Karfin Hali: Ƴan Fashi Sun Shiga Teku, Sun Sace Jirgin Ruwa Maƙare da Ɗanyen Mai
- Wasu 'yan fashin teku sun yi awon gaba da jirgin ruwan Honour 25 dauke da ma'aikata 17 yayin da yake kusa da gabar tekun Somaliya
- Wannan satar jirgin man fetur, wanda ke dauke da gangar mai 18,500, na iya janyo karin tashin farashin man fetur a babban birnin Mogadishu
- Kawo yanzu dai babu wata sanarwa a hukumance daga gwamnatin Somaliya ko rundunar tsaron teku ta Turai game da wannan hari
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.
Somaliya – Jami’an tsaro da dama sun tabbatar da cewa wasu ‘yan fashin teku sun yi awon gaba da jirgin dakon man fetur mai suna Honour 25 a kusa da gabar tekun Somaliya.
Mahara shida dauke da makamai ne suka mamaye jirgin a daren ranar Laraba, inda suka kwace ikon sa yayin da yake nisan mil 30 daga gabar teku.

Source: Getty Images
Wannan lamari ya tayar da hankali a yankin tekun Indiya, wanda aka dade ba a fuskanci irin wannan satar jiragen ruwan ba tun shekaru uku da suka gabata, in ji rahoton BBC.
Yadda sace jirgin zai shafi tattalin Somaliya
Jirgin, wanda ke dauke da gangar mai dubu 18,500, ya nufi birnin Mogadishu ne lokacin da aka sace shi. Masana tattalin arziki na fargabar cewa wannan danyen aikin zai kara jefa babban birnin na Somaliya cikin garari.
A cikin jirgin akwai ma'aikata guda 17 wadanda suka hada da 'yan kasar Pakistan guda 10, 'yan kasar Indonesiya guda hudu, sai kuma guda daya-daya daga kasashen Indiya, Sri Lanka, da kuma Myanmar.
Bayanan da aka samu sun nuna cewa 'yan fashin sun tsare jirgin ne a kusa da garuruwan kamun kifi na Xaafun da Bander Beyla.
Rahotanni sun nuna cewa wasu karin maharan guda biyar sun sake shiga cikin jirgin bayan an riga an tsare shi, wanda hakan ke nuna cewa akwai wani tsari na musamman da maharan suka bi domin tabbatar da cewa sun rike jirgin a karkashin ikon su.

Kara karanta wannan
Hormuz: Matakin Amurka da Iran ya ta'azzara farashin fetur a duniya, ganga ta haura $100
Abin da ya faru kafin sace jirgin Honour 25
Bayanai daga Yahoo News sun nuna cewa jirgin ya bar tashar jiragen ruwa ta Berbera a Somaliland tun ranar 20 ga watan Fabrairu, 2026.
Bayan ya yi shawagi a kusa da tekun hadaddiyar daular Larabawa (UAE), ya juya ne a ranar 2 ga watan Afrilu domin nufar Mogadishu.
Shi dai wannan jirgin ya shafe kwanaki yana kewaye a cikin ruwan da ke kusa da mashigar Hormuz kafin ya yanke shawarar komawa Somaliya, inda a karshe 'yan fashin suka yi masa kwanton bauna kusa da Bander Beyla.
Kawo yanzu dai, hukumomin Somaliya da kuma rundunar tsaron teku ta Tarayyar Turai (EUNAVFOR), wadanda ke sa ido kan harkokin tsaro a tekun Somaliya, ba su fitar da wata sanarwa a hukumance ba.

Source: Getty Images
Fargabar karuwar 'yan fashin teku
Masana harkokin tsaro na ganin cewa idan ba a dauki matakin gaggawa ba, 'yan fashin za su ci gaba da amfani da wannan dama wajen neman kudin fansa ko kuma yin zagon kasa ga harkokin kasuwanci na duniya.
A baya, fashin teku ya taba zama babban kalubale ga tattalin arzikin duniya, inda dubban jirage suka fada hannun mahara, lamarin da ya janyo asarar biliyoyin daloli.
Sace Honour 25 babban jan kunne ne ga kasashen duniya cewa barazanar fashin teku ba ta gushe gaba daya ba.
'Yan fashin teku sun tare jirgi a Najeriya
A wani labari, mun ruwaito cewa, 'yan fashin teku sun tare jirgin ruwa, sun yi awon gaba da fasinjoji 13 a kogin Idaka da ke ƙaramar hukumar Okrika a jihar Ribas.
Maharan sun kuma kwace wasu jiragen ruwa biyu da suka ɗauko kayayyaki amma daga bisani an ji cewa an yi nasarar ƙwato su.
Shugaban kungiyar ma'aikatan sufurin ruwa (NWU) ya nemi Kantoma ya gaggauta ɗaukar mataki domin abin na neman wuce gona da iri.
Asali: Legit.ng

