Kwana Ya Kare: Daga Fitowa Motsa Jiki, Tsohon Dan Wasan Najeriya Ya Rasu a Kaduna
- Tsohon dan wasan gaba na Najeriya, Mike Eneramo ya riga mu gidan gaskiya yayin atisayen motsa jiki a jihar Kaduna
- Rahotanni sun nuna cewa Eneramo ya fito motsa jiki a filin makarantar Firamare da ke Unguwan Yelwa, sai ya yanke jiki ya fadi kuma rai ya yi halinsa
- Eneramo ya yi ritaya daga buga ƙwallon ƙafa a shekarar 2018 bayan ya shafe shekaru yana taka leda a ƙasashen waje, musamman a kasar Turkiyya
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Jihar Kaduna, Nigeria - An shiga jimami bayan tabbatar da rasuwar tsohon dan wasan gaba na kungiyar kwallon kafa ta Najeriya, Mike Eneramo.
Rahotanni sun nuna cewa tsohon ɗan wasan gaban ya rasa rayuwarsa ne bayan ya fito atisaye da nufin motsa jikinsa a jihar Kaduna mai tarihin 'yan kwallo.

Source: Facebook
Rahoton jaridar Daily Trust ya nuna cewa lamarin ya faru ne da safiyar Juma’a yayin atisayen motsa jiki a filin kwallo na makarantar firamare da ke Ungiluwan Yelwa a jihar Kaduna.
Yadda lamarin ya faru a Kaduna
An ce Eneramo ya gamu da bugun zuciya ne a lokacin da ake tsakiyar atisayen, kuma ya rasu kafin a kai shi asibiti domin samun kulawa.
Bayanan da aka samu sun nuna cewa 'dan wasan kwallon kafar ya rasu yana da shekaru 40 na haihuwa.
Tarihin rayuwarsa a kwallon kafa
Eneramo ya yi ritaya daga buga ƙwallon ƙafa a shekarar 2018 bayan ya shafe shekaru yana taka leda a ƙasashen waje, musamman a kasar Turkiyya.
Ya taka leda a kungiyoyi kamar Sivasspor, Besiktas, Istanbul Basaksehir, Karabukspor da Manisaspor.
Haka kuma ya yi fice sosai a ƙungiyar Esperance ta Tunisia, inda ya lashe kofin lig na ƙasar sau biyar, tare da zama wanda ya fi kowa cin ƙwallo a kakar wasa sau biyu.

Kara karanta wannan
Arewa da Kudu za su amfana da Tinubu ya nemi izinin sake ciyo bashin Dala miliyan 516
Ya kuma zama gwarzon mai cin ƙwallo a gasar CAF Champions League ta kakar 2009/2010, sannan ya lashe kofin ƙasar Tunisia sau uku.
Gudunmawar 'dan wasan kwallon ga Najeriya
Tsohon ɗan wasan ya buga wa ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Najeriya, Super Eagles, wasanni 11 inda ya zura ƙwallaye uku.
Duk da cewa an taɓa neman ya wakilci ƙasar Tunisia, ya ƙi wannan tayin domin ya ci gaba da bugawa Najeriya.

Source: Getty Images
Abin lura shi ne, ya fara buga wa Najeriya wasa ne a karon farko da Tunisia a gasar neman gurbin shiga gasar cin kofin duniya ta 2010, inda ya zura ƙwallo a wasan.
Ana sa ran za a sanar da shirye-shiryen jana’izarsa nan gaba kaɗan, kamar yadda jaridar Leadership ta kawo.
Tsohon dan wasan tsakiya ya mutu
A wani rahoton, kun ji cewa tsohon dan wasan tsakiya na Super Eagles, Henry Nwosu, ya rasu yana da shekaru 62 a duniya.
Tsohon abokin wasansa Segun Odegbami ne ya sanar da rasuwarsa, yana mai bayyana alhini da jimamin wannan babban rashi da suka yi.
Odegbami ya ce tun daga ranar Laraba 11 ga watan Maris din shekarar 2026 aka kwantar da shi a sashen kulawa ta musamman amma daga bisani rai ya yi halinsa.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
