Bayan Boye Boye saboda Yaƙin Iran, Netanyahu Ya Fadi Halin Lafiyarsa

Bayan Boye Boye saboda Yaƙin Iran, Netanyahu Ya Fadi Halin Lafiyarsa

  • Firaministan Isra’ila, Benjamin Netanyahu ya bayyana halin da ya shiga bayan kamuwa da rashin lafiya na tsawon lokaci
  • Netanyahu ya bayyana cewa ya warke daga cutar daji bayan an gano ta a farkon mataki kuma aka yi masa magani cikin nasara
  • Rahoton lafiyarsa ya nuna an gano cutar ne bayan gwaje-gwaje na yau da kullum, amma ya ɓoye batun saboda yaƙin Iran don kauce wa amfani da shi

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Tel Aviv, Israel - Firaministan Isra’ila, Benjamin Netanyahu, ya yi karin bayani kan halin lafiyarsa bayan kamuwa da cuta

Benjamin Netanyahu ya bayyana cewa ya samu cikakkiyar lafiya bayan an yi masa nasarar maganin cutar daji a farkon mataki.

Netanyahu ya tabbatar da warkewa daga cuta a lokacin yaki
Firayim ministan Isra'ila, Benjamin Netanyahu a birnin Tel Aviv. Hoto: Anadolu Ajansi.
Source: Getty Images

Fitayim ministan ya bayyana haka ne a cikin wani rubutu da ya yi a shafinsa na X a yau Juma'a 24 ga watan Afrilun 2026.

Kara karanta wannan

Kwana ya kare: Daga fitowa motsa jiki, tsohon 'dan wasan Najeriya ya rasu a Kaduna

Yadda aka kula da lafiyar Netanyahu ana yaƙi

Rahoton ya nuna cewa an fara yi masa tiyata a watan Disamba 2024 saboda kumburi, inda aka ce aikin ya gudana cikin nasara ba tare da wata matsala ba.

Bayan haka, binciken MRI ya gano wata ƙaramar alama mai girman ƙasa da milimita ɗaya, wanda ƙarin gwaje-gwaje suka tabbatar da cewa cutar sankara ce a matakin farko.

Netanyahu ya bayyana cewa ya jinkirta fitar da rahoton na tsawon watanni biyu domin kada Iran ta yi amfani da yanayin lafiyarsa wajen yaɗa farfaganda a lokacin yaƙi.

Ya ce:

“Na yanke shawarar jinkirta fitar da rahoton domin kada a fitar da shi a lokacin kololuwar yaƙi inda Iran za ta iya amfani da shi”

Ya ƙara da cewa yanzu yana cikin ƙoshin lafiya da ƙarfi bayan an cire cutar gaba ɗaya, yana mai jaddada cewa an gano ta tun tana matakin farko.

Netanyahu ya fadi cutar da ta ke damunsa
Firayim ministan Isra'ila, Benjamin Netanyahu yana jawabi a birnin Tel Aviv. Hoto: Benjamin Netanyahu.
Source: Facebook

Karin da ya fito a jikin Netanyahu

Likitan da ya jagoranci jinyar, Farfesa Aharon Popovzer, ya ce an gano ƙari mai girman santimita 0.9 wanda aka tabbatar cutar sankara ce, cewar The Jerusalem Post.

Kara karanta wannan

2027: An fara zargin Obi zai yaudari 'yan Arewa saboda ya muzguna masu a baya

Ya bayyana cewa an yi masa cikakken bincike sannan aka tabbatar cutar na cikin mataki na farko, wanda hakan ya taimaka wajen samun sauƙin magani.

Likitan ya ƙara da cewa an yi masa jinya ta zamani a asibitin Hadassah, kuma sakamakon gwaje-gwaje ya nuna cewa cutar ta ɓace gaba ɗaya.

Rahoton ya kammala da cewa jinyar ta yi nasara sosai, inda aka tabbatar da bacewar cutar ta hanyar hotuna da gwaje-gwajen dakin gwaje-gwaje bayan jiyya.

'Dan uwan Netanyahu ya rasu a yaƙi

A baya, kun ji cewa Firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu ya aika sako na ban tausayi don tunawa da marigayi ɗan uwansa, Yoni Netanyahu.

Yoni Netanyahu, babban jami'in sojan IDF da aka karrama, wanda aka kashe a lokacin aikin ceto na Entebbe a ƙasar Uganda a shekarar 1976.

Firaministan na Israila ya bayyana cewa yana cikin kewar dan uwan na sa tun bayan da aka raba shi da duniya inda ya yi masa fatan alheri.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.