Bayan Katsina, Gwamnati Ta Fadi Jihar da Tinubu Zai Bude Ayyuka Ranar Alhamis
- Rahotanni sun bayyana cewa an jibge 'yan sanda, sojoji, DSS, NSCDC da sauran jami'an tsaro a Anambra gabanin ziyarar Shugaba Bola Tinubu
- Hukumar tsaron farar hula (NSCDC) ta ce ta ta tura jami'ai 1,531 zuwa sassa daban daban na birnin Awka, domin tabbatar da tsaro a ranar Alhamis
- Ana sa ran Tinubu zai ƙaddamar da ayyuka kamar Solution FunCity, sabon gidan gwamnati, da cibiyar Emeka Anyaoku, da dai sauransu a Anambra
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Anambra - An ƙara tsaurara matakan tsaro a faɗin Awka, babban birnin jihar Anambra, gabanin ziyarar da Shugaba Bola Tinubu ya shirya yi a ranar Alhamis.
An rahoto cewa an rufe wasu titunan Awka tare da tsaurara jami'an tsaro a wurare masu mahimmanci daban-daban a cikin birnin.

Asali: Twitter
An jibge jami'an tsaro a Anambra
Rahoton jaridar Vanguard ya nuna cewa an jibge jami'an rundunar 'yan sandan Najeriya, hukumar tsaron farin kaya (DSS) da sojojin Najeriya.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sauran hukumomin tsaron da aka gani sun hada da, rundunar tsaron farar hula (NSCDC), hukumar kiyaye haɗurra (FRSC), da ƙungiyoyin 'yan banga na jihar.
Jami’in hulɗa da jama’a na ‘yan sandan Anambra, SP Tochukwu Ikenga, ya tabbatar da cewa jami’an tsaro sun daura damarar tabbatar da tsaro kafin, yayin, da kuma bayan ziyarar Tinubu.
SP Tochukwu Ikenga ya bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa da aka bai wa manema labarai a jiya Larabawa, a birnin Awka.
NSCDC ta tura jami'ai 1,531 Awka
Ya ƙara da cewa matakan da aka dauka za su ingan tsarin tsaro na jihar don tabbatar da tsaron shugaban ƙasa, manyan baƙi, da duk masu halartar taron a jihar.
Rundunar NSCDC, reshen jihar Anambra, ta ce ta tura jami'anta 1,531 zuwa Awka don ƙarfafa tsaro gabanin ziyarar Shugaba Bola Tinubu.
Kwamandan rundunar na jihar, Olatunde Maku, ya bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa da jami’in hulɗa da jama’a na rundunar, Edwin Okadigbo, ya fitar a Awka a ranar Laraba.
Jaridar Tribune ta rahtoo Olatunde ya bayyana cewa za a ɗauko ma'aikatan ne daga Enugu, Imo, Abia, Ebonyi da Delta don ƙarfafa ayyukan tsaro a Anambra.

Asali: Original
Ayyukan da Tinubu zai kaddamar a Anambra
A halin da ake ciki, ana ta murna a faɗin jihar, musamman a Awka, inda aka yi wa manyan titunan birnin ado da kuma allunan masu dauke da sakonni daban daban, kamar:
“Mai girma shugaban kasa, Ndi Anambra na son ka,” “Muna tare da Shugaba Bola Ahmed Tinubu har gobe,” “Asiwaju Nnoo, Anambra na yi maka barka da zuwa."
Ana sa ran Tinubu zai ƙaddamar da muhimman ayyuka da dama, ciki har da ginin bifnin Solution FunCity, Anambra Country Club, sabon gidan gwamnati, sabon gidan gwamna da sabon gidan saukar shugaban kasa.
Tinubu zai kuma buɗe cibiyar Emeka Anyaoku a jami'ar Nnamdi Azikiwe, da wata hasumiya da kamfanin Dutum ya gina a gidan gwamnati don zama alamar jiha.
Bola Tinubu ya bude ayyuka a jihar Katsina
A wani labarin, mun ruwaito cewa, a ranar Juma'a, 3 ga Mayu, 2025, Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya kai ziyarar aiki ta yini ɗaya a jihar Katsina.
Ziyarar shugaban kasar ta mayar da hankali ne kan ƙaddamar da wasu muhimman ayyukan da gwamnatin Malam Dikko Umaru Radda ta kammala.
A cikin ayyukan da shugaban ƙasa zai ƙaddamar akwai titin da ya tashi daga Dutsin-ma, ya ratsa ta Kano/Daura, har zuwa Yandaki a ƙaramar hukumar Kaita.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng