Da Gaske Sanya Satilait a Gida Zai Kai Musulmi Wuta? Sheikh Ya Yi Fatawa

Da Gaske Sanya Satilait a Gida Zai Kai Musulmi Wuta? Sheikh Ya Yi Fatawa

  • Sheikh Habeebullah Adam El-Ilory ya ce ya kamata a sake duba wasu koyarwar addini da suka sabawa ci gaban al’umma na yau da kullum
  • Ya soki malaman da ke hana amfani da na'urorin zamani, ya ce yin haka ba ya hana shiga Aljanna domin tabbas aikata hakan ba laifi ba ne a addini
  • Malamin ya tuna yadda aka soki ra’ayinsa a 2010 kan shiga siyasar mata, amma yanzu Saudiya ma ta amince da hakan a dukan matakai na kasar
  • Ya zargi wasu malamai da fahimtar addini ba daidai ba, yana maicewa suna amfani da nassoshi ba tare da ilimi ba, ya ba su shawara kan haka

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

FCT, Abuja - Shahararren malamin addinin Musulunci, Sheikh Habeebullah Adam El-Ilory, ya kalubalanci wasu tsofaffin fahimtar addini da suka sabawa zamani.

Malamin wanda kuma shi ne Daraktan Markaz ya buƙaci malamai su waye wurin koyar da addini ga mabiyansu wanda ya dace da koyarwar zamani.

Sheikh ya soki wasu malamai kan fahimtarsu
Sheikh Habeebullah Adam El-Ilory ya soki fahimtar wasu malamai kan kayan zamani. Hoto: @Habibelilory.
Asali: Twitter

Fahimtar wasu malamai kan amfani da na'urorin zamani

A cikin hudubarsa ta baya-bayan nan, Sheikh Ilory ya soki wasu malamai da ke haramta kayan zamani da kuma shigar mata siyasa a cikin al’umma, cewar rahoton Punch.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya ambaci ikirarin da ake cewa amfani da na’urar satilait na hana shiga Aljanna, yana mai cewa hakan ba shi da tushe bare makama ko wata hujja.

A ikirarin, an ce:

“Duk wanda ya daura na’urar satilait a rufin gidansa kuma ya mutu, ba zai shiga Aljanna ba."
Sheikh Adam El-Ilory ya soki tsohuwar fahimtar wasu malamai
Sheikh Habeebullah Adam El-Ilory ya saɓa da fahimtar wasu malamai kan sanya satilait a gida. Hoto: @Habibelilory.
Asali: Twitter

Sheikh ya yi fashin baki kan fahimtar malamai

Sheikh Ilory ya kuma tuna yadda aka soki kalamansa a shekarar 2010 lokacin da ya bayyana goyon bayansa ga siyasar mata.

Ya ce daga baya Saudiya ta amince mata su jefa kuri’a tare da shiga harkokin siyasa, abin da ke nuna sauyi a fahimta.

Ya ce:

“Da na ce a 2010 cewa mata za su iya shiga siyasa, mutane sun yi mani kaca-kaca.
“A halin yanzu, ana koyar da mata harkar soja a Saudiya kuma suna saka wando."

Malamin ya caccaki wasu malamai da ke daurewa tsofaffin ra’ayoyi gindi, yana cewa suna karkatar da nassosin addini.

Ya ce addinin Musulunci na zamani ne amma wasu suna fahimtarsa yadda bai dace ba, ya shawarce su kan yi wa koyarwarsu duba na zamani.

Ganin wata: Malami ya saɓa wa Sarkin Musulmi

Kun ji cewa Sheikh Muhammed Habibullah Adam Abdullah El-Ilory ya bayyana Litinin, 31 ga Maris, 2025, a matsayin ranar Eid-el-Fitr a Najeriya, bisa ga ka’idojin ilimi da addini.

Malamin ya ce ba za a iya ganin sabon jinjirin wata ba a ranar 29 ga Maris, 2025, don haka 31 ga Maris din 2025 ita ce ranar farko ta Shawwal.

Sheikh El-Ilory ya jaddada cewa ilimin taurari na zamani na iya hango lokaci da matsayin wata, kamar yadda ake hasashen faduwar rana da duniyar rana.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.