Gwamnatin Tinubu Ta Dakatar da ba da Lamunin Karatu ga Ɗalibai zuwa Ƙetare

Gwamnatin Tinubu Ta Dakatar da ba da Lamunin Karatu ga Ɗalibai zuwa Ƙetare

  • Gwamnatin tarayya ta dakatar da tallafin karatu ga ɗaliban da ke karatu a ƙasashen waje, tana mai cewa akwai makarantun gida masu inganci
  • Ministan ilimi, Morufu Olatunji Alausa, ya ce ba zai yiwu a ci gaba da kashe kuɗi kan karatu a waje ba yayin da akwai madadinsu a cikin gida
  • Dr. Olatunji Alausa ya ce ɗaliban da ke ci gaba da karatu yanzu za su ci gaba da samun tallafi har su gama, amma kudin zai fi amfani a cikin gida

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

FCT, Abuja - Gwamnatin tarayya ta dakatar da shirin tallafin karatu na 'Bilateral Education Agreement (BEA)' ga ɗaliban jami’a da ke karatu a ketare.

Gwamnatin tarayya ta ce ta dauki matakin ne saboda saboda ƙarancin kuɗi da bunƙasar ilimi a gida Najeriya wanda bai zama dole sai an fita ketare kan hakan ba.

Tinubu ya dakatar da lamunin karatu ga dalibai
Gwamnatin Tinubu ta soke lamunin karatu ga dalibai. Hoto: Ministry of Education Nigeria.
Asali: Twitter

An dakatar da tallafin karatun dalibai a ketare

Wannan na kunshe a cikin wata sanarwa da shafin ma'aikatar ya wallafa a manhajar Facebook.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Hakan ya zo ne a daidai lokacin da ƙasar ke fama da matsin tattalin arziki sakamakon sauye-sauyen da Shugaba Bola Tinubu ya kawo.

Ministan ilimi, Morufu Olatunji Alausa shi ya tabbatar da hakan inda ya ce bangaren ilimi a Najeriya ya bunƙasa.

Alausa ya ce sun dakatar da ba da lamunin karatu zuwa ketare na BEA ba tare da ba ta lokaci ba.

Ya ce:

"Kowane fanni da 'yan Najeriya ke zuwa karatu a waje ta BEA, yanzu akwai shi a nan kuma mai inganci a jami’o’inmu da kwalejojin da muke da su.
"Ba za a ci gaba da kashe kuɗin gwamnati kan karatu a ƙasashen waje ba alhali akwai makarantun gida masu nagarta a cikin gida."
Tinubu ya dakatar da lamunin karatu na dalibai
Tinubu ya soke lamunin karatu na dalibai a ƙetare. Hoto: Asiwaju Bola Tinubu.
Asali: Facebook

Gwamnati ta fadi inda za ta ba karfi

Alausa ya ce zai fi kyau a mayar da kuɗin tallafin wajen ƙarfafa jami’o’in cikin gida domin ƙara wa ilimi ɗorewa da inganci a ƙasar da ke fama da matsaloli.

Ya ƙara da cewa waɗanda ke ci gaba da karatu a karkashin shirin za su ci gaba da samun tallafi har zuwa lokacin da za su kammala karatunsu.

Ɗalibai da dama sun samu damar amfani da tallafin wurin zuwa kasashen ketare da yawa domin inganta ilimi da kuma rayuwarsu.

Sai dai wasu na ganin wannan sabon tsari da aka kawo zai iya kawo cikas ga ɓangaren ilimi duba da yadda harkar ta lalace a cikin gida.

Gwamnatin Tinubu ta yarda a kafa sababbin jami'o'i

A baya, kun ji cewa Gwamnatin Tarayya ta amince da kafa sababbin jami'o'i na kudi guda 11 domin bunkasa harkokin neman ilimi a Najeriya.

Shugaban hukumar kula da jami'o'i ta ƙasa, Farfesa Abdullahi Ribaɗu ne ya miƙa lasisin fara aiki ga sababbin makarantun a birnin Tarayya, Abuja.

Ministan ilimi, Tunji Alausa ya buƙaci makarantun kudi su yi haɗin guiwa da juna da haɗa kai da jami'o'in duniya wajen bunƙasa harkokin ilimi.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.