mawaki Dauda Kahutu Rarara da Aisha Humaira ta jima tana janyo ce-ce-ku-ce a tsakanin jama’a, musamman a shafukan sada zumunta da fagen nishadi.
Aisha, wadda ta shahara a harkar fina-finan Hausa da kuma matsayin 'yar amshi a wakokin siyasa, ta kasance tare da Rarara a kusan duk wakokinsa na 'yan shekarun bayan nan.
A wasu lokuta, masoya da mabiyan wakokin Rarara sun fara nuna zargin cewa akwai soyayya a tsakanin su, musamman ganin yadda suke yawan bayyana tare a wasu bidiyo da kuma irin yadda suke da fahimtar juna sosai a tsakaninsu.
Duk da cewa a baya Aisha ta karyata jita-jitar cewa suna shirin aure, yanzu da labarin daurin auren ya tabbata, hakan ya tabbatar da abin da mutane da dama ke hasashe tun da dadewa.
Auren Rarara da Aisha na nuna yadda hulɗar aiki a masana’antar nishadi ke iya juyewa zuwa soyayya ta gaske, kuma ya kara jan hankali kan yadda mawaka da 'yan fim ke karfafa juna da kulla zamantakewa mai karfi.
Rahama Sadau ta tabo maganar aure
A wani rahoton, kun ji cewa fitacciyar jarumar Kannywodd, Rahama Sadau ta fara magana kan yin aure ta na mai shekaru 31.
Rahama Sadau ta yi magana ne bayan an yi wani gagarumin biki a lokacin auren wani mawaki da aka fi sani da Juma Jux da amaryarsa.
Jarumar ta ce bikin ya kayatar matuka, musamman shigan da kawayen amarya suka yi, kuma tana fatan a yi irin shi a lokacin aurenta.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng