Nasarawa: 'Yan Bindiga Sun Kashe Ango, Sun Sace Amaryarsa Kwanaki 13 da Aurensu

Nasarawa: 'Yan Bindiga Sun Kashe Ango, Sun Sace Amaryarsa Kwanaki 13 da Aurensu

  • Wasu 'yan bindiga da ake zargin makiyaya ne sun kashe wani sabon ango tare da sace amaryarsa a kauyen Akaleku, jihar Nasarawa
  • Rahotanni sun bayyana cewa kwanaki 13 da suka wuce ne aka daura auren ango da amaryar, kuma suna cin amarci aka farmake su
  • A jihar Edo kuwa, ‘yan bindiga sun kashe wani magidanci tare da sace matarsa mai juna biyu, da ‘yar uwarta, a gaban ‘ya’yansa uku

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Nasarawa - Wasu 'yan bindiga da ake zargin makiyaya ne sun tafka babbar ta'a a wani sabon hari da suka kai jihar Nasarawa.

An ce 'yan ta'addar sun harbe wani sabon ango har lahira, sannan suka sace amaryarsa a wani kauye da ke Nasarawa, a daren ranar Laraba.

Ana fargabar 'yan bindiga su kashe wani ango tare da sace amaryarsa a jihar Nasarawa
Jami'an rundunar 'yan sandan Najeriya a bakin aiki. Hoto: @PoliceNG
Asali: Twitter

'Yan bindiga sun kashe ango a Nasarawa

Wani ganau ya shaida wa jaridar Vanguard cewa 'yan bindigar sun kai farmaki gidan sababbin ma'auratan da misalin karfe 11 na dare.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Majiyar ta ce sun harbe mijin sannan suka yi awon gaba da matarsa, lamarin da ya jefa al'ummar kauyen Akaleku cikin tashin hankali.

An ce ma'auratan na zaune a a kauyen Akaleku da ke karamar hukumar Obi, wadda ke a kan hanyar garin Lafia zuwa Makurdi.

'Yan bindiga sun yi awon gaba da amaryar

Rahoton ya nuna cewa an daura auren Mr Alu Anzaku da matarsa a ne a ranar 12 ga Afrilu, kasa da makonni biyu da suka gabata.

Ana zargin suna cikin hutun amarcinsu ne a lokacin da 'yan bindigar suka farmake su, suka kashe hanzarin angon da kuma sace amaryar.

Yayin da ake fitar da wannan rahoto, iyalai da makwabta sun bayyana damuwa sakamakon rashin ji daga 'yan bindigar game da matar da suka sace.

'Yan bindiga sun kashe magidanci a Edo

A wani lamari makamancin wannan, ‘yan sanda a jihar Edo ta tabbatar da cewa 'yan bindiga sun kashe wani Friday Pius tare da sace matarsa mai juna biyu da ‘yar uwarta.

Rundunar ta shaida cewa lamarin ya faru ne a garin Uluoke da ke Uzairue, karamar hukumar Etsako ta Yamma, a jihar Edo.

Mai magana da yawun rundunar, Moses Yamu, ya ce jami’an tsaro sun isa yankin da lamarin ya faru domin daukar mataki.

A cewarsa, jami’an ‘yan sanda suna aiki tare da 'yan sa kai da maharba wajen ceto wadanda aka sace da kama masu laifin.

Rundunar 'yan sanda ta yi magana da 'yan bindiga suka kashe magidanci a Edo
Shugaban rundunar 'yan sandan Najeriya, Kayode Egbetokun. Hoto: @PoliceNG
Asali: Twitter

'Yan bindigar sun sace mata da yar uwarta

Jaridar Premium Times ta ruwaito cewa lamarin ya faru da asuba, tsakanin karfe 1 zuwa 2 na safiyar ranar Litinin din da ta gabata.

Shaidu sun bayyana cewa ‘yan bindigar sun harbe Pius har lahira sannan suka sace matarsa da ‘yar uwarta, suka bar ‘ya’yansa uku suna kuka kusa da gawarsa.

Mazauna yankin sun ce sun ji harbe-harbe amma sun gaga fitowa saboda fargaba har sai da maharan suka bar yankin.

'Yan bindiga sun kashe sabon ango a Neja

A wani labarin, mun ruwaito cewa, wasu ‘yan bindiga sun kashe wani sabon ango a wani mummunan hari da suka kai kauyen Madaka da ke jihar Neja.

Lamarin ya faru ne kwanaki uku bayan daura masa aure, lokacin da ya je kasuwa domin gudanar da sana'ar sayar da nama kamar yadda ya saba.

Majiyoyi sun ce maharan sun harbi wasu ƙananan yara tare da tilasta wa mata karya azuminsu, in ba haka ba za su kashe su nan take.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.