"Hanya 1 Ta Rage," Limaman Masallatan Juma'a Sun Fitar da Matsaya kan Matsalar Tsaron Najeriya
- Kungiyar limaman masallatan Juma'a ta Najeriya ta ce tsarin tsaron Najeriya ya gaza, lokaci ya yi da za a koma ga Allah don neman dauki
- Mataimakin sakataren kungiyar na kasa, Dr Yusuf Abdullahi Yusuf ya bukaci limamai su dage da addu'o'i a masallatai don samun zaman lafiya
- Yusuf ya jaddada cewa Allah SWT ne kaɗai zai iya sauya halin da ake ciki a Najeriya idan aka koma gare shi ta hanyar addu'o'i
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Jos, Nigeria - Kungiyar Limaman Masallatan Juma’a ta Najeriya ta bayyana cewa tsarin tsaro da sauran tsare-tsaren ƙasa sun gaza, tare da kira da a dage da addu’a domin samun zaman lafiya da kwanciyar hankali.
Mataimakin sakataren kungiyar, Dr Yusuf Abdullahi Yusuf, ya bayyana hakan ne a ranar Juma’a yayin taron addu’a ta musamman da aka gudanar a Masallacin Juma’a na Jos domin neman zaman lafiya da haɗin kai.

Source: Facebook
Taron ya haɗa limamai da shugabannin addini daga sassa daban-daban na jihar Filato da ma Najeirya baki daya, kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.
Matsayar limamai kan tsarin tsaro
A cewarsa, idan limamai ba su tashi tsaye wajen addu’a da kuma jagorantar al'umma zuwa tafarkin shiriya ba, ba za a iya ceto ƙasar daga halin da take ciki ba
“Mu a matsayinmu na mutane, mun gaza, koƙarinmu na kashin kai ya gaza. Duk da muna da tsarin tsaro, amma ya gaza.
"Ƙasar nan na fuskantar matsaloli kamar tabarbarewar tattalin arziki, rikicin addini da ƙabilanci, fashi da makami, garkuwa da mutane da sauran ayyukan tashin hankali,” in ji shi.
Limamai sun kawo mafita ga Najeriya
Yusuf ya jaddada cewa Allah SWT ne kaɗai zai iya sauya halin da ake ciki a Najeriya idan aka koma gare shi ta hanyar dagewa da addu’o'i.
Ya ce addu’a za ta taimaka wajen shiryar da jami’an tsaro da shugabanni su ɗauki matakan da suka dace.
Ya kuma ƙara da cewa koyarwar fiyayyen halitta, Annabi Muhammad (SAW) ta ta’allaka ne kan zaman lafiya, haɗin kai da tsaro.

Source: Twitter
Umarnin da aka ba limaman Juma'a
Kungiyar ta bukaci limamai su riƙa sanya addu’ar zaman lafiya da haɗin kai a cikin hudubobin Juma’a a kai a kai, kamar yadda Vanguard ta ruwaito.
Ta bayyana cewa da wannan yunƙuri ne mai matukar kyau, kuma tana da fatan Allah zai karɓi addu’o’in limamai tare da kawo sauyi mai kyau a ƙasar nan.
Malami ya soki masu dorawa musulmi laifi
A wani rahoton, kun ji cewa wani malamin Musulunci, Imam Tajuddeen Muhammad Adigun, ya yi kakkausar suka kan abin ke faruwa a jihar Plateau.
Malamin ya koka kan yada labarin karya da ke nuna Musulmi a matsayin masu haddasa rikici da tashin hankali, wanda ke jawo asarar rayuka a jihar.
Ya ce irin wannan zargi na nuna son rai da kuma rashin daidaito, yana mai cewa Musulmi ba su da iko a Plateau da zai ba su damar shirya irin wadannan hare-hare.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

