Siyasar 2027: Sufeton 'Yan Sanda a Mulkin Buhari zai Yi Takarar Gwamna a APC
- Tsohon Sufeto Janar na ‘Yan Sanda, Mohammed Adamu, ya bayyana aniyarsa ta tsayawa takarar gwamna a jihar Nasarawa a zaben 2027
- Mohammed Adamu ya bayyana hakan ne a wani taro da ya gudanar da shugabannin jam’iyyar APC a jihar Nasarawa a birnin Lafia
- Tsohon shugaban 'yan sandan ya ce jama’a ne suka bukaci ya tsaya takarar, kuma zai samar da shugabanci nagari idan ya samu nasara
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Nasarawa - Yayin da zaɓen 2027 ke kara karatowa, tsohon sufeton ‘yan sanda, Mohammed Adamu, ya shiga sahun ‘yan siyasar da ke neman mulkin jihar Nasarawa.
Adamu, wanda ya rike mukamin Sufeto Janar na 20 a Najeriya, ya sanar da kudurinsa na tsayawa takarar gwamnan jihar a karkashin jam’iyyar APC.

Asali: Facebook
The Guardian ta wallafa cewa ya bayyana hakan ne a ranar Laraba, yayin wani taro da ya gudana a ofishin jam’iyyar APC da ke Lafia, babban birnin jihar Nasarawa.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Dalilin neman takarar IGP Adamu a APC
Mohammed Adamu ya ce kiran jama’a da goyon bayan da yake samu daga mutane daban-daban ne suka sa ya yanke shawarar tsayawa takara.
A cewar shi:
“Na amsa kiran jama’ar jihata da ke da yakinin cewa zan iya jagorantar jihar zuwa gaba.
Gwamnatina za ta dama da kowa, gaskiya da kuma himma wajen samar da ci gaba,”
Ya ce idan Allah ya ba shi nasara, zai mayar da hankali wajen inganta bangarori daban-daban na rayuwar al’umma kamar ilimi, lafiya, tsaro da tattalin arziki.
IGP Adamu zai kai labari a 2027?
Fitowar Mohammed Adamu a matsayin mai son yi takara a APC ya kara fito da jerin sunayen manyan ‘yan siyasar da ke son neman kujerar gwamnan Nasarawa a 2027.
Ana ganin Adamu na daya daga cikin ‘yan jam’iyyar APC da ke da karfi da gogewa, musamman ganin irin mukamin da ya rike a gwamnatin tarayya, wanda ana ganin hakan zai masa tasiri.
An ce tsohon Sufeto Janar din wanda ya fito daga birnin Lafia, yana da kusanci da jama’ar jihar da dama, lamarin da zai iya masa amfani a fafatawar siyasa.

Asali: Twitter
IGP Adamu ya yi aiki da shugaba Buhari
Mohammed Adamu ne Sufeto Janar na 20 a Najeriya, ya karbi ragamar jagoranci daga Ibrahim Kpotun Idris a ranar 15 ga Janairu, 2019.
An nada shi ne a mulkin tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari, bayan dogon aiki da gogewa a bangaren tsaro.
Yanzu haka, da ya yi murabus daga aikin dan sanda, ya koma siyasa da niyyar cigaba da hidimtawa jiharsa ta Nasarawa da Najeriya baki ɗaya.
Yadda aka nada Adamu sufeton 'yan sanda
Mohammed Adamu ya zama Sufeto Janar na 20 a tarihin rundunar ‘yan sandan Najeriya bayan da tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari ya nada shi a ranar 15 ga Janairu, 2019. An nada shi ne bayan ritayar Ibrahim Kpotun Idris, wanda ya kammala wa’adin aikinsa.
Kafin nadin nasa, Mohammed Adamu ya rike mukamai daban-daban a fannin tsaro da suka hada da aiki a sashen binciken manyan laifuka (CID) da kuma wakilci a hukumomin tsaro na kasashen waje kamar INTERPOL.
Buhari ya zabi Adamu ne saboda irin kwarewarsa da dogon tarihin aikinsa a rundunar ‘yan sanda, da kuma matsayin sa na mutum mai nutsuwa da sanin aiki.
Bayan nadin nasa, Adamu ya dauki matakan sauya fasalin tsarin tsaro, ciki har da daukar nauyin yaki da ‘yan bindiga da masu tada zaune tsaye a sassan kasar.
A lokacin aikinsa, ya fuskanci kalubale da dama da suka hada da zanga-zangar #EndSARS, wanda ya jawo cece-kuce kan yadda ake tafiyar da rundunar ‘yan sanda.
Duk da haka, ya kammala wa’adinsa da kwarin gwiwa, kuma yanzu yana amfani da wannan tarihin don neman kujerar gwamna a jiharsa ta Nasarawa a 2027.
An nemi Tinubu ya hakura da takarar 2027
A wani rahoton, kun ji cewa bayan ajiye aiki a fadar shugaban kasa, Hakeem Baba Ahmed ya bukaci Bola Tinubu ya hakura da takarar 2027.
Dr. Hakeem ya ce Bola Tinubu ya shafe kusan shekara biyu ba tare kawo wani gagarumin sauyi ba a Najeriya.
Ya kuma shawarci Tinubu da kar ya mayar da hankali a kan zaben 2027 a halin yanzu yana cewa lokacin siyasa bai yi ba.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng