Dubban Masu Zanga Zanga Sun Kewaye Ofishin Wike a Abuja kan Karin Albashi
- Malaman makaranta da ma’aikatan lafiya sun gudanar da zanga-zanga a Abuja domin nuna fushinsu kan kin biyan sabon albashi na N70,000
- Sun ce duk da an sako biliyoyin Naira daga ofishin Nyesom Wike domin biyan hakkokinsu, shugabannin kananan hukumomi sun ki biyansu
- Ministan Abuja, Nyesom Wike, ya bayyana fushin yadda shugabannin kananan hukumomi suka ki aiwatar da albashin duk da an ba su kudin
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja - Dubban malaman makaranta da ma’aikatan lafiya a babban birnin tarayya Abuja sun mamaye ofishin Ministan Abuja, Nyesom Wike, suna zanga-zanga kan rashin biyan albashi.
Zanga-zangar dai ta shafi malamai, ma’aikatan kananan hukumomi da ma'aikatan lafiya daga hukumomin yankin guda shida da ke Abuja.

Asali: Facebook
Daily Trust ta wallafa cewa zanga-zangar ta biyo bayan kin biyan sabon albashi na N70,000 da kuma wasu hakkoki duk da cewa gwamnati ta saki N4.1bn domin biyan hakkokin.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Zanga zanga a ofishin Wike da wurare
Masu zanga-zangar sun fara haduwa ne a gaban Labour House da misalin karfe 11:00 na safe, dauke da kwalaye masu rubuce-rubuce na korafi kafin su nufi sakatariyar FCTA a Area 11.
Shugaban kungiyar malaman makaranta ta Abuja, Kwamred Abdullahi Mohammed Shafas, ya ce sun fito domin nuna rashin jin dadinsu kan yadda aka ki biyan sabon albashi da sauran hakkoki.
Sahara Reporters ta wallafa cewa Shafas ya ce duk da cewa Wike ya saki N4.1bn domin biyan hakkokin, shugabannin kananan hukumomin sun ce kudin na ayyuka ne, ba albashi ba.
An rufe asibitoci a kananan hukumomin Abuja
Shugaban kungiyar ma’aikatan jinya da ungozoma ta Abuja, Kwamred Jamadi Medan, ya ce sun rufe dukkan cibiyoyin lafiya tun sama da wata guda da ya gabata saboda yajin aiki.
Ya ce wannan matsalar na kara haifar da mutuwar mata masu juna biyu da kananan yara sakamakon rashin magunguna da kulawa.
A cewarsa, akwai kimanin cibiyoyin lafiya 202 a Abuja, amma ungozoma kasa da 103 ke aiki a cikinsu – lamarin da ke kara tabarbarewar harkar lafiya.
Martanin Nyesom Wike kan zanga zangar
Ministan Abuja, Nyesom Wike, ya bayyana takaicinsa kan yadda shugabannin kananan hukumomi suka ki biyan hakkokin malaman makaranta da ma’aikatan lafiya.
A wata hira da manema labarai bayan duba ayyuka a birnin, Wike ya ce ya saki kudin ne domin a biya albashi, amma an ki biyan ma'aikatan.
Ya ce wannan rashin adalci ne ga malamai da ma’aikata, kuma dole ne a dauki mataki domin kare rayuwar al’umma da makomar yara.

Asali: Facebook
Tinubu zai gana da Wike da Fubara
A wani rahoton, kun ji cewa ana sa ran shugaba Bola Ahmed Tinubu zai gana da Nyesom Wike, Simi Fubara da wasu manyan Rivers.
Ana rade radin cewa hakan na cikin shirye shiryen samar da daidaito a jihar kafin mayar da gwamna Fubara ofis.
Hakan na zuwa ne bayan wata ganawa da aka yi tsakanin Fubara da Bola Tinubu a London kan lamuran siyasar jihar Rivers.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng