Latest
Bayan ta ce an samu inganci a bangaren ilimi a Najeriya, gwamnatin tarayya ta dakatar da ba da tallafin karatu ga ɗaliban da ke karatu a ƙasashen waje.
Isra'ila ta yi barazanar kai hari Iran kamar yadda ta yi wa Hamas da Hezbollah, bayan harin Houthi, kuma ta ce za ta iya kare kanta ba tare da taimakon Amurka ba.
Alhaji Aliko Dangote na shirin kafa katafaren kamfanin sukari a kasar Ghana. Kamfanin zai samar da ayyuka ga matasa da dama da bunkasa tattakin arzikin Afrika.
Najeriya ta kammala biyan bashin dala biliyan $3.4 daga IMF, wanda aka karba a 2020 don tallafin Korona; yanzu ba ta cikin jerin kasashen da ake bi bashi.
'Yan bangaren CPC da suke tare da shugaba Buhari a CPC sun jaddada cewa za su cigaba da goyon bayan Bola Tinubu. sun ce suna nan daram a jam'iyyar APC.
Gwamnan jihar Ondo, Lucky Aiyedatiwa ya samu nasarar a ƙarar da NNPP da ɗan takararta na gwamna, Hon. Gbenga Edema suka kalubalanci zaɓen fidda gwanin APC.
An tsaurara tsaro a Anambra gabanin ziyarar Tinubu. Ana sa ran shugaban kasar zai ƙaddamar da wasu muhimman ayyuka da gwamnatin jihar ta kammala.
An yi ta yada wasu rahotanni cewa shugaban hukumar zabe ta INEC, Farfesa Mahmud Yakubu ya nemi afuwar ƴan Najeriya kan canza sakamakon zaben 2023.
Jam'iyyar PDP mai adawa a Najeriya ta sake yin rashi na wasu mambobinta a majalisar wakilai. 'Yan majalisar wadanda suka fito daga Katsina sun koma APC.
Masu zafi
Samu kari