Kwamkwasiyya Ta Rikice: Ɗan Majalisar Kano, Kabiru Rurum Ya Fice daga NNPP zuwa APC

Kwamkwasiyya Ta Rikice: Ɗan Majalisar Kano, Kabiru Rurum Ya Fice daga NNPP zuwa APC

  • Siyasar jihar Kano ta sake rikicewa bayan Kabiru Alhassan Rurum, dan majalisar wakilai daga NNPP ya koma jam’iyyar APC mai mulki
  • Rurum wanda ke wakiltar Rano/Kibiya/Bunkure ya taba rike mukamin kakakin majalisar Kano, kuma dama tsohon mamba ne na APC
  • Jama’a sun rarrabu kan sauya shekar; wasu sun zarge shi da son kai, yayin da wasu ke ganin hakan wani tasiri ne na siyasar 2027

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Kano - Siyasar jihar Kano ta sake rikicewa a karo na biyu a cikin kwanaki biyu yayin da dan majalisar wakilai, Kabiru Alhassan Rurum ya fice daga NNPP.

Kabiru Alhassan Rurum wanda ke wakiltar mazabar Rano/Kibiya/Bunkure a majalisar wakilai ta tarayya ya fice daga NNPP ne zuwa APC mai mulki a kasa.

Dan majalisar Kano, Kabiru Alhassan Rurum ya sauya sheka daga NNPP zuwa APC.
Dan majalisar wakilai, Kabiru Alhassan Rurum daga jihar Kano. Hoto: Fatihu Yusuf Abdullahi
Asali: Facebook

Dan majalisar Kano ya fice daga NNPP zuwa APC

Tsohon mai tallafawa tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari kan kafofin sada zumunta, Bashir Ahmad ya sanar da sauya shekar Kabiru Rurum a shafinsa na X.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A sanarwar da ya fitar a yammacin ranar Alhamis, 24 ga watan Afrilu, Bashir Ahmad ya ce Kabiru Rurum ya sanar da komawa APC a hukumance.

Kabiru Alhassan Rurum ba bako ba ne a siyasar Kano domin ya taba rike mukamin kakakin majalisar Kano, kuma dama can tsohon mamba ne na jam'iyyar APC.

Sanarwar Bashir Ahmad ta ce:

"Tsohon kakakin majalisar dokokin jihar Kano, Rt. Hon. Kabiru Alhassan Rurum, wanda yanzu ke wakiltar Rano, Kibiya da Bunkure a majalisar wakilai, ya sanar da ficewarsa daga jam’iyyar NNPP tare da komawa jam’iyyarsa ta asali, watau APC."

Martanin mutane kan sauya shekar Rurum

Legit Hausa ta tattaro wasu daga cikin ra'ayoyin mutane game da sauya shekar Hon. Kabiru Rurum:

@Dele93748586:

"Zuwa shekara mai zuwa, PDP za ta daina wanzuwa a matsayin jam’iyyar siyasa."

@metublaze:

"Rurum bai da kishin jama’a, ficewarsa daga NNPP zuwa APC cin amanar wadanda suka zabe shi ne.
"Ya bar NNPP ne don ribar kansa, kuma hakan yana tarwatsa hadin kai da cigaban Kano. Yanzu dai an gano shi dan siyasa ne mai cike da son kai."

@gbengagiwa_gg:

"Idan aka ci gaba da tafiya a haka, to ba zan yi mamaki ba idan @AishaYesufu ta ce Shugaba @officialABAT 'shine shugabana'."

@Manlikeskindo98:

"Ganduje ba kanwar lasa ba ne."

"Duk su yi su gama" - Ambasada Habeeb

Mun ci gaba da tattaro ra'ayoyin mutane game da wannan sauya sheka:

@LinusChime:

"Eh, har ma da hukumar INEC, duk sun koma APC."

@AmbHabeeb:

"Duk su yi su gama kawai."

@Anthonydennis27:

"Kowa ya tafa masu. Babban abin da APC ke yi kena; tara ‘yan siyasa daga sauran jam’iyyu."

@Garbxt:

"Masu shakku da wannan gwamnati za su ga sakamako idan jam’iyyunsu suka fara karewa."

@BelloMuhd63408:

"Waɗannan ‘yan siyasar suna yaudarar masu zabe ne kawai. Burinsu kawai shi ne cikar muradunsu na siyasa. Allah yana kallon komai."

Duba sanarwar a kasa:

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.