Ghana: Dangote zai Kafa Katafaren Kamfanin Sukarin da zai Samar da Ayyuka
- Attajirin Afrika, Aliko Dangote, ya kaddamar da wani katafaren kamfanin sukari a yankin Bono na kasar Ghana domin rage dogaro da kayayyakin waje
- Kamfanin zai rika sarrafa tan 12,000 na rake a kowace rana tare da samun sauran amfanin amfanin gona daga gonaki masu fili mai girman hekta 25,000
- Ana sa ran aikin ya kasance wata dama ta bunkasa masana’antu a Ghana, da samar da ayyukan yi da kuma inganta tattalin arzikin Afrika baki daya
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Ghana - Aliko Dangote da ya fi kowa kudi a nahiyar Afrika zai shiga Ghana inda zai gina wani katafaren kamfanin sukari a Kwame-Danso, cikin yankin Bono.
Ana sa ran aikin zai taimaka matuka wajen rage yawan kudin da kasar ke kashewa wajen shigo da sukari daga kasashen waje.

Asali: UGC
Rahoton Business Insider Africa ya bayyana cewa aikin zai samar da ayyukan yi da dama ga matasa.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A cewar wani jami’in kamfanin, an riga an tanadi fili don aikin, kuma ana kan kammala yarjejeniyoyi da hukumomi domin fara gini.
Bayani kan kamfanin sukarin Dangote a Ghana
Sabon kamfanin zai rika sarrafa tan 12,000 na rake a kullum, tare da samun kayan amfanin gona daga filin noma mai fadin hekta 25,000 da za a shuka rake.
Baya ga sukari, za a kuma samar da sinadarai masu daraja wanda za su samar da damammaki a fannin sarrafa amfanin gona da samar da makamashi.
Kamfanin Dangote ya bayyana muhimmancin aikin yana mai cewa wannan wani tsani ne na cin gashin kai da bunkasa tattalin arziki da samar da ayyukan yi.
Za a rage shigo da sukari a kasar Ghana
Ghana dai ta shafe shekaru tana dogaro da shigo da sukari daga waje domin biyan bukatunta na cikin gida.
Rahoton Forbes Africa ya bayyana cewa wannan aikin zai zama sabon shafi a yunkurin kasar na dogaro da kanta.
Rahotanni sun bayyana cewa shigar Dangote Ghana zai inganta ci gaban yankunan karkara, samar da ayyukan yi, da kuma kawo sababbin fasahohi a fannin sarrafa rake.

Asali: Getty Images
Yankin gabashin Bono da ke fama da karancin zuba jari zai amfana matuka da wannan aiki wanda zai janyo hankalin masu zuba jari daga cikin gida da waje.
Inganta kasuwanci a yammacin Afrika
Ana ganin gina kamfanin wani bangare ne na shirin Dangote na yaduwar aikin noma da masana’antu a duk fadin Afrika.
Kamfaninsa a Najeriya shi ne mafi girma wajen sarrafa sukari, yana da karfin sarrafa rake fiye da tan miliyan 1.5 a kowace shekara.
Matakin gina sabon kamfanin na zuwa ne a daidai lokacin da ake kara karfafa hadin gwiwar tattalin arziki tsakanin kasashen Afirka karkashin yarjejeniyar AfCFTA.
An sako matatar man Dangote a gaba
A wani rahoton, kun ji cewa Alhaji Aliko Dangote ya ce wasu mutane sun sako matatar shi da ya gina a Legas a gaba.
Alhaj Aliko Dangote ya ce duk da kalubalen da ake jefa masa na ganin matatar ba ta yi aiki yadda ya kamata ba zai yi nasara.
Dangote ya jaddada cewa ya saba da gwagwarmaya a tarihin rayuwar shi kuma hakan na ba shi karfin gwiwa cewa ba za su ga bayan shi ba.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng