Mummunan Iftila'i Ya Fada wa Amurka, Gari Guda Ya Rushe, An Rufe Sansanin Sojoji
- Wata mummunar guguwa ta afka wa birnin Enid da ke jihar Oklahoma a ranar Alhamis, inda ta ruguje gidaje, tare da raba dubban mutane muhallansu
- Hukumomin agajin gaggawa sun tabbatar da cewa babu wanda ya rasa ransa, sai dai mutane kusan 15 sun sami raunuka daban-daban
- Bala’in ya tilasta wa gwamnatin Amurka rufe sansanin sojin sama na Vance sakamakon lalacewar hanyoyin samar da ruwa da wutar lantarki a yankin
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.
Amurka – Wata gagarumar guguwa mai karfin gaske ta raunata mutane aƙalla 15 tare da ruguza gidaje da gine-ginen kasuwanci a birnin Enid na jihar Oklahoma.
Guguwar, wadda ta afka wa yankin a ranar Alhamis, 23 ga watan Afrilu, 2026, ta bar tarkacen karfe da itace a ko'ina cikin birnin.

Source: Getty Images
Mummunar guguwa ta afka wa Amurka

Kara karanta wannan
Hormuz: Matakin Amurka da Iran ya ta'azzara farashin fetur a duniya, ganga ta haura $100
Rahoton CBS News ya nuna cewa Keli Cain, daraktar hulda da jama'a ta hukumar bayar da agajin gaggawa ta jihar ce ta shaida wa manema labarai a abubuwan da suka faru a safiyar yau Juma'a.
Keli Cain ta ce duk da girman asarar dukiya, ba a samu rahoton rasa rai ba yayin da bidiyo da aka yaɗa a intanet suka nuna yadda mummunar guguwar ta karya bishiyoyi, ta raba su da jijiyoyinsu, sannan ta yi katantanwa da motoci.
Magajin garin Enid, David Mason, ya bayyana cewa wasu mazauna yankin sun maƙale a cikin gidajensu sakamakon tarkacen gine-ginen da suka danne su kafin jami'an kwana-kwana su ceto su.
Mutane sun taimaka wa 'yan uwansu
Yankin Gray Ridge da ke kudancin birnin ya fi fuskantar barna, inda gidaje da dama suka rushe gaba ɗaya.
"Goyon bayan da muka samu daga al'umma abin a yaba ne. Yan kasuwa sun kawo kayan aiki, mazauna yankin sun buɗe gidajensu ga waɗanda ba su da wurin kwana." — David Mason
Sakamakon wannan bala'i, an rufe babban titin Interstate 81 da wasu hanyoyi da dama, yayin da ofishin ƴan sanda ya sanar da cewa layukan wayarsu sun yanke sakamakon barnar da iskar ta yi.

Kara karanta wannan
Majalisa ta dauki mataki kan hare haren Boko Haram da suk kashe manyan sojojin Najeriya
Ofishin ƴan sandan na Garfield ya wallafa a shafinsa na Facebook cewa mutanen yankin za su iya kiran 911 idan har suna neman agajin gaggawa.

Source: Getty Images
Guguwa ta tilasta rufe sansanin sojin Amurka
An rufe sansanin sojojin saman Amurka na Vance, wanda ke cikin birnin, har sai yadda hali ya yi, kamar yadda sanarwar sansanin ta nuna a shafin Facebook.
Shugabannin sansanin sun bayyana cewa suna kokarin mayar da wutar lantarki da ruwan sha da suka yanke. An umarci dukkan ma'aikatan da ba sa yin ayyuka na musamman da su zauna a gida har sai an kammala tantance barnar da guguwar ta yi wa sansanin.
Cocin Oakwood Christian da ke Enid ya buɗe kofofinsa tun daren jiya domin samar da wurin kwana da abinci ga mutanen da iskar ta raba da gidajensu.
Ambaliya ta kashe mutane 120 a Amurka
A wani labari, mun ruwaito cewa, Shugaba Donald Trump ya ziyarci Texas domin duba ambaliyar da ta yi sanadin mutuwar mutane 120 tare da bacewar wasu 160.
Trump ya gana da iyalan mamata da jami’an ceto a yankin Kudancin Texas, inda kogin Guadalupe ya balle, ya haifar da barna mai yawa.
Rahoto ya nuna cewa ambaliyar ta kashe yara 36 da ke sansanin Camp Mystic, mafi munin iftila'i tun bayan da Trump ya hau mulki.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng