Sanusi II Ya Magantu kan Yawan Cin Bashin Gwamnatin Tinubu duk da Cire Tallafin Fetur
- Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II, ya kalubalanci gwamnatin tarayya bayan cire tallafin mai a Najeriya wanda ya jawo maganganu a kasar
- Sarkin ya tambayi dalilin ci gaba da karbar bashi duk da cire tallafin mai, yana gargadin cewa rashin daidaito na iya lalata ribar sauye-sauyen
- Ya ce gyaran farashin dala da cire tallafi sun dace amma lokaci da rashin tsauraran manufofi sun janyo faduwar Naira, yana bukatar karin tsari mai kyau
CHECK OUT: How to Start Earning with Copywriting in Just 7 Days – Even if You’re a Complete Beginner
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Kano - Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II, ya nuna damuwa kan yadda gwamnatin tarayya ke ci gaba da karbar bashi wanda ke kara jawo matsala ga tattalin arziki.
Sarkin ya nuna takaici kan karɓar basukan ne duk da cire tallafin mai wanda ya jefa al'umma mummunan hali tun farkon hawan gwamnatin Bola Tinubu a Mayun 2023.

Kara karanta wannan
Ningi: Babban kuskuren da zai hana wasu sanatoci da 'yan majalisu koma wa kujerunsu a 2027

Source: Facebook
A wata hira da News Central TV ta wallafa, tsohon gwamnan Babban Bankin Najeriya ya ce cire tallafi da sassauta farashin dala sun dace amma akwai matsaloli.
Muhammadu Sanusi II ya kawo mafitar inganta tattalin arziki
Sarkin ya bayyana cewa rashin tsauraran matakan kudi da rashin tsari mai kyau sun janyo faduwar darajar Naira cikin sauri, abin da ke janyo matsaloli.
Sanusi II ya ce tallafawa matatun mai na kasashen waje alhali na cikin gida ba sa aiki yadda ya kamata wata babbar matsala ce.
Sai dai ya nuna farin ciki cewa yanzu Najeriya na da matatar mai a gida, tana rage shigo da mai tare da fara fitar da shi wanda kuma zai kara inganta tattalin arziki.
Ya ce:
“Yanzu muna da matatar mai a gida, ba mu shigo da mai ba, har muna fitarwa zuwa Turai, wannan abu ne mai kyau ga tattalin arziki.”

Source: Twitter
Tattalin arziki: Sarki Sanusi II ya ankarar da Tinubu
Duk da haka, ya ce akwai tambayoyi kan lokacin aiwatar da sauye-sauyen da kuma ko an yi wasu muhimman matakai kafin aiwatar da su.
Ya kara da cewa sassauta farashin dala a yanayin da ake da yawan kudin da ke yawo ya janyo karin faduwar darajar Naira.
Sanusi II ya ce:
“Ba zai yiwu ka cire tallafi ba sannan ka ci gaba da karbar bashi, dole ne a ga amfanin kudin da aka samu.”
Ya jaddada cewa idan gwamnati ba ta kashe kudin tallafi ba, ya kamata a rage karbar bashi kuma a inganta tsarin kudade yadda ya kamata.
Yadda Sanusi II ya yabi Tinubu da CBN
A baya, mun ba ku labarin cewa Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II ya yaba da matakan da gwamnatin Bola Tinubu ke ɗauka don farfaɗo da tattalin arzikin ƙasa.
Khalifa Sanusi II, wanda tsohon Gwamnan CBN ne ya ce cire tallafin mai da daidaita farashin Dala da Naira sun taimaka wa Najeriya da kuma tattalin arzikinta.
Mai Martaban ya bayyana cewa tattalin arziki na nuna alamun farfaɗowa, duk da buƙatar ƙarin gyare-gyare da ba za a rasa ba a yanzu.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
