An Fadi Yawan Albashin Tinubu, Kashim, Gwamnoni da Sauran Masu Mukaman Siyasa

An Fadi Yawan Albashin Tinubu, Kashim, Gwamnoni da Sauran Masu Mukaman Siyasa

  • Shugaban hukumar tattara kudin shiga da raba su, RMAFC, Muhammed Shehu ya ce albashin shugabanni ba ya da yawa kamar yadda ake tunani ba
  • Shehu ya bayyana cewa shugaban kasa na karbar kasa da N1.5m a wata, yayin da wasu ma’aikatan CBN ke karbar kudi fiye da ministocin tarayya
  • Rahotanni sun bayyana yadda albashin ministoci da hadimai ke da yawan kudi kuma hakan na iya gyara wasu bangarori idan an sake zuba su

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

FCT, Abuja - A cikin wata hira, shugaban hukumar tattara kudin shiga da raba su, RMAFC, Muhammed Shehu, ya yi magana kan albashin shugaban kasa, ministoci da yan majalisa.

Shehu ya ce ba gaskiya ba ne cewa shugabannin siyasa na karbar albashi mai yawa idan aka kwatanta da sauran ma'aikata.

Yawan albashin Tinubu, Kashim da gwamnoni
Hukumar RMAFC ta fadi albashin Tinubu da sauran ƴan siyasa. Hoto: @officialABAT.
Asali: Twitter

Yadda ma'aikacin CBN ya fi minista albashi

Shehu ya ce tun daga shekarar 2008 ba a kara albashin shugabannin siyasa ba, ma’aikata da dama na karbar kudi fiye da ministoci da 'yan majalisa, cewar rahoton ICIR.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya ce:

"Tun 2008 har yau, ba a sabunta albashi ba, Shugaban kasa na karbar kasa da N1.5m, minista ma ba ya kai miliyan daya."
"Na san wani ma’aikacin CBN da ba darakta ba, amma albashinsa ya fi na minista."
Hukuma ya yi magana kan albashin Tinubu da mukarraban gwamnati
Hukumar RMAFC ta fadi yawan albashin da Tinubu, Kashim da sauran yan siyasa ke dauka. Hoto: Asiwaju Bola Tinubu.
Asali: Facebook

Yadda albashi ke cinye kudin Najeriya

A cikin shekaru, an sha samun cece-kuce kan albashin masu rike da mukaman siyasa tare da kiran a rage kashe kudi a gwamnati.

A kasafin 2023, an ware N2.9tn domin albashi, wanda shi ne na biyu mafi yawan kudi a kashe-kashen da aka yi.

An ruwaito albashin sanata, minista da hadimai, inda suka nuna cewa idan za a yi amfani da su a kasa da kyau zai taimaka matuka wurin kawo ci gaba.

Hakanan an fadi yadda ministocin Tinubu 46 za su ci N29.91m a kowane wata domin albashinsu na asali.

A cewar RMAFC, ga albashin shugabanni a wata, amma ba ya hade da alawus da rance da ke zuwa da mukamansu.

Yawan albashin masu mukaman siyasa a Najeriya

1. Shugaban kasa - N1,171,568

2. Mataimakin shugaban kasa - N1,010,524

3. Minista/Sakataren gwamnati - N650,137

4. Karamin minista - N628,057

5. Hadiman shugaban kasa - N590,958

6. Shugaban majalisar dattawa - N724,571

7. Mataimakin shugaban majalisar dattawa - N673,507

8. Sanatoci - N1,063,860

9. Shugaban majalisar wakilai - N412,852

10. Mataimakin shugaban majalisar wakilai - N381,172

11. Yan majalisar wakilai - N794,087

12. Gwamnoni - N648,581

13. Mataimakan gwamnoni - N616,063

Wadannan alawus sun hada da masauki, kayan daki, tafiya, lafiya, kudin sallama, hutu da kuma rancen motoci.

Hakanan, kamar yadda tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari ya yi, minista na da damar karbar kudi don tafiyar aiki.

Yaya albashi yake a fannin ma'aikatan gwamnati?

A Najeriya, yawancin ma’aikata na fama da karancin albashi wanda ba ya wadatar su don biyan bukatun yau da kullum.

Duk da cewa akwai cece-kuce kan yawan albashin ‘yan siyasa, hakikanin gaskiya ita ce mafi yawan ma’aikatan gwamnati na karbar albashi kadan sosai idan aka kwatanta da tsadar rayuwa.

A kasafin kudin 2023, an ware N2.9 tiriliyan domin biyan albashi, amma rahotanni sun nuna cewa wannan kaso yawanci yana zuwa ne ga manyan mukarraban gwamnati da alawus masu yawa.

Ma’aikaci mai matsakaicin matsayi a Najeriya na karbar albashi tsakanin N30,000 zuwa N70,000 a wata, wanda ba zai iya daukar nauyin abinci, haya, wutar lantarki da kula da iyali ba.

A gefe guda kuwa, shugabanni irin su ministoci da sanatoci na samun albashi da alawus da ke kai fiye da miliyan daya a wata. Wannan babbar gibin albashi ya janyo cece-kuce, inda jama’a ke ganin tsarin bai da adalci.

Duk da cewa shugaban hukumar RMAFC ya ce wasu ma’aikatan banki na karbar fiye da ministoci, yawancin ma’aikata a kasa ne ke fuskantar matsanancin hali, inda albashinsu ba ya kai su ƙarshen wata.

Obasanjo ya koka kan mafi ƙarancin albashi

Mun ba ku labarin cewa tsohon Shugaban Kasa, Olusegun Obasanjo ya ce sabon mafi karancin albashi ba zai isa biyan bukatun ma’aikata ba.

Obasanjo ya zargi shugabannin kungiyoyin kwadago da fifita bukatun kansu fiye da muradun ma’aikata.

Ya zargi cewa tun daga 2015 ake rufe wa shugabannin kwadago baki da kudi masu yawa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.