Shugaba Trump Ya Kuma Sako Magana, Kasar Iran Ta Gabatar da Sabon 'Tayi' ga Amurka

Shugaba Trump Ya Kuma Sako Magana, Kasar Iran Ta Gabatar da Sabon 'Tayi' ga Amurka

  • Shugaban Amurka, Donald Trump ya bayyana cewa kasar Musulunci ta Iran ta gabatar da tayi da nufin cika sharuddan da ya shimfida
  • Duk da bai yi cilakken bayani kan tayin na Iran ba, Trump ya ce Amurka za ta yi nazari kafin ta dauki mataki na gaba
  • Ana sa ran tawagar Amurka za ta isa birnin Islamabad a gobe Asabar bayan ministan harkokin wajen Iran, Abbas Araghchi ya kai ziyara Pakistan

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

United states - Shugaban kasar Amurka, Donald Trump ya yi ikirarin cewa Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta gabatar da sabon tayi domin ci gaba da tattaunawar sulhu.

Wannan kalamai na Trump na zuwa bayan kasar Iran ta kafa sharadin cewa ba za ta koma zagaye na biyu na tattaunawa da Amurka ba har sai an bude tashoshin ruwanta.

Kara karanta wannan

Ana tsaka da maganar sulhu, Trump ya yi barazana mai ɗaga hankali ga Iran

Trump.
Shugaban Amurka, Donald Trump ya fito hira da yan jarida a birnin Washington DC Hoto: Alexander Harnik
Source: Getty Images

Wane irin tayi Iran ta gabatar?

Amma a wata hira da kamfanin dillancin labarai na Reuters, Trump ya yi ikirarin cewa Iran na bukatar a ci gaba da tattaunawa, kuma ta turo da sabon tayi.

“Sun gabatar da wani tayi, za mu gani yadda abin zai kasance,” in ji shi.

Sai dai shugaban na Amurka bai fayyace wane bangare daga cikin jami’an gwamnatin Iran yake tattaunawa da su kan wannan lamari ba.

“Ba na son in bayyana, amma muna hulɗa da mutanen da ke da iko a kasar Iran a yanzu,” in jj Trump.

Zuwa Islamabad domin tattaunawa

Rahotanni sun nuna cewa Ministan harkokin wajen Iran, Abbas Araghchi, ya isa birnin Islamabad na kasar Pakistan.

Haka kuma ana sa ran wata tawagar Amurka karkashin jagorancin Witkoff da Kushner za su tafi birnin a gobe Asabar, sai dai har yanzu Iran ba ta tabbatar da ko Araghchi zai gana da su ba.

Kara karanta wannan

Rasha ta yi tone tone, an ji yadda kasar Musulunci ta Iran ta fada tarkon Amurka

Mai magana da yawun Fadar White House, Karoline Leavitt, ta ce an samu wasu ci gaba a baya-bayan nan a tattaunawar da Amurka ke yi da Iran ta hanyar tura sakonni.

Halin da ake ciki tsakanin Iran da Amurka

Ta bayyana cewa tattaunawar yanzu na kan matakin bincike, ba irin cikakkiyar tattaunawar da aka yi a baya ba ce, kamar yadda NBC News ta kawo.

Islamabad
Wurin da aka yi tattaunawar farko tsakanin Amurka da Iran a birnin Islamabad Hoto: Pool
Source: Getty Images

Ta ce a wannan karon, wakilan Amurka na musamman za su jagorantar tattaunawar, ba tare da mataimakin shugaban kasa, JD Vance ba.

Leavitt ta ce Vance da sakataren harkokin wajen Amurka Marco Rubio za su ci gaba da sa ido daga Washington, amma za su iya zuwa Islamabad idan tattaunawar ta kai wani muhimmin matsayi.

Trump ya sallami shugaban sojin ruwa

A wani rahoton, kun ji cewa gwamnatin Donald Trump ta sauke shugaban rundunar sojin ruwan Amurka, John Phelan yayin da ake cigaba da takaddama da Iran.

Ba a bayyana dalilai karara kan sanadin sauke shi ba, sai dai an haska cewa kasar na bukatar sabon hannu a rundunar sojin ruwa a halin yanzu.

Mai magana da yawun Pentagon, Sean Parnell, ya bayyana cewa Phelan zai bar mukaminsa “nan take,” wani mataki da ya zo ba zato ba tsammani.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262