Al’umma Sun Samu Saukin Hare Hare, Hatsabibin Dan Ta’addan ISWAP Ya Bakunci Lahira

Al’umma Sun Samu Saukin Hare Hare, Hatsabibin Dan Ta’addan ISWAP Ya Bakunci Lahira

  • Dakarun Operation HADIN KAI sun samu nasarar rage mugun iri a yakin da suke ci gaba da yi da ta'addanci a Arewa
  • Rundunar ta yi nasarar kashe wani babban jigo a majalisar Shura ta ISWAP a wani samame da suka kai a yankin Yobe
  • Rahotannin tsaro sun ce an tabbatar da kashe shi da misalin karfe 6:12 na yamma ranar 22 ga Afrilun 2026 bayan samun sahihan bayanan sirri

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Damaturu, Yobe - Rundunar sojojin Najeriya na ci gaba da samun galaba kan yan ta'adda a Arewacin kasar wanda ya yi katutu.

Dakarun Operation HADIN KAI sun hallaka wani fitaccen dan majalisar Shura ta kungiyar ISWAP, Abu Jirir a yayin wani samame da suka kai a jihar Yobe cikin nasara.

An hallakakwamandan ISWAP
Ministan tsaro, Christopher Musa da kwamandan ISWAP da aka kashe, Abu Jirir. Hoto: General GC Musa, @zagazOlamakama.
Source: Twitter

Majiyoyin tsaro daga Zagazola Makama sun bayyana cewa an tabbatar da wannan lamari da misalin karfe 6:12 na yamma ranar 22 ga Afrilun shekarar 2026.

Kara karanta wannan

Za a gurfanar da sojoji 36 da ake zargi da yunkurin yi wa Tinubu juyin mulki gaban kotu

Yadda sojoji ke arangama da mayakan ISWAP

Wannan kyakkyawan labari na zuwa ne yayin da ake ci gaba da kai ruwa rana tsakanin dakarun sojoji da kuma mayakan kungiyar ISWAP.

Ko a watan Faburairun 2026 ma, ‘yan ta’addan kungiyar ISWAP sun kai wani mummunan hari a kan sansanin sojoji da ke jihar Borno inda suka yi barna mai yawan gaske.

Rahotannin da aka samu zuwa yanzu sun tabbatar da cewa sojoji takwas sun mutu, 23 sun jikkata a harin da ya gigita na kusa da yankin.

Maharan, wadanda suka yi jeron gwano a kan babura akalla 70, sun kurda ta hanyoyi daba-daban kafin su isa sansanin da aka kai wa hari.

Babban jigo a kungiyar ISWAP ya bakunci lahira
Taswirar jihar Yobe da mayakan Boko Haram da ISWAP ke kai hare-hare. Hoto: Legit.
Source: Original

Yadda sojoji suka yi nasarar kashe kwamandan ISWAP

An tabbatar da cewa dakarun sojojin sun samu nasara ne bayan samun bayanan sirri kan dan ta’addan.

An gano cewa babban dan ta’addan mai suna Abu Jarir ya gamu da ajalinsa ne a hannun dakarun soji a yankin Babangida bayan artabun da aka yi.

Kara karanta wannan

Ba sauki: Sojoji sun kashe babban kwamandan ISWAP da 'yan ta'adda da dama

A cewar majiyoyin, wannan kisa ana kallonta a matsayin babbar illa ga tsarin shugabancin kungiyar ISWAP a yankin Tafkin Chadi baki daya.

Majiyoyin sun kuma kara da cewa babban kwamandan ISWAP a yankin Tafkin Chadi, wanda ake kira Ba Shuwa, ya tura wata tawaga domin dauko gawar mamacin.

An ce an hango tawagar binciken suna tafiya da babura kusan 12 a yankin Aljanna Jaule a wannan rana domin gudanar da aikin nasu.

Ana sa ran karin bayani kan wannan samame yayin da jami’an tsaro ke ci gaba da tattara bayanai da kuma zurfafa bincike kan lamarin.

ISWAP ta sanar da mutuwar kwamandanta

A baya, mun ba ku labarin cewa kungiyar ISWAP ta sanar da mutuwar babban kwamandanta wanda ke cikin majalisar 'Shura' na kungiyar wanda yake da tasiri.

ISWAP ta tabbatar da mutuwar Abu Yahya Al-Muhajir, tana mai bayyana hakan a matsayin babbar asara wanda ba za ta taba mantawa da ita ba.

Rahotanni sun nuna cewa an kashe ‘yan ta’adda da dama yayin harin Malam Fatori da sojoji suka dakile wanda ya ba su damar samun nasara.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.