Asusun Lamuni na IMF Ya Cire Najeriya daga cikin Jerin Kasashen da Yake Bi Bashi

Asusun Lamuni na IMF Ya Cire Najeriya daga cikin Jerin Kasashen da Yake Bi Bashi

  •  Najeriya ta kammala biyan bashin dala biliyan 3.4 da ta karɓa daga IMF a 2020 a matsayin tallafin cutar COVID-19
  •  IMF ta cire sunan Najeriya daga cikin jerin kasashen da ke da bashi daga ranar 1 zuwa 6 ga Mayu, 2025 da ake ciki
  •  Gwamnatin Tinubu ta ce biyan bashin na nuna cewa Najeriya na tafiyar da tattalin arzikinta bisa gaskiya da amana

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

FCT Abuja – Asusun ba da lamuni na duniya (IMF) ya cire sunan Najeriya daga jerin kasashen da ke da bashi a wajensa daga ranar 1 zuwa 6 ga Mayu, 2025

A cikin jerin, wanda aka wallafa a ranar Talata, sama da kasashe 90 ne ke bin bashi jimillar dala biliyan 117.79, kuma Najeriya ba ta cikin su.

Banki
Asusun IMF ya cire Najeriya daga cikin kasashen da take bi bashi Hoto: @KGeorgieva
Asali: Twitter

Jaridar The Cable ta ruwaito cewa bayanai daga IMF sun tabbatar da cewa cibiyar ta Bretton Woods ta bayar da lamunin SDR biliyan 2.45 ga Najeriya a shekarar 2020.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Bankin bayar da lamuni na duniya (IMF) na amfani da nau'in kudi na SDR, wato Special Drawing Right, a tsarin ajiyar kudinsa.

Najeriya ta biya bashin IMF

Jaridar Punch ta ruwaito cewa, bisa bayanan IMF, an biya kudin biyan bashi kamar haka: SDR miliyan 613.62 a 2023, SDR biliyan 1.22 a 2024, da kuma SDR miliyan 613.62 a 2025.

IMF ba ta fitar da wata sanarwa kai tsaye game da sabunta jerin kasashen da ke bi bashi wanda aka karba a lokacin Korona.

Da yake tsokaci kan batun, Tolu Ogunlesi, tsohon hadimin Shugaba Muhammadu Buhari, ya tabbatar da cewa Najeriya ta biya kudin da gwamnatinsu ta karbo. Ogunlesi ya ce an kammala biyan bashin ne cikin shekaru biyar kamar yadda aka amince tun farko.

Ya ce:

“Wannan lamuni na dala biliyan $3.4 (daidai da SDR biliyan 2.454.5) tallafin Korona da IMF ta bayar, yanzu an gama biya kamar yadda aka tsara a yarjejeniyar.”
“Gwamnatin PBAT ta bi ka’idojin yarjejeniyar, kuma zuwa watan Mayu 2025, an kammala biyan bashin. Najeriya ba ta da dabi’ar gasawa wajen biyan bashi."

Hadimin Tinubu ya magantu kan bashin IMF

Shi ma, O’tega Ogra, babban mai taimaka wa Shugaba Bola Tinubu kan kafafen yada labarai na zamani, ya ce biyan bashin ya nuna cewa karan Najeriya ya tsaiko.

Tinubu
Najeriya ta biya bashin IMF da aka karbo a lokacin Korona Hoto: Bayo Onanuga
Asali: Facebook

Ya kara da cewa hakan zai nuna wa duniya da 'yan Najeriya cewa kasar na da niyyar tafiyar da tattalin arzikinta da hangen nesa da gaskiya da amana. Ogra ya ce daga yanzu duk wata hulda ta gaba da IMF za ta kasance bisa tsari na hadin gwiwa, ba dogaro da asusun ba.

Ana zargin IMF da ingiza gwamnatin Najeriya

A wani labarin, kun ji shahararren lauya mai kare hakkin dan Adam, Femi Falana (SAN), ya zargi IMF da Bankin Duniya da matsa wa gwamnatin Najeriya lamba.

A cewar Falana, karin kudin wutar lantarki da gwamnatin tarayya ta aiwatar a baya, ba wani abu ba ne illa cika bukatun wadannan cibiyoyi na kasashen waje.

Falana ya jaddada cewa rashin mayar da hankali wajen kare muradun al’umma da kawo saukin rayuwa shi ne ya haifar da karancin wuta, tsadar kayayyaki, da fatara.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.